islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Lazimtar Sunnar Annabi s.a.w


13405
Surantawa
Haqiqa musulunci ya lazimtawa musulmi lazimtar sunnar manzon Allah saw a kowane irin yanayi, kuma wannan shi zai baiwa musulmi kusanci da ubangijinsa, da samun yardarsa a nan duniya da lahira.

Manufofin huxubar

Bayanin haqiqanin sonsa (ﷺ).

Bayanin cewa, ibada ba za ta zama karvavviya ba sai ta dace da sunnarsa.

Bayanin cewa, ma’anar shaidawa Muhammadu manzon Allah ne, shi ne tsantsanta biyayya gare shi.

Bayanin amfanin lazimtar sunnah.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta. Baya haka;

Ya ku bayin Allah! A cikin mu waye ba ya son manzon Allah (ﷺ)? Wanene a cikinmu ba ya son kasancewa tare da manzon Allah (ﷺ) a lahira?

Wanene a cikinmu ba ya qaunar ceton Almustafa (ﷺ)?

Kowanne daga cikinmu yana fafutuka don rabauta da kusanci da Manzon Allah (ﷺ) da samun cetonsa a ranar alqiyama, da kusantar Allah da sonsa. Sai dai menene tafarki zuwa a haka, menene hanya mai sadarwa zuwa cim ma waannan buri?

Hayan xaya ce babu ta biyu, ita ce, lazimtar biyayya gare shi (ﷺ). Domin son Manzon Allah (ﷺ), Allah ne wanda ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya ya wajabta shi, don haka babu imani ga wanda ba ya son sa. Kuma alama ta farko ta gaskiyar saonsa tana cikin biyayya gare shi, da bin sunnarsa. Allah Ta’ala Ya ce:

(قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ الْكَافِرِينَ32) [آل عمران: ٣٢].

(Ka ce, ku bi Allah da manzonsa, idan kuwa suka ba da baya to Allah ba ya son kafirai).

Kuma ya ce:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآَخِرِ ذَلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا59) [النساء: 59] (Ya ku waxanda suka imani, ku bi Allah ku bi Manzo, da shugabanni a cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani lamari, to ku mai da shi zuwa ga Allah da Manzonsa, in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar lahira, wannan shi ne mafi alhri kuma mafi kyawun makoma).

Kuma Allah yana cewa:

(قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُمْ مَا حُمِّلْتُمْ وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ54) [النور: 54]

٥٤].

(Ka ce ku bi Allah ku bi manzo, idan kun juya baya, to abin da aka xora masa ne ke kansa, ku kuma abin da aka xora muku ne ke kanku. Idan kuwa kuka bi shi kwa shiryu, ba komai yake a kan manzo ba face isarwa mabayyaniya).

Kuma ya ce:

(قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ31) [آل عمران: 31]

“Ka ce, in kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah zai so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku, Allah mai gafara ne mai jinqai.”

Allah Ta’ala ya ce:

(وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُبِينًا36) [الأحزاب: 36]

(Bai kasance ga wani mumini ko mumina ba idan Allah da manzonsa suka hukunta wani lamari, ya zama suna da zavi a lamarinsu ba. Duk wanda ya savi Allah da manzonsa, to haqiqa ya vata, vata mabayyani).

Allah maxaukakin sarki yana cewa:

(إِنَّمَا كَانَ قَوْلَ الْمُؤْمِنِينَ إِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ أَنْ يَقُولُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ51 وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَخْشَ اللَّهَ وَيَتَّقْهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَائِزُونَ52) [النور: ٥١ – ٥٢].

(Kaxai faxin muminai idan aka kira su zuwa ga Allah da manzonsa, domin ya yi hukunci a tsakaninsu, shi ne, su ce, mu ji kuma mun bi. Waxannan su ne masu rabauta. Wanda ya bi Allah da manzonsa kuma ya ji tsoron Allah, ya tsorace shi, to waxannan su ne masu samun rabo).

Ya ku bayin Allah, hadisai da yawa sun zo suna zaburarwa a kan wajabcin bin sunna Ma’aiki. Ga kaxan daga cikinsu:

An karvo daga Irbadh bn Sariyah (R.A), ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya yi mana wa’azi wanda zukata suka raurawa da shi, idanuwa suka zubar da hawaye. Sai muka ce, ya Ma’aikin Allah, kamar ka ce, wa’azi ne na mai ban kwana! Ka yi mana wasiyya. Ya ce, "Ina muku wasiyya da tsoron Allah, da ji da bi, koda an shugabantar muku da bawa a kanku, domin wanda zai rayu a cikinku, to zai ga savani mai yawa, don haka na hore ku da bin sunnata da sunnar halifofina shiryayyu ababan shiryarwa, ku cije ta da fiqoqinku. Kuma na hane ku da fararrun lamurra, domin kowace bidi’a vata ce”. Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Hibban, da Ibn Majah suka rawaito shi. Tirmizi ya ce; Hadisi ne kyakkyawa ingantacce.

An karvo daga Xan Abbas (R.A), cewa, Manzon Allah (ﷺ), ya yi huxuba a yayin hajjin ban kwana sai ya ce, “Haqiqa shaixan ya yanke qauna a bauta masa a qasarku, sai dai ya yarda a bi shi a komabayan haka, daga abubuwan da kuke rainawa daga ayyukanku. To ku shiga taitayinku! Haqiqa na bar muku abin da in kuka yi riqo da shi ba zaq ku vata ba, har abada, littafin Allah da sunnar Annabinsa. Har qarshen hadisin. Hakim ne ya rawaito shi kuma ya inganta shi.

Daga Abu Hurairah, Allah ya qara yarda a gare shi cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Dukkanin al’ummata za su shiga aljanna sai wanda ya qi”. Suka ce, ya manzon Allah waye zai ce, ya qi? Sai ya ce: “Wanda ya bi ni zai shiga aljanna, wanda ya sava min kuwa to ya qi”, Bukhari ne ya rawaito shi.

Daga Jabir xan Abdullahi (R.A) ya ce: “Mala’iku sun zo gurin Annabi (ﷺ) yana barci, sai sashinsu ya ce: Haqiqa barci yake. wasu kuwa suka ce; Idon yana barci, amma zuciyar a faxake take. Suka ce, lallai mutumin naku yana da misali, ku buga masa misali. Sai suka ce; Misalinsa kamar misalin mutum ne da ya gina gida, sai ya sanya kavaki a cikinsa, ya aika mai shela, to duk wanda ya amsawa mai shelar zai shiga gidan, kuma ya ci daga wannan kavakin, wanda kuwa bai amsa ba, ba zai shiga gidan ba. Kuma ba zai ci daga kavakin ba. Sai suka ce; To ku fassara wannan misalin ya fahimce shi. Sai sashinsu ya ce, Shi barci yake. Sashinsu kuma ya ce, lallai idan barci suke, amma zuciyar a faxake take. Sai suka ce, gidan dai shi ne aljanna, mai kiran kuwa shi ne Muhammadu (ﷺ). to duk wanda ya bi Muhammadu (ﷺ) to ya bi Allah, wanda ya savi Muhammadu (ﷺ) to ya savi Allah, kuma Annabi Muhammad (ﷺ) shi ne bambancin da ke tsakanin mutane”. Bukhari ne ya rawaito shi.

An karvo daga Abu Rafi’i, (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Kada in sami xayanku yana kishingixe a kan gadonsa, umarnina ya zo masa daga abin da na yi umarni da shi, ko na yi hani a kansa, sai ya ce, Ban sani ba, abin da muka samu a cikin littafin Allah za mu bi shi (in ba haka ba to a za mu bi ba). Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi da sanadi ingantacce.

Daga Ibn Mas’ud, (R.A) ya ce; “Tsaka-tsaki a sunna fi alheri sama da kazar-kazar a bidi’a”, Hakim ne ya rawaito shi, ya ce, isnadinsa ingatacce ne.

Ya ku bayin Allah! Haka nan maganganu sun zo daga sahabbai a wannan babi kuma suna da yawa. Kaxan daga cikinsu:

Mujahid yana cewa, mun kasance tare da Ibn Umar Allah ya jiqansa, a cikin wata tafiya, sai ya wuce ta wani guri, sai ya karkace masa. Sai aka tambaye shi saboda me ka aikata haka? Sai ya ce, "Na ga Manzon Allah (ﷺ) ya aikata haka, sai ni ma na aikata". Ahmad da Bazzar ne suka rawaito da Isnadi kyakkyawa.

Kuma daga Ibn Umar (R.A); cewa shi ya kasance yana zuwa gurin wata bishiya tsakanin Makka da Madina sai ya yi qailula a qarqashinta. Sai ya ba da labari cewa Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana aikata haka. Bazzar ne ya rawaito da Isnadin da babu laifi a cikinsa.

Akwai fa’idoji masu ximbin yawa da musulmi zai samu a cikin bin sunnar Annabi (ﷺ), Ga kaxan daga muhimmansu:

A cikin bin sunnar manzon Allah (ﷺ) akwai samun kariya daga faxawa cikin savani wanda marar kyau, ma nisanta bawa daga addini, wanda shi ne alamar rauni, kuma mutum ba zai kuvuta daga gare shi, ba sai da bin Allah da manzonsa. Allah ta’ata ya ce:

(وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَا تَنَازَعُوا فَتَفْشَلُوا وَتَذْهَبَ رِيحُكُمْ وَاصْبِرُوا إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ46) [الأنفال: 46]

(Kuma ku bi Allah da manzonsa, kuma kada ku yi jayayya sai ku sami karyewa, kuma qarfinku ya tafi, ku yi haquri, haqiqa Allah yana tare da masu haquri).

Hakanan a cikin hadisin Irbadh da ya gabata Annabi ya ce, «Ina muku wasiyya da tsoron Allah, da ji da biyayya, koda bawa ne Bahabashe ya zama shugabanku, domin duk wanda ya rayu daga cikinku to zai ga savani mai yawa, kuma na gargaxe ku ga barin fararrun lamura, domin su vata ne. Wanda ya riski haka daga cikinku, to na hore ku da bin sunna ta, da sunnar halifofi shiryayyu ababan shiryarwa, ku cije ta da fiqoqinku». (Ma’ana, ku riqe su gangam).

Amfani na biyu; A cikin bin sunna da lazimtar ta, akwai kuvuta daga rarrabuwar kai, wadda Allah ya yi alkawarin narko ga ahlinta.

Tirmizi ya ruwaito hadisi daga Abdullahi xan Umar. Annabi (ﷺ) ya ce; "Haqiqa abin da ya zo wa Banu Isra’ila zai zo wa al’ummata, kwabo-da-kwabo, kuma haqiqa Banu Isra’ila sun rabu qungiya saba’in da biyu. Al’umma ta kuwa za ta kasu zuwa qungiya saba’in da uku, dukkansu suna cikin wuta sai qugiya xaya". Suka ce, wacce ce ya manzon Allah? Ya ce, “Ita ce (wacce take kan) abin da nake kai, ni da sahabbaina”.

Amfani na uku; A cikin lazimtar sunna akwai samun shiriya da kuvuta daga vata. An karvo daga Abu Huraira (R.A) ya ce; Manzon Allah (ﷺ) ya ce; “Haqiqa na bar abu biyu a cikinku ba za ku tava vata bayansu ba, littafin Allah da sunnata, kuma ba za su tava rabuwa ba, har sai sun zo gare ni a wajen tafkin alkausara”. Hakim da Daruquxni da Baihaqi ne suka fitar da shi.

Kuma an rawaito daga Xan Abbas (R.A) cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya yi huxuba cikin mutane a hajjin ban ikwana sai ya ce “Ya ku mutane haqiqa ni na bar muku abin da in kun yi riqo da shi ba za ku tava vata ba, littafin Allah da sunnar Annabinsa.” Baihaqi ne ya fitar da shi.

Waxannan hadisai suna fa’idantar da cewa, a cikin bin sunnar Annabi (ﷺ), a nan kuvuta take daga vata.

Malik Allah ya jiqansa, ya ce; “Sunna, kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya noqe ya halaka.”

Wannan gaskiya ne, domin jirgin ruwan Annabi Nuhu, ba wanda ya hau shi, sai wanda ya gaskata manzanni, wanda bai hau shi ba, ya qaryata manzanni. Shi kuwa bin sunna bi ne ga manzancin da ya zo daga Allah. Don haka wanda ya bi shi, kamar wanda ya bi jirgin ruwa ne, zahiri da baxini, wanda ya qi bin manzancin, kamar wanda ya qi bin Annabi Nuhu ne da hawa jirgin ruwa tare da shi.

Amfani na huxu: A cikin sunna akwai shiga cikin tawagar Annabi (ﷺ), a cikin barin ta kuwa akwai fita daga cikin tawagarsa.

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Anas xan Malik (R.A) yana cewa; “Wasu mutane uku sun zo ga matan manzon Allah (ﷺ) suna tambaya game da bautar Annabi (ﷺ). Yayin da aka ba su labari, sai kamar sun ga qarancinta, suka ce, ina mu ina Annabi (ﷺ), alhali shi an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa da abin da ya jinkirta, xayansu ya ce, amma ni zan yi sallah tsawon dare har abada. Xayan ya ce, ni za yi azumin har abada ba za sha ba. Xayan ya ce, ni zan nisanci mata ba za yi aure ba har abada. Sai manzon Allah (ﷺ) ya zo wajen su, ya ce “Ku ne kuka ce kaza da kaza, amma wallahi ni, na fi ku tsoron Allah, sai dai ni ina azumi ina sha, ina sallah in barci, kuma ina auren mata, to duk wanda ya yi bar sunnata ba ya tare da ni.”

Barin sunnar Annabi (ﷺ) mataki biyu ne. Yana iya kasancewa a matsayin savo. Yakan kuma iya kasancewa a matsayin kafirci. Wal’iyazu billahi.

Idan ka bar sunnar don sakaci da kasala, ba don ganin cewa akwai naqasa a cikinta ba, to hukuncinka shi ne gwargwadon irin sunnar da ka bari. In ka bar wajibi ne, to kana da laifin barin wajibi. In kuma Mustahabbi ka bari to haqiqa falalar mustahabbi ya kuvuce maka.

Ku ji tsoron Allah ya bayin Allah ku yi riqo da igiya mafi aminci ta musulunci, kuma ku yi sani cewa mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinku (ﷺ), kuma mafi sharrin lamurra shi ne fararrunsu kuma dukkanin fararrun abubuwa bida’a ce, kuma dukkanin bidi’a vata ne, wal’iyazu billah.

Wannan shi ne abin da zan iya faxa, kuma ina neman gafarar Allah maxaukaki mai girma ga kaina da ku da sauran musulmi daga dukkan zunubi, ku nemi gafararsa, haqiqa shi mai gafara ne mai jinqai.

Yabo ya tabbata ga Allah, Shi ne qasaitaccen sarki. Tsira da amincin Allah, su tabbata ga bayinsa da ya zava, bayan haka, ya ku bayin Allah!

Amfani na biyar; cewa a cikin falalar sunna, da binta akwai ‘yantuwa daga hanyoyin shaixani. An karvo daga Ibn Mas’ud (R.A), ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya zana wani zane sai ya ce: “Wannan shi ne tafarkin Allah, sannan sake yin wasu ‘yan qananan zane a hagunsa da damansa. Sannan manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wannan shi ne tafarkina, waxannan kuma wasu hanyoyi ne, a kan kowace hanya akwai shaixani da yake kira zuwa gare shi". Sannan ya karanta faxar Allah:

(وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ153) [الأنعام: 153]

(Kuma cewa wannan shi ne tafarkina miqaqqe, ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi, sai su raba ku da tafarkinsa, wannan shi ne abin da ya yi muku wasiyya da shi, tsammaninku za ku ji tsoron Allah).

Duk wanda ya bi sunnar Annabi (ﷺ) ya bi tafarki maidadaici, kuma ya kuvuta daga hanyoyin shaixanu.

Ibn Taimiyya Allah ya jiqansa, ya ce: “Mafi yawancin waxannan hanyoyin vatan suna shigo wa wanda bai yi riqo da littafin Allah da sunna ba. Kamar yadda Zuhri yake cewa, “Malamanmu sun kasance suna cewa, riqo da sunna shi ne tsira.”

Amfani na shida: A cikin bin sunna akwai samar da addinin da shari’a. Wannan kuwa saboda addini ma’anarsa ka bautawa Allah, kuma kada ka bauta masa sai da abin da ya shar’anta, kuma ba mu da hanyar sanin shar’ah ba tare da Alqur’ani da sunnar Annabin (ﷺ) ba. Don haka ibadu suka kasance sai yadda shari’a ta tsara su. Babu mamaki da nana A’isha (R.A) ta ce: "Halayensa (ﷺ) suna kasance Alqur’ani". Sunnarsa (ﷺ) ta kasance ta mamaye dukkanin addini. Ita ce mai bayyana ma’anonin Alqur’ani mai girma. Allah Ta’ala ya ce:

(وَأَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ44) [النحل: 44]

(Kuma mun saukar da ambato gare ka domin ka bayyana wa mutane abin da aka saukar musu, tsammaninsu za su yi tunani).

Allah Ta’ala ya ce:

(وَمَا أَنْزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ إِلَّا لِتُبَيِّنَ لَهُمُ الَّذِي اخْتَلَفُوا فِيهِ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ64) [النحل: 64]

(Kuma ba mu saukar maka da littafi ba, sai don ka bayyana musu abin da suka yi savani a cikinsa, kuma da shiriya, da rahama ga mutane da suke masu imani).

Annabi (ﷺ) ya yi alwala sai ya ce: “Wannan ita ce alwalata, kuma alwalar annabawa gabani na, duk wanda ya qara ko ya tauye, to ya munana, ya yi zalunci.”

Kuma Annabi (ﷺ) ya yi salla, kuma ya ce, “Ku yi salla kamar yadda kuka gan ni ina sallah.”

Kuma shi ne ya ce: “Kaxai an aiko ni ne don in cika kyawawan xabi’u”. Kuma shi ne ya ce, “Ku yaxa sallama a tsakaninku, kuma ku ciyar da abinci, ku yi sallah da dare yayin da mutane suke barci, za ku shiga aljannar Ubangijinku da aminci”.

Amfani na bakwai: A cikin bin ka ga sunna akwai xage alamar qasqanci da wulaqanci daga al’umma, domin sunna ita ce addini, kuma barin addini shi ne musabbabin qasqanci da wulaqanci.

Ahmad da Abu Dawud sun ruwaito hadisi daga Ibn Umar, ya ce, Mun ji manzon Allah (ﷺ) yana cewa, “Idan kuka yi cinikin eena, kuma kuka riqi kiwo, kuma kuka raja’a kan noma, kuka bar jihadi, Allah zai xora muku qasqancin da ba zai cire muku shi ba har sai kun komo zuwa addininku”.

Cinikin eena shi ne, cinikin da mutum ya sayar wa da wani mutum kaya bashi zuwa wani lokaci, sannan ya sayi kayen daga wajesa a take, da kuxin da ba su kai abin da ya sayar masa ba.

Don haka komawa sunna, komawa ne zuwa ga addini.

Amfani na takwas: A cikinta akwai bayanin cutar da ta samu wannan al’umma ta Musulmi da kuma bayanin maganinta.

Ahmad da Abu Dawud sun ruwaito hadisi daga Sauban, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Al’ummomi sun kusa su yi ca a kanku, kamar yadda masu cin abinci suke yi daka wawa a kan akushisu". Sai wani ya ce, saboda rashin yawanmu ne a lokacin? Sai ya ce: “A’a, ku a lokacin kuna da yawa, sai dai kun zama shara, kamar sharar da ruwa yake korawa. Lallai za a cire kwarjininku daga zukatan abokan gabarku, kuma za a jefa rauni a zukatanku". Wani mai magana ya ce, ya manzon Allah mene ne rauni? Sai ya ce, “Son duniya da qin mutuwa”.

Manzon Allah (ﷺ) ya siffanta mana cutar mu da halinmu ya ce, “Lallai al’ummomi sun kusa su yi ca a kanku kamar yadda masu cin abinci suke daka wasoso a kan akushinsu”. Shin wannan bai faru ba?! Wallahi ya faru. Qasashen mulkin mallaka sun yi ca, a kan qasashen musulmai. Waxannan qasashe na musulmai, Allah Ta’ala Ya ba su alherai, ya azurta su da alheran qoramu, da noma, da fetur, da abubuwa daban daban, amma duk da haka sun riqa daka wawa a kansu kamar yadda masu cin abinci suke wawa kan akushinsu. Wannan yanayi ba zai rabu da wannan al'umma ba har sai ta koma ga addininta. Komawa ga addinin kuwa shi ne, komawa zuwa ga Alqur'ani da Sunna.

Amfani na tara: A cikin sunnarsa (ﷺ), akwai samun cikar halaye da kyawawan xabi’u na gari. Ahmad ya ruwaito hadisi daga Abu Huraira, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce,: “Kaxai an aiko ni ne don in cika kyawawan halaye".

Ibn Abdul Barr, ya ce, "Wannan hadisin Madina ne ingantacce". Kuma nagarta da dukkan alheri da addini, da falala, da kyautayi, da adalci, duk sun shiga cikin wannan ma’ana.

Amfani na goma: Cikin riqo da sunna akwai tsira daga fitina da azaba mai raxaxi.

Allah maxaukakin sarki ya ce:

(لَا تَجْعَلُوا دُعَاءَ الرَّسُولِ بَيْنَكُمْ كَدُعَاءِ بَعْضِكُمْ بَعْضًا قَدْ يَعْلَمُ اللَّهُ الَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنْكُمْ لِوَاذًا فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ63) [النور: 63]

(Kada ku riqa kiran Manzon Allah kamar yadda kuke kiran junanku. Haqiqa Allah ya san waxanda suke silalewa don fakewa daga acikinku, don haka masu savawa lamarinsa, su kiyayi kada wata fitina ta same su, ko wata azava mai raxaxi).

Duk wanda ya savawa sunnah! Lallai ya kiyayi: “Lallai waxanda suke savawa lamarinsa su kiyayi kada wata fitina ta same su ko azaba mai raxaxi”. Wata fitina ta same su, kamar kafirci ko munafunci ya shiga zuciyarsu, ko su shiga bidi’o’i, sai azaba mai raxaxi ta samu su. Saboda haka yana daga cikin falalar bin sunnar manzon Allah (ﷺ), samun tsira daga fitina.

Wani mutum ya zo wajen Imamu Malik ya ce, ya Imam ina son Umara! Sai ya ce, "Ka je ka yi mana!" Ya ce, ina so in yi mata harama daga nan Madina daga masallaci! Sai Malik ya ce, "Ya xana! Manzon Allah (ﷺ) ya yi Umara, kuma daga Zulhulaifah ya yi harama. Yin haramarka daga masallaci savanin sunna ne. Ina jiye maka tsoron fitina idan ka aikata haka. Sannan ya karanta faxar Allah:

“Lallai waxanda suke savawa lamarinsa su kiyayi kada fitina ta same su, ko azaba mai raxaxi”.

Ya xan uwa ka bi sunnar manzon Allah (ﷺ) sak. Ka tsaya kai da fata a kan sha'anin ibada, ba sassauci. Ka tabbata idan har ka ta fi a kan haka, to zuciyarka za ta gyaru. Hakanan iyalanka da duka danginka.

Gyaruwar iyali gyaruwar mahalli ne.

Gyaruwar mahalli kuwa gyaruwar gari ne duka.

Gyarywar gari kuwa gyaruwar qasa ce.

Gyaruwar qasa, gyaruwar al’umma ce.

Gyaruwar al’umma gyaruwar duniya gabaxaya, da izinin Allah.

Ka yi kwaxayi wajen fara gyara kanka, ka fara da kanka, sannan na kusa da kai, sannan na kusa. Ka san cewa, sunna ita ce tafarki, kuma bin shi zai samar maka da haka. Ina A’uzu billahi minasshaixanir-rajim:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآَخِرِ ذَلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا59) [النساء: 59]

(Ya ku waxanda suka ba da gaskiya, ku bi Allah ku bi manzo da shugabanni a cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani lamari, to ku mai da shi zuwa ga Allah da manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar lahira, wannan shi ne mafi alhri kuma mafi kyawun makoma)..