islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Ranar Juma’a


18589
Surantawa
Ranar jumaa itace mafi alherin dukkan wata rana da rana ta fito a cikinta. cikinta Allah ya halicci Adam, cikinta ne qiyama zata tsayu, kuma ita ranar idi ice ga musulmai.Don haka nema aka sharanta wasu abubuwa acikinta, daga ciki akwai: hudubar jumaa, wanka, fesa tirare, fita cikinta da mafi kyawun kaya da yanayi me kyau, yin kabarbari lokacin fita sallar, kusantar liman, da kuma tara tunani gaba daya domin sauraren wa'azi da ambato (wato huduba).

Manufofin huxubar

Bayanin kan fifita ranar juma’a da shiryar da wannan alu’mma ta Annabi Muhammadu (ﷺ) zuwa gare ta.

Bayanin hukuncin sallar juma’a da wasu daga ladubbanta.

Laifin wanda ya qi zuwa sallar juma’a.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ya ku mutane ku ji tsoron Allah, kuma ku sani cewa, Allah yana halittar abin da ya so kuma ya zava, kamar yadda ya ce,

(وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ وَيَخْتَارُ مَا كَانَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ سُبْحَانَ اللَّهِ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ68) [القصص: 68]

(Kuma Ubangijinka yana halittar abin da ya so kuma ya zava. Su ba su kasance suna da zavi ba).

Kuma ku sani cewa, Allah Ta’ala yana da hikima isasshiya cikin abin da yake zava, domin Allah yana zavar manzanni daga cikin mala’iku, da kuma mutane: Allah yana cewa,

(اللَّهُ يَصْطَفِي مِنَ الْمَلَائِكَةِ رُسُلًا وَمِنَ النَّاسِ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ75) [الحج: 75]

(Allah yana zavar manzanni daga mala’iku da kuma mutane).

Kuma Allah Ta’ala ya zavi Makka a bisa ragowar gurare, sannan bayanta ya zavi Madina gidan hijirar cikamakin Annabawa. Sannan bayansu ya zavi Baitul –Maqdisi mazaunar mafiya yawa daga Annabawan da Allah ya ba mu labaransu.

Allah Ta’ala Ya fifita wasu watanni da darare a bisa wasu, domin adadin watanni a wajan Allah watanni goma sha biyu ne a ranar da Allah ya halicci sammai da qasa, daga cikinsu akwai guda huxu waxanda suke masu alfarma ne; su ne Zul-Qi’ida da Zul-Hijjah da Muharram da Rajab.

Kuma mafificin yini da rana ta fito a cikinsa shi ne, yinin ranar Juma’a don haka ku girmama abin da Allah ya girmama. Allah ya yi muku rahama.

An karvo daga Aus ibn Aus (R.A.) Annabi (ﷺ) ya ce, "Wanda ya yi wanki, ya yi wanka, ya matsa kusa, ya yi sammako, ya kusanto (liman) ya saurari (huxuba), zai sami ladan tsayuwar shekara xaya da azuminta da dukkan tako da ya yi)). Tirmizi da Nasa'i da suka rawaito shi .

Kuma an karvo daga Anas ya ce, "An bijiro da sallar Juma'a ga Manzon Allah (ﷺ). Mala'ika Jibrilu ne ya zo masa da ita a tafinsa kamar farin amdubi, a tsakiyarsa akwai wani baqin xigo, sai ya ce: "Menene wannan ya jibrilu?" Ya ce masa, "Wannan ita ce Juma'a Ubangijinka yake bijiro da ita a gare ka; domin ta kasance idi a gareka da alummarka a bayanka, kuma ku kuna da alheri a cikinta, wanda kai ne za ka zama na farkon samunsa, kuma yahuduwa da nasara su zama a bayanka. Kuma a cikinta akwai wata sa'a babu wani bawa da zai yi addu'a a cikinta ta alheri da yake rabonsa ne, face an ba shi, ko ya nemi tsari daga sharri face an ije masa mafi girma daga abin da ya nema, kuma mu a sama muna ambatonsa ranar qari...". Xabarani ne ya rawaito shi a cikin Al-Ausat da isnadi mai kyau .

Kuma an rawaito daga Abu Hurairata (R.A) ya ce: "Manzon Allah (ﷺ) ya ce: (Mafificin yinin da da rana ta fito a cikinsa shi ne yinin ranar Juma'a; a cikinsa aka halicci Annabi Adam, kuma a cikinsa a ka shigar da shi aljanna, kuma a cikinsa aka fitar da shi daga cikinta). Muslim da Abu Dawud da Nasa'i suka rawaito shi.

An karvo daga Huzaifa Allah ya yarda da shi ya ce, Manzan Allah (ﷺ) ya ce: (Allah tabaraka wa Ta'ala Ya vatar da waxanda suke gabanin mu ga barin Juma'a, sai Yahudawa suka sami Asabar, Nasara kuma suka sami Lahadi, don haka su bayan mu suke bi, har ya zuwa ranar sakamako. Mu ne na qarshe daga ahalin duniya, mu ne na farko a ranar Alqiyama, waxanda za a yi wa hukunci gabanin al'ummai), Muslim ne ya rawaito shi .

Yana daga mafi girman abubuwan da Juma'a ta kevanta da su cewa, tana daga mafi girman salloli a matsayi, mafi qarfin farilla, mafi yawan lada. Haqiqa musulunci ya ba ta qarin kulawa, da isashiyar lura; don haka ya zaburar a kan yin wanka dominta, da tsabta da da yanke duk wani sansane mara daxi, da fita zuwa gareta cikin mafi kyawun tufafi da mafi cikar kama, da sammako wajan fita zuwa gareta, da kusantowa zuwa ga liman, da tattaro zuciya, waje daya domin sauraren wa'azi da ambaton Allah, a cikin hadisin da Bukhari da Muslim suka rawaito shi daga Abu Hurairata Allah ya qara yarda a gare shi cewa, Manzan Allah ya ce: (Duk wanda ya yi wanka ranar Juma'a irin wankan janaba, sannan ya tafi a sa'a ta farko to kamar ya gabatar da rakuma ne (sadaka) har qarshan hadisin.

Kuma Hakim ya rawaito kuma ya inganta shi, daga Samrah xan Jundubi (R.A.) cewa, Annabin Allah ya ce: "Ku halarto sallar Juma'a, kuma matso kusa da liman, domin mutum ba zai gushe ba yana nesa, har sai Allah ya jinkirta shi a cikin aljanna ko da ya shige ta".

Idan ya halarta ya shagala da ibada da bin ubangiji na daga sallah da zikiri da karatun Alqur'ani, har lima ya fito.

Yayin da liman ya fito sai ya kasa kunne ya saurari huxuba, sannan ya yi sallar da tsoron Allah da nutsuwa, da tuntuntuni a kan abin da ake karantawa a cikinta na zancan Allah mai buwaya da xaukaka, yayin da ya idar da sallahr farillar sai ya shagla da zikiran da aka shar'anta bayan sallah.

Kuma an sunnanta nafila mai raka'a huxu a cikin masallaci, ko kuma mai raka'o'i biyu a gidan sa, amma jinkirtata zuwa gida shi ya fi falala domin haka Annabi (ﷺ) ya yi. kamar yadda ya tabbata a cikin Bukhari da Muslimu.

Duk wanda ya kwaxaita bisa aikata haka kuma ya aiwatar da shi da ikhlasi, to ya cancanci ya sami falalar wannan rana mai albarka, kuma ya sami ladansa mai girma daga mai ni'ima mai karamci, domin haqiqa Annabi (ﷺ) ya ce: “Wanda ya yi alwala kuma ya kyautata alwalar, sannan ya zo sallar Juma'a, sannan ya ji kuma ya saurara, za a gafarta masa abin da ke tsakaninsa, da wata Juma'ar (mai zuwa) har da qarin kwana uku.” Muslim ne ya rawaito shi a cikin Sahihinsa .

Ya ku bayin Allah! Haqiqa shari'a ta yi hani bisa wasu al'amura da suke hana ladan Juma'a, ko tawayar ladanta, kamar jinkiri wajan tafiya zuwa gareta, har sai liman ya fito, da shagaltar da masu sallah ta hanyar tsatsallaka su, domin Annabi (ﷺ) ya ga wani mutum – lokacin da yake huxuba- yana tsattsallaka mutane sai ya ce masa yana masa inkari, "Ka zauna haqiqa ka cutar kuma ka wahalar". Kuma haqiqa ana jiye wa wanda ke aikata haka tsoron kada ya shiga dungumin fadin Allah, mabuwayi da xaukaka:

(وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُبِينًا58) [الأحزاب: 58]

(Kuma waxannan da suke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da wani abu da (su muminan) suka aikata ba, to haqiqa sun xauki nauyin qire da laifi mai girma).

Daga ciki: akwai uzurrawa bayin Allah ta hanyar xaga murya da zikiri ko karatun Alqur’ani, haqiqa Manzon Allah (ﷺ) ya hana hakan, da faxinsa ga sahabbai yayin da suka xaga muryarsu da qira'a: "Kada sashinku ya baiyana karatun Alqur'ani a bisa sashi" .

Mafi muni daga haka, idan wannan uzurrawar ta zamo da zance ne a kan lamarin duniya kurum, musamman ma ana cikin huxuba, domin yana daga cikin hanawa mutum (dacewa), da qarancin basira mutum ya shagala ga barin huxuba da zance, ko wasa, ko waninsa, har ladan Juma'a da falalarta su kuvuce masa. Haqiqa Annabi (ﷺ) ya faxa wajan yin gargaxi a kan haka: “Duk wanda ya shafi qasa a yayin huxuba to ya yi wasa”. Muslim ne ya rawaito shi.

Kuma na rawaito daga Abu Hurairata (R.A.) cewa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ka ce da sahibinka: yi shiru, ranar Juma'a alhali liman yana huxuba to ka yi yasasshiyar magagana”.

Kuma Imam Ahmad ya rawaito daga Ali ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Duk wanda ya ce ga sahibinsa yayin da liman yake huxuba: yi shiru to haqiqa ya yi yasasshiyar magna. Duk kuwa wanda ya yi yasasshiyar magana, to ba shi da ladan Juma'a" .

Ya ku bayin Allah! Haqiqa Manzon Allah ya tsananta wajan gargaxi game da qin halartar sallar Juma'a ba tare da wani uzuri na shari'a ba, yana mai bayyana cewa, wanda ya aikata haka haqiqa ya bijirar da kansa ga kamuwa da cutar gafala ta barin Allah, da yin rufi a kan zuciyar sa, duk kuwa wand Allah ya yi rufi a kan zuciyarsa to basirarsa za ta makance, kuma makomarsa ta munana, Muslim ya rawaito cewa, Manzon Allah ya ce:

“Lallai mutane su dai qin halartar sallar Juma'a, ko kuwa lalle Ubangiji zai rufe zukatansu, sannan su kasance daga gafalallu”.

Kuma imam Ahmad ya rawaito da Isnadi kyakkyawa, da kuma Hakim, a cikin Sahihinsa daga Abi Qatadata (R.A) cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya bar Juma’a sau uku ba tare da wata lalura ba, Allah zai yi xab'i a kan zuciyarsa”.

To ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah, kuma ku san irin falala da rahamar da Allah ya yi a kanku, ku tsaya a kan umarninsa ku bar abubuwan da ya hana, ko kwa rabauta da aljannatansa, a ranar gamuwa da shi.

Ina faxar abin da kuka ji, kuma ina neman gafarar Allah Mai Girma da xaukaka, ga kaina da dukkan musulmi, daga kowane irin zunubi. Ku nemi gafararsa, lallai shi mai yawan gafara ne, mai yawan jinqai.

Godiya ta tabbata ga Allah, ya umarce mu da lazimtar jam’i da juma’a, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gasikiya sai Allah shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne, kuma manzonsa ne, Allah ya yi tsira da aminci a gare shi mai tarin yawa. Bayan haka:

Haqiqa abin da muka yi cikin lokacin nan da ya shuxe na daga ladubba da falaloli da abubuwan da juma’a ta kevanta da su, kamar gulbi ne in an kwatantashi da kogi, kuma kaxanne daga cikin abu mai yawa.

Yaku bayin Allah! Haqiqa Ma’aikin Allah (ﷺ) ya kasance yana cin moriyar ranar Juma’a ta hanyar aikata ayyuka na qwarai, ya kasance daga aikina shiriyarsa (ﷺ), girmama wannan rana da darajta ta, da kevantarta da wasu abubuwa na musamman, kamar karanta Surar (Alif lam mim Assajdat) da (Hal ata alal insani) a sallar Alfijir xinsa, saboda sun qunshi abin da ya kasance da abin da zai kasance a yininta.

Kuma yan daga cikin abubuwan da ta kevanta da su: an so yawaita salati ga Annabi (ﷺ) a daranta.

Imam Ibn Alqaiyim Allah ya jiqansa yana cewa: "Manzo Allah shi ne shugaban halitta, kuma yinin Juma’a shi ne shugaban ranaku, don haka yin salati a gare shi a wannan rana yana da falala wadda babu irinta. Tare da wata hikimar wadda ita ce: Kasancewar duk wani alheri da al’ummarsa ta samu a duniya da lahira ta same shi ne ta hannunsa. Sai Allah ya tarawa al’ummarsa tsakanin alherin duniya da lahira, don haka mafi girman girmamawa za su samu za su same ta ne ranar Juma’a. Domin a ran nan ne za a tashe su zuwa gidaddajinsu da fadojinsu a cikin Aljanna. Kuma ranar Idi ce a gare su a duniya. Yinin da a cikinsa Allah Ta’ala yake taimakonsu da amsa addu’o’insu da buqatunsu. Kuma ba ya mai da hannun mai roqo fayau a cikinsu . Duk wannan kuwa sun san shi ne, kuma ya same su ne saboda shi, kuma ta hanyarsa. Don haka yana daga cikin biyan kaxan daga cikin haqqinsa, mu yawaita salati a gare shi a wannan yini da darensa”. Kuma ga shi Allah Ta’ala ya ce,

(إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا56) [الأحزاب: 56]

“Haqiqa Allah da mala’ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati da sallama mai yawa a gare shi.”

Daga cikin akwai karanta sororin (juma’a) da (almunafiqun) ko (Sabbih) da (Algashiyah) daga ciki; akwai cewa mai tafiya zuwa gareta yana da ladan aiki na shekara, duk taku xaya da yayi, duka da a zminta, da tsayuwara daranta.

Daga ciki akwai cewa yana kankare zunubai.

Ya ku bayin Allah! Haqiqa yana daga ababuwan da shari’a ta kevanci wannan yini dashi cewa, a cikinta akwai wata sa’a da babu wani bawa musulmi da zai yi dace da ita, yana roqon Allah daga alherin duniya da lahira, face Allah ya amsa masa addu’arsa.

Domin an ruwaito daga Abu Huraira (R.A) ya ce: Manzo Allah ya ce “Haqiqa a cikin Juma’a akwai wata sa’a babu wani musulmi da zai yi dace da ita yana tsaye yana yin sallah, yana roqon Allah wani alheri, face sai ya ba shi”. Ya yi haka da hannunsa yana alamta qarancinta (ma’ana ita sa’ar). Muslim ne ya rawaito shi.

Lallai wannan ta isa kyauta mai girma, kuma dama babba, baiwa gwaggwava, wadda Allah yake buxa qofofinsa ga bayinsa, don su roqe shi da ita. Hasararre shi ne wanda aka hana shi fallalr wannan yini da albarkar wannan sa’ar mai xinbin albarka, wadda take maimaituwa a gare mu a kowane sati. Kuma mafi rinjayen maganganu wajen tantance lokacinta shi ne, daga tsakanin La’asar zuwa faxuwar rana. Domin an karvo daga Jabir (R.A) ya ce, Manzon Allah ya ce: “Ranar juma’a sha biyu ce”: yana nufin sa’o’i, babu wani musulmi da za a samu yana roqon Allah mai girma da xaukaka wani abu face Allah ya ba shi, don haka ku neme ta a qarshen lokaci bayan La’asar”.

Ya ku musulmi! Ku yi gasa a kan wannan alheri mai girma, wanda Allah ya sanya shi cikin ranar Juma’a ga wanda ya sunnanta da sunnan Annabi a cikin wannan, ku tsaftacce jukkunanku, ku sanya mafi kyawun tufafin ku, ku yi asuwaki, ku sanya turare, ku yi sammako don ku tafi sallar Juma’a, ku lazimci ladubban Annabi (ﷺ), da tsari na Muhammadiyya. Ku kasance daga masu rigaye zuwa alherai, masu rabauta da mafiya xaukakar darajoji, (Wannan falala ce ta Allah da yake ba da ita ga wanda yaso, kuma Allah shi ne ma’abocin falala mai girma). Na ja kunnenku a kan qin halartar wannan alheri, da sakaci da waxannana sunnoni, domin ya zo a cikin sahihin hadisi: "Wasu mutane ba su gushe ba suna jinkirta ta har sai Allah Ya jinkirta su”.

Ina neman tsari da Allah daga shaxani abin la'annane.