islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Rayuwar Lahira Itace Rayuwa Ta Haqiqa


11786
Surantawa
Lallai kowane mai rai ya san qarshensa mutuwa ne,don haka, xan Adam yana da gidaje biyu: Gidan duniya, wanda ba na tabbata ba ne, da gidan lahira, wanda shi ne dahir. Duniya, komai tsawon da ta yi, mai qarewa ce, ita da duk abin da yake cikinta, don haka, mai hankali shi ne wanda yake kallon duniya a matsayin tasha-tasha, da zai yi guzuri don lahira.

Manufofin huxubar

Dasa imani da ranar lahira a zukata.

Kwaxaitarwa a kan yin guzuri domin lahira.

Jan-kunne game da raja’a a kan duniya.

Bayanin banbancin tsakanin gidan duniya da na lahira.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ku mutane, wane ne daga cikimu ba ya fatan ya rayu rayuwa mai kyau a duniya da lahira? Wanene zai yarda ya raya duniya mai qariya, ya rusha lahira wacce ita ce rayuwa ta haqiqa? Ko kuma wanene bay a son ya zama xan aljannah?!

Ya ku ‘yan uwa! Lallai kowane mai rai ya san qarshensa mutuwa ne, kamar yadda Allah yake cewa,

(كُلُّ مَنْ عَلَيْهَا فَانٍ26 وَيَبْقَى وَجْهُ رَبِّكَ ذُو الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ27) [الرحمن: ٢٦ – ٢٧].

(Duk wanda yake kan doron qasa mai qarewa ne. Fuskar Ubangijinka ce za ta wanzu, Ma’abocin girma da xaukaka).

Don haka, xan Adam yana da gidaje biyu: Gidan duniya, wanda ba na tabbata ba ne, da gidan lahira, wanda shi ne dahir. Duniya, komai tsawon da ta yi, mai qarewa ce, ita da duk abin da yake cikinta, don haka, mai hankali shi ne wanda yake kallon duniya a matsayin tasha-tasha, da zai yi guzuri don lahira. Allah yana cewa,

(اعْلَمُوا أَنَّمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا لَعِبٌ وَلَهْوٌ وَزِينَةٌ وَتَفَاخُرٌ بَيْنَكُمْ وَتَكَاثُرٌ فِي الْأَمْوَالِ وَالْأَوْلَادِ كَمَثَلِ غَيْثٍ أَعْجَبَ الْكُفَّارَ نَبَاتُهُ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَاهُ مُصْفَرًّا ثُمَّ يَكُونُ حُطَامًا وَفِي الْآَخِرَةِ عَذَابٌ شَدِيدٌ وَمَغْفِرَةٌ مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانٌ وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا مَتَاعُ الْغُرُورِ20) [الحديد: 20]

(Ku sani cewa, rayuwar duniya wasa ce da wargi da qawa da alfahari a tsakanin ku, da tinqaho a cikin dukiya da ‘ya’ya, kamar misalin girgijen da tsiransa suka ba wa manoma mamaki, sannan sai ya girgiza ka gan shi yalo, sai ya zamo karmami. A lahira akwai azaba mai tsanani, da kuma gafara daga Allah, da yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce, face kayan ruxi).

Kuma Allah yana cewa,

(إِنَّمَا مَثَلُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَاءٍ أَنْزَلْنَاهُ مِنَ السَّمَاءِ فَاخْتَلَطَ بِهِ نَبَاتُ الْأَرْضِ مِمَّا يَأْكُلُ النَّاسُ وَالْأَنْعَامُ حَتَّى إِذَا أَخَذَتِ الْأَرْضُ زُخْرُفَهَا وَازَّيَّنَتْ وَظَنَّ أَهْلُهَا أَنَّهُمْ قَادِرُونَ عَلَيْهَا أَتَاهَا أَمْرُنَا لَيْلًا أَوْ نَهَارًا فَجَعَلْنَاهَا حَصِيدًا كَأَنْ لَمْ تَغْنَ بِالْأَمْسِ كَذَلِكَ نُفَصِّلُ الْآَيَاتِ لِقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ24) [يونس: 24]

(Kaxai dai, misalin rayuwar duniya, kamar ruwa ne da ya sauko daga sama, sai tsirran qasa suka cakuxe da shi cikin abin da mutane suke ci, da dabbobi, har sai qasa ta riqe adonta, ta qawatu, ma’abotanta sun yi tsammanin suna da iko a kanta, sai al’amarinmu ya zo mata da daddare, ko da rana, sai ya mayar da ita girbabbiya, kamar ba ita jiya. Kamar haka ne muke bayyana ayoyi ga mutanen da suke tunani).

Kuma Allah ya ce,

(وَمَا هَذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا لَهْوٌ وَلَعِبٌ وَإِنَّ الدَّارَ الْآَخِرَةَ لَهِيَ الْحَيَوَانُ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ64) [العنكبوت: 64]

(Rayuwar wannan duniya, ba komai ba ce, face wasa da wargi. Lallai gidan lahira shi ne rayuwa, da mutane suna da ilimi).

Aliyu bin Abi Xalib ya ce, “Duniya ta tafi, tana mai ba da baya, lahira ta taho tana mai gabatowa: Kowace xaya daga cikinsu, tana da ‘ya’ya. Ku zamo ‘ya’yan lahira, kada ku zamo ‘ya’yan duniya, domin yau aiki ne ba hisabi, gobe kuma hisabi ne ba aiki.” [Bukhari ya kawo shi]

Zaid ibn Thabit (RA) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wanda duniya ita ce damuwarsa, Allah zai xaixaita al’amarinsa, ya kuma sanya talaucinsa a gaban idanunsa, kuma ba zai sami komai ba na duniya, sai abin da aka rubuta masa. Wanda kuwa ya zamo lahira ne damuwarsa, Allah zai tattara al’amarinsa gare shi, kuma ya sanya wadatarsa a cikin zuciyarsa, kuma duniya ta zo masa tilas xinta.” [Ibni Majah ya rawaito shi]

Ya ku musulmai! Ku yi rige-rige cikin ayyukan alheri, don ku sami duniya da lahira, kada ku fifita duniya a kan lahira, sai ku yi asarar su duka biyun. Saboda ita duniya gona ce, lahira kuma can ake girbi. Duk wanda bai yi shuka a cikinta ba, babu abin da zai girba a lahira. Ibn Rajab yana cewa, lokacin da yake sharhin Abdullahi xan Umar, ka kasance kamar baqo a duniya. Wannan hadisin ginshiqe ne wajen taqaita buri a duniya, saboda mumini bai kamata ba a gare shi, ya xauki duniya a matsayin matabbaci, zuciyarsa ta nutsu da ita. Abin da ya kamata, ya xauki duniya a matsayin tasha, wadda za ta kai shi zuwa lahira.

Ya ku ‘yan uwa! Lallai rayuwar duniya lahira ita ce haqiqanin rayuwa, wanda idan mutum ya gan ta, zai riqa cewa, ina ma na yi aikin alheri a duniya, saboda rayuwa ce da babu mutuwa a cikinta, kuma duk wani abu da rai yake kwaxayi, ko idanu, akwaita a cikinta, rayuwa ce ta aminci, wadda ta kuvuta daga dukkan tawaya, ta kuvuta daga dukkan bala’i, babu cuta a cikinta, babu matsi a cikinta, babu tsufa a cikinta. Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, “Wurin sandar xayanku a lahira, ya fi duniya da abin da yake cikinta.” Kuma Allah yana faxa, yayin da yake siffanta ni’imar ‘ya’yan aljanna, ya ce, “Amma idan ya zamo cikin abubuwan kusantarwa, to qanshi da aljannar ni’ima za a ba shi.”

Kuma Allah yana cewa,

(وَجَزَاهُمْ بِمَا صَبَرُوا جَنَّةً وَحَرِيرًا12مُتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الْأَرَائِكِ لَا يَرَوْنَ فِيهَا شَمْسًا وَلَا زَمْهَرِيرًا13 وَدَانِيَةً عَلَيْهِمْ ظِلَالُهَا وَذُلِّلَتْ قُطُوفُهَا تَذْلِيلًا14وَيُطَافُ عَلَيْهِمْ بِآَنِيَةٍ مِنْ فِضَّةٍ وَأَكْوَابٍ كَانَتْ قَوَارِيرَ15قَوَارِيرَ مِنْ فِضَّةٍ قَدَّرُوهَا تَقْدِيرًا16 وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا كَانَ مِزَاجُهَا زَنْجَبِيلًا17 عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّى سَلْسَبِيلًا18 وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيْتَهُمْ حَسِبْتَهُمْ لُؤْلُؤًا مَنْثُورًا19 وَإِذَا رَأَيْتَ ثَمَّ رَأَيْتَ نَعِيمًا وَمُلْكًا كَبِيرًا20عَالِيَهُمْ ثِيَابُ سُنْدُسٍ خُضْرٌ وَإِسْتَبْرَقٌ وَحُلُّوا أَسَاوِرَ مِنْ فِضَّةٍ وَسَقَاهُمْ رَبُّهُمْ شَرَابًا طَهُورًا21) [الإنسان: ١٢ – ٢١].

(Kuma muka saka musu da aljanna, da hariri, saboda haquri da suka yi. Suna kishingixe a cikin gadaje, ba sa ganin rana a cikinta, ballantana tsananin sanyi. Inuwowinta suna kusa, kuma an kusanto da ‘ya’yan itatuwanta zuwa qasa, ana kewayawa gare su da qorai na azurfa, da kofuna, wanda aka daidaita su daidaitawa. Ana shayar da su a cikinta, giya wadda aka haxa ta da zanjabil, daga wani ido a cikinta, wanda ake ce masa salsabil. Yara madawwama suna kewaya su, idan ka gan su, ka ce lu’u-lu’u ne, saboda tsananin kyau. Idan ka ga waccan aljanna, za ka ga ni’ima da mulki mai girma, tufafin alhariri kore, ya lulluve su da istabraq, kuma an sanya musu kambu na azurfa, sannan Ubangijinsu yana shayar da su abin sha tsarkakakke).

An karvo daga Abu Huraira (RA) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Farkon zugar da za su shiga aljanna, surarsu kamar wata ranar sha huxu. Ba sa kaki a cikinta, ba sa kaki a cikinta, ba sa bayan-gida, qoransu a cikinta na zinare ne, talgeshansu kuwa na zinare da azurfa ne, kowanne daga cikinsu yana da mata biyu, ana ganin vargonsu ta bayan nama, saboda tsananin kyau, babu savani a tsakaninsu, babu qiyayya, zuciyarsu kamar zuciyar mutum xaya take, suna tsarkake Allah, safiya da maraice.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahmar, Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa da mabiya tafarkinsa har zuwa tashin qiyama.

Ya ku mutane! Tunda rayuwar lahira ita ce rayuwa ta gaskiya, don haka magabata suka mayar da duniya a matsayin gona ga lahira. Umar ibn Abdul-Aziz ya faxa a cikin huxubarsa, ya ce, “Lallai duniya ba mazaunanta ba ce. Allah ya rubuta mata qarewa, ya rubuta wa mazaunanta zakuxawa daga cikinta, don haka ku yi guzuri, mafificin guzuri, shi ne tsoron Allah.”

Yahaya xan Mu’azu kuwa, cewa ya yi, “Ita duniya, giyar Shaixan ce. Duk wanda ya bugu da ita, ba zai farka ba, sai lokacin mutuwa, alhali yana mai nadama, tare da wanda suka yi asara.”

Muhammad ibn Wasi’i, ya kasance idan zai yi barci, sai ya ce da iyalinsa, “Ina muku ban-kwana da Allah, domin ta yiyu mutuwa ta ce ta zo.”

Bakr Almuzani cewa ya yi, “Idan xayanku ya sami damar kada ya kwanta, face wasiyyarsa tana rubuce a kusa, to ya aikata haka, domin bai sani ba, a ina zai kwana, a duniya ko lahira?”

Uwaisu kuwa, ya kasance, idan aka ce, yaya yanayi? Sai ya ce, “Ni ban damu da yanayin ba!” saboda bai sani ba, idan ya wayi gari, ko zai kai yamma, idan kuma ya kai yamma, ko zai sake wayar gari.

Ya ku ‘yan uwa! Lallai wannan duniya mai qarewa, bai kamata ta ruxe mu ba. Ya kamata mu yi guzurin ayyukan qwarai, kamar sallah da azumi da sadaka da biyayya ga iyaye da ciyarwa don Allah, don rabauta a lahira. Ubangiji yana cewa,

(مَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ97) [النحل: 97]

(Wanda duk ya yi aikin qwarai, mace ko namiji, alhali yana mumini, to za mu rayar da shi rayuwa mai daxi, kuma za mu ba su ladansu, da abin da ya fi kyau daga abin da suka kasance suna aikatawa).