islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Tsoro Tare Da Kyakkyawan Fata


7223
Surantawa
Allah ya halacci wuta kuma ya tsawatarwa bayinsa game da ita domin su tsorace shi, hakanan ya halicci aljanna kuma ya kwadaitar game da ita don su yi fatanta, Shi tsoron azabar Allah abu na me tunzura zuciya zuwa kowane alheri,kuma mai katange ta daga kowane sharri, hakanan fatar rahamar Allah, abune mai jagorantar bawa zuwa ga yardar ubangiji da falalarsa, kuma mai harzuqa himmar mutum ne zuwa ga ayyuka kyawawa, kuma mai kawar dashi ne daga munanan ayyuka.

Manufofin huxubar

Bayani a kan ma’anar tsoro da kyakkyawan fata.

Fa’idarsu da muhimmancinsu a rayuwar xan adam musulmi.

Umarni da jin tsoro da yin kyakkyawan fata.

Falalar jin tsoron Allah, da kuma kykkyawan fata

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka: Ya ku bayin Allah!

Haqiqa ayyuka na zukata suna daga cikin manyan abubuwa. Kuma suna da girman lada da babbar uquba. Ayyukan gavvai suna tafiya kafaxa da kafaxa da ayyukan zukata. Zuciya ita sarauniya ce ta gangar jiki.

Abin da ake nufi da daidaiton zuciya shi ne, kaxaita Allah Ta'ala, da girmama shi, da son shi da tsoron shi, da kykkyawan fatan rahmar shi da yi masa biyayya da gujewa sava masa.

Muslim ya ruwaito daga Abu Hurairata Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Lalle Allah ba gangar jikinku yake kallo ba, ko dukiyoyinku, a'a yana kallon zukatanku ne da ayykanku).

Imam Hasanul Basri ya ce da wani mutum: “Ka magance zuciyarka, babban abin da Allah Yake so ga bayi shi ne, guruwar zukatansu".

Yana daga cikin ayyukan zukata wanda yake zaburar da gavvai a wajen yin kyawawan ayyuka, shi ne cusa mata tsoron Allah da kwaxayin rahamarsa. Domin tsoron Allah shi yake yi wa zuciya jagora a wajen aiki na qwarai, tare da kare ta daga munanan ayyuka. Kyakkyawan fata kuma yana yi wa zuciya jagor wajen neman yardar Allah sakamakonsa, tare da zaburar da ita zuwa ga ayyukan qwarai, da hana ta munanan ayyuka.

Tsoron Allah yana kare ziciya daga bin sha’awe-sha’awenta, da yi tawata mata akan bin hanyar halaka. Yana kuma tura ta zuwa ga duk wani abu da zai gyara ta ta samu rabauta. Tsoron Allah wani vangare ne na kaxaita Allah, saboda haka bai kamata wani ya ji tsoron wani ba irin tsoron da yake wa Allah. Yin hakan wani nau'i ne na shirka.

Allah ya yi umarni da aji tsoronsa, ka da a ji tsoron kowa sai shi. Allah ya cewa:

( إِنَّمَا ذَلِكُمُ الشَّيْطَانُ يُخَوِّفُ أَوْلِيَاءَهُ فَلَا تَخَافُوهُمْ وَخَافُونِ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ175) [آل عمران: 175]) (Haqiqa shexan ne yake tsoratar da masoyansa. Don haka kar ku ji tsoronsu, ni kaxai za ku ji tsorona, in dai kun kasance muminai(.

Hakanan yana cewa:

(فَلَا تَخْشَوُا النَّاسَ وَاخْشَوْنِ وَلَا تَشْتَرُوا بِآَيَاتِي ثَمَنًا قَلِيلًا44) [المائدة: ٤٤].

(Kada ku ji tsoron mutane, ni kaxai za ku ji tsoro. Kada ku saida ayoyin Allah da xan kuxi kaxan).

Ya zo a hadisin Anas Xan Malik ya ce: Manzon Allah ya yi mana huxuba ya ce: “da kun san abin da na sani da kun yi kuka diyawa, kuma kun yi dariya kaxan». Sai sahabban Manzon Allah suka rife fuskokinsu da mayafansu sun kuku. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Kalmar tsoro tana nufin zuciyar bawa ta riqa firgita tana razana da tunanin uqubar Ubangijin Allah akan aikata wani aiki na haram, ko barin wani aiki na wajibi. Ko gazawa wajen aikata aikin mustabbi. Da jin tsoron daga Allah ya qi karvar aikin mutum da ya yi na kirki. Don haka irin wannan tsoron ya gadarwa da zuciya gujewa ayyukan haramun, da gaggawa wajen aikata alheri.

Amma kalmar Khashyah, tana nufin tsoro Allah tare da ilimin saninsa da ganin girmansa. Shi ya sa Allah ya yi amfani da ita inda yake cewa:

(إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ28) [فاطر: ٢٨].

(Kaxai waxanda suke tsoron Allah su ne malamai).

Ya zo cikin Hadisin Bukhari da Muslim, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Lalle ni na fi ku tsoron Allah, na fi ku taqawa gare shi).

Ya ku Musulmi!

Allah ya yi alqawarin kyakkyawan lada ga duk wanda ya ji tsoronsa, kuma ya kame kansa ga barin bin son zuciya. Allah ya ce:

(وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى40 فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى41) [النازعات: ٤٠ – ٤١].

(Duk wanda ya ji tsoron tsayuwarsa a gaban Ubangijinsa, kuma ya hana kansa bin son zuciya, to lalle aljanna ce makomarsa).

Kuma haka yake cewa:

(وَلِمَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ جَنَّتَانِ46 فَبِأَيِّ آَلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ47 ذَوَاتَا أَفْنَانٍ48) }الرحمن: ٤٦ - ٤٨].

(Wanda duk ya ji tsoron tsayuwa gaba ga Ubangijinsa to yana da aljanna guda biyu ma’abociyar kyawawa rassa).

Imam Axa’u ya ce kowane reshe ya haxa kaloli na kayan marmari.

Allah ya sake cewa:

(وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ25 قَالُوا إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِي أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ26 فَمَنَّ اللَّهُ عَلَيْنَا وَوَقَانَا عَذَابَ السَّمُومِ إِنَّا كُنَّا مِنْ قَبْلُ نَدْعُوهُ إِنَّهُ هُوَ الْبَرُّ الرَّحِيمُ28) [الطور: ٢٥ - 28].

)Sai wani vangare daga cikin ‘yan aljanna ya fuskanci wani vangaren suna masu tambayar junansa. Suka ce, «Da mun kasance a duniya muna cikin iyalanmu, muna masu tsoro, sai Allah ya yi mana baiwa ya tserar da mu daga azaba ta guba mai quna. Da ma mun kasance muna bauta masa, haqiqa shi Ubangiji ya kasance mai karvar addu’ar bawa ne mai jinqai).

Wannan ya nuna mana cewa duk wanda ya ji tsoron Allah zai kumutar da shi daga duk wani abin qi, kuma ya yi masa baiwar kykkyawan qarshe.

Magabata sun kasance tsoron Allah yana rinjayarsu, tare da kyautata ayyuka. Kuma suna fatan samun rahamar Allah. Wannan yasa suka zama masu halin qwarai, masu kyawawan ayyuka.

Wata rana Umar xan Khaxxab Allah ya yarda da shi ya fita yana ran gadi dadaddare, sai ya jiyo wani mutum yana karanta suratux-Xur. Sai ya sauka daga kan jakinsa, ya jingina da garu. Ya yi rashin ta tsawon wata xaya mutane na zuwa dubo shi. Ba wanda ya san mai yake damunsa.

Amirul muminina Aliyu (R.A), yake cewa a wani lokaci bayan gama sallar Asuba: “Haqiqa na ga sahabban manzon Allah, ban ga wani abu da yake kama da su ba. Haqiqa sun kasance suna wayar gari idanuwansu da fuskokinsu sun yi hazo-hazo, da qura-qura. Goshinsu sun yi tabo kamar gwiwar akuya. Sun kwana suna masu tsaiwa da sujjada ga Ubangijinsu. Idan sun wayi gari suna masu ambaton Allah. Suna layi kamar bishiyar da iska take kaxawa. Idanuwansu na zubar da hawaye har rigunan jikinsu su jiqe sharkaf saboda kuka». Abu Nu’aim ne ya ruwaito shi a littafin Hilyah.

Abu Hafs yake cewa: «Tsoron Allah bulalarsa ce da yake dawo da bijarrun bayinsa da ita». Hakanan yake cewa: «Tsoro Allah fitila ce a cikin zuciya».

Abu Sulaiman yana cewa: «Duk zuciyar da ta rasa tsoro a cikinta ta lalace kuma ta ruguje».

Tsoro na qwarai shi ne wanda yake zaburar da baya a kan aiki na qwarai, kuma ya hana aiki mummuna. Haka idan tsoro ya wuce qa’ida, to sai ya haifarwa mutum xebe qauna daga rahamar Allah.

Ibn Rajab yana cewa: tsoron da ya sanya mai shi sauke nauyin abin da aka xora masa, ya nisanci zunubai, to wannan shi ne abin da ake bukata na wajibi. In ya qaru ta yadda ya zaburar da shi wajen nafilfili to wannan duk ya zama falala. Idan kuma ya qaru akan haka, har ya gadarwa da mai shi rashin lafia ko ma mutuwa, kuwa wata damuwa ta dindindin wanda za hana shi yin wani kazarkazar to wani tsoron ba ya da kyau».

Musulmi yana tsakanin tsoro biyu. Tsoron abin da ya riga ya wuce bai son mai Allah zai yi masa akansa ba. Da kuma tsoron abin da zai zo nan gaba bai son mai Allah zai hukunta masa ba.

Amma kyakkyawar fata shi ne kwaxayin rahamar Allah, tare da yin aiki na qwarai, da kame kai daga aikata haramun. Haqiqa kwaxayi da kyakkyawan fata ba ya kasancewa ga mutum, sai idan an gabatar da aiki na qwarai, an guji aikata munanan ayyuka, ko an tuba daga aikata su. Amma mutum ya ba aikin da wajaba akansa, ya riqa bin soye-soyen zuciyarsa, yana kuma fatan samun rahamar Allah, to wannan shi ne ake cewa, amince makircin Allah, Allah kuma yana cewa:

(أَفَأَمِنُوا مَكْرَ اللَّهِ فَلَا يَأْمَنُ مَكْرَ اللَّهِ إِلَّا الْقَوْمُ الْخَاسِرُونَ99) [الأعراف: 99]

(Shin sun amince wa makircin Allah ne. To babu wanda zai amincewa makircin Allah sai mutanen da suka asararru).

Allah ya yi bayanin cewa, kykkyawan fata shi ne wanda yake tare da kykkyawan ayyuka. Idan babu kyawawan ayyuka to babu shi. Allah yana cewa:

(إِنَّ الَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَنْفَقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً يَرْجُونَ تِجَارَةً لَنْ تَبُورَ29) [فاطر: 29] “Haqiqa waxanda suke karanta littafin Allah suka tsaida sallah, kuma suka ciyar daga abin da muka azurta su a voye da sarari, suna kwaxayin kasuwanci wanda babu asara a cikinsa).

Hakanan yana cewa:

(إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا وَالَّذِينَ هَاجَرُوا وَجَاهَدُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ أُولَئِكَ يَرْجُونَ رَحْمَةَ اللَّهِ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ218) [البقرة: 218]

(Haqiqa waxanda suka yi imani, kuma suka yi hijira, suka yi jihadi don xaukaka kalmar Allah, to waxannan su ne masu kwaxayin rahamar Allah. Kuma Allah mai yawan gafara ne mai yawan jin qai).

Duk wanda ya xora kwaxayinsa ga wanin Allah to haqiqa ya yi shirka.

Allah yana cewa:

فَمَنْ كَانَ يَرْجُوا لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا [الكهف: 110]

(To duk wanda ya kasance yana fatan kyakkyawar haxuwa da Ubangijinsa, sai ya yi aiki na qwarai, kuma kada ya haxa wani da bautar Ubangijinsa).

Haqiqa kwaxayi wata hanya ce zuwa ga Ubangiji. Ya zo a hadisi Manzon Allah ya ce, «Allah Ta’ala Ya ce: «Ni ina nan inda bawana yake zatona. Kuma ina tare da shi idan ya ambace ni». Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Yaku musulmi! Ku sani cewa, Duk wani da ba ya aika aikin kwarai amma ya ce yana fatan samun rahamar Ubangijinsa to yana yaudarar kansa ne. Allah kuma ya hana hakan. Allah yana cewa:

(Ya ku mutane, lalle alkawarin Allah gaskiya ne. To don haka kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma ka da mai ruxi ya ruxe ku).

Bayin Allah! Wannan shi ne abin da ya sauwaqa za ku ji shi daga gareni ina neman gafarar Allah gare ni da ku bakixaya. Ku nemi gafararsa, lalle shi mai yawan gafara ne mai karvar tuba.

Godiya ta tabbata ga Allah bisa kyautayinsa, da gamon katar xinsa baiwarsa. Tsarki ya tabbata gare shi. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta Annabinmu Muhammad wanda yake kira zuwa ga yardar Allah. Tsira da aminci su tabbata gare shi shi da sahabbansa da alayensa da mu tare su har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:

Yaku Musulmi! Ku sani cewa:

Babban abin da ake buqata ga bawa shi ne ya haxa tsoro da kwaxayi. Wannan shi ne halin annabawa da dukkanin bayi salihai.

Allah yana cewa:

(إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ90) [الأنبياء: 90]Ma’ana: (Lelle su sun kasance suna gaggawa wajen aikata alheri, kuma suna bauta mana tare da kwaxayi da tsoro. Kuma sun kasance masu qasqantar da kai ne gare mu).

Hakan Yana cewa:

(تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنْفِقُونَ16) [السجدة: 16]

(Jikkunansu suna nesa daga shimfuxunsu. Suna bauta Ubangijinsu, suna masu tsoro masu kwaxayi. Kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su).

Idan bawa ya san faxin rahamar Allah da faxin jinqansa, da kuma yadda yake ya fe manya-manyan zunubai, to sai ya sa kwaxayi a wajen neman rahamar Allah. Idan kuma ya san azabarsa da tsananin kamunsa, da hisabinsa, da abubuwan tsoro na ranar qiyama, da irin dangogin azaba na wutar jahannama, to sai ya firgita ya tsorata ya guji sava masa. Saboda haka ya zo cikin hadisin Abu Huraira, Manzon Allah ya ce: “Da bawa mumini ya san abin da ke wajen Allah na uquba, da ba wanda zai sa ran samun rahamarsa ba. Da a ce kafiri ya sa abin da ke wajen Allah na jinqai, da babu mai xebe qauna daga aljannarsa. Muslim ne ya rawaito shi.

A ayoyi dadama Ubangiji ya haxa maganar gafara da azaba a guri xaya. Kamar inda yake cewa:

(وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغْفِرَةٍ لِلنَّاسِ عَلَى ظُلْمِهِمْ وَإِنَّ رَبَّكَ لَشَدِيدُ الْعِقَابِ6) [الرعد: 6]

(Haqiqa Ubangijinka mai gafara ne ga mutane a bisa zalincinsu. Kuma mai matsanancin uquba ne).

Imamul Gazali ya hakaito daga Makahul al-Dimashqi ya ce, «Duk wanda ya bautawa Allah da tsoro kaxai ya zama kawariji. Wanda ya bauta masa da kwaxayi shi kaxai to ya zama Murji’i. Wanda kuwa ya bauta masa da soyayya kaxai to ya zama zindiqi. Wanda ya bauta masa da tsoro da kwaxayi da soyayya, wannan shi ne mai kaxaita Allah kuma bin tafarkin sunna». [Ihya’u Ulumud-Din].

Ibnul Qayyim ya ce, zuciya kamar tsuntsu ce, soyayya shi ne kan. Tsoro da kwaxayi su ne fukafukan, duk lokacin da kai da fukafukai suka yi lafiya, to sai tashin tsuntsun ya yi kyau. Idan aka yanke kan to tsuntsu ya tashi daga aiki. Idan kuma ya rasa fukafukansa biyu, to duk wani abin farauta za zo ya cimma masa. Sai dai magabata suna son qarfafa fiffiken tsoro sama da fiffiken kwaxayi yayin da suke cikin qoshin lafiyarsu. Lokacin mutuwarsu kuma sai sukan qarfafi fiffiken fata sama da fiffiken tsoro. Soyayyar Allah ita ce abin hawan, shi kuma fata shi ne gaba yana kira, shi tsoro yana korawa, Allah kuma shi zai kai bawansa gida lafiya da baiwarsa da karamcinsa».

Ya ku musulmi! ku ji tsoron Allah, ku yi fatan samun rahamarsa da tsoron azabarsa. Ku saurari faxin Allah da yake cewa:

(اعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ وَأَنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ98) [المائدة: 98]

(Ku sani lalle Allah mai tsananin uquba ne. Kuma lalle Allah mai yawan gafara ne kuma mai jin qai).

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga An-Nu’uman Ibn Bashir Allah ya yarda da su, ya ce, Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: "Wanda ya fi 'yan wuta samun sauqin azaba, wani mutum ne da za a sa masa garwashin wuta a qarqashin tafin qafarsa, qwaqwalwarsa tana tafarfasa saboda su. Ba a ya zaton akwai wanda ya fi shi xanxanar azaba, alhalin shi ne ya fi kowa samun sauqin azaba".

Muslim ya ruwaito daga Mugirah bn Shu'ubah Allah ya yarda da shi, shi kuma daga Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Annabi Musa ya tambayi Ubangijinsa ya ce: "Ya Ubangiji wane xan aljanna ne ya fi qaqantar matsayi? Sai ya ce, wani mutum ne da zai zo bayan 'yan aljanna sun shiga aljanna, sai a ce masa: Shiga aljanna. Sai ya ce, Ta yaya duk kowa ya shige gidansa. Kowa ya karvi rabonsa. Sai a ce, "Ka gamsu a ba ka kwatankwacin mulkin wani sarki mai mulki na duniya?". Sai ya ce, "Allah na yarda a ba ni". Sai Allah ya ce, "An ba ka kamar wannan, da kwatankwacinsa, da kwatankwacinsa, da kwatankwacinsa, da kwatankwacinsa'. Sai a ta biyar ya ce, "Ya Ubangiji na fa gamsu". Sai Ubangiji ya ce, "Kana da kwatankwacin haka har sau goma. Kuma am ba ka duk abin da ranka ke sha'awa, idanka ke gani ya ji daxi". Sai ya ce, "Ya Ubangiji na gamsu".

To a zamani irin wannan da zukata suka qeqashe, san duniya ya cika su. Mutane suka daina jin tsoron savawa da aukawa zunubi, to ya kamata a rinjayar da fiffiken tsoro, domin zukata su daidaita. Idan kuma bawa ya zo mutuwa to sai ya rinjayar da janibin fata da kwaxayin samun rahama, kamar yadda Manzon tsira yake cewa: "Kada xayanku ya mutu face yana kyautata zatonsa ga Ubangijinsa".

Don haka – Ya ku bayin Allah - tsoron Allah yana buqatar tsayawa a zo da haqqin Allah ta'ala. Mutum ya guji sakaci akansu, kuma bawa ya nisanci zaluntar bayin Allah, ya ba su duk wani haqqi na su, kada ya yi musu wasa ko ya tozarta haqqin wani. Kuma tsoron Allah yana hana bawa sakin jiki wajen bin sha'awar ransa, ko aikata haramun. Kuma ya zama yana taka-tsantsan game da duniya da fitintinunta, kuma yana begen lahira da ni'imarta.