Manufofin huxubar
Bayani a kan abin da ya wajaba musulmi ya aikata bayan qarewar Ramadan.
Bayanin tallafar juna da ke cikin musulunci.
Bayanin hukunce-hukucen sallar idi da abin da ke cikinta na hikimomi.
Huxuba Ta Farko
Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.
Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Ubanjiginku, ku yi wa kanku hisabi, me kuke aiwatarwa a cikin watanku mai girma, domin shi baqo ne mai gaggawar tafiya, ya kusa ya tafi ya bar ku, kuma zai zamo mai shaida a gare ku, ko a kanku, da abin da kuka voye a cikinsa na ayyuka, to ku yi gaggawa – Allah ya jikan ku – ku ribaci abin da ya rage da cikinsa da tuba da neman gafara, da yawaita kyawawan maganganu, da ayyuka, da aiki zuwa ga ma’abocin girman da buwaya, da fatan wannan zai tohe muku givin da ya faru daga gareku.
Ya ku bayin Allah! Haqiqa Ubangijinku Mai girma ya shar’anta muku ibada masu girma a qarshen wannan wata, wanxanda za su qara muku imani da cikar ibada da ni'imar Allah gare ku..
Zakkar Fid-da-kai; wata sadaka ce da take wajaba yayin gama azumin watan Ramadan. An san zakkar Fid-da-kai da suna na sadaka wajiba, saboda sauke azumin watan Ramadan. Domin sadaka wajiba daidai take da ma’anar zakka, don haka ake kiranta zakkar fidda kai.
Ya ku bayina Allah! Malaman fiqihu sun haxu a kan cewa zakkar fid da kai wajibi ce a kan kowane Musulmi mai iko. Hadisin da aka rawaito daga Ibn Umar (R.A) yana nuna shar’anta ta, ya ce, “Manzon Allah (ﷺ) ya wajabta zakkar fid da kai a watan Ramadan a bisa mutane, sa'i guda na dabino, ko sa’i na sha’ir, a kan kowane xa, ko bawa, namiji ko mace, daga cikin musulmai” Bukhari ne ya rawaito. Umarni a nan yana nuna wajabci.
Musulunci ya shar’anta zakkar fid da kai saboda hikimomi guda biyu. Su ne;
Hikima ta farko: Tsarkake azumin mai azumi. An shar’anta zakkar fid da kai don toshe givin da yakan faru a cikin azumin mai azumi, saboda ba makawa a tsarkake shi daga ya sasshiyar magana, da batsa, da manyan lamura, da qananansu. Haqiqa Annabi (ﷺ) ya yi nuni zuwa haka a cikin hadisi inda Ibn Abbas ya ce, “Manzon Allah (ﷺ) ya farlanta zakkar fid da kai, don ta zam tsarki ga mai azumi, daga yasasshiyar magana, da sakin baki, don kuma ciyarwa ga musulmai” Ahmed ne ya rawaito shi.
Hikima ta biyu: Tallafwa faqirai da miskinai. An shar’anta zakkar fid da kai don tausasawa miskinai da wadatar da su ga barin roqo a ranar Idi, da shigar da farin ciki a zukatansu a ranar da mutane suke farin ciki, da annushuwa, domin ta hanyar ba su zakka ne za a sauqaqa musu damuwa da raxaxin talauci da wahala.
Ya ku bayin Allah! Akwai sharaxai da suke wajabta zakkar Fid-da-kai sun:
Musulunci: Don haka bata wajaba a kan kafiri ba, koda yana da makusanta musulmai waxanda ciyar da su ya wajaba akansa, domin zakka idaba ce ta Musulunci, ba ta wajaba a kan wanda ba Musulmi ba.
'Yanci: Ba ta wajaba a kan bawa a asali, domin ba ya mallakar dukiya, amma idan bawan ya zama mabiyi ne ga shugabansa, to a nan zakka ta wajaba a kan Ubangidansa, saboda wajabcin ciyarwarsa a kansa take, faxin Annabi (ﷺ) “Ku ba da (zakkar Fid-da-kai) a madadin duk wani xa, ko bawa da kuke ciyar da shi”.
Iko na dukiya: Akan fitar da ita, wannan iko kuwa yana tabbata ne, da mallakar dukiyar da ta qaru a kan buqatarsa a daren idi da yininsa, don haka zakkar tana wajaba idan mutum ya mallaki wannan gwargwado na dukiya, ko da ya cancanci a ba shi zakka.
Shigar lokaci: Zakkar Fid-da-kai tana wajaba bayan gama azumin watan Ramadana, wannan kuwa na kasancewa ne da faxuwar ranar yinin qarshe na azumi, domin babu azumi a bayansa. Kuma lokacinta yana qarewa ne dazarar a gama sallar idi. Kuma ba ya halatta a jinkirta ta, daga ranar idi. Idan ba a fitar da ita a ranar Idi ba, ya fitar daga baya to ta zama sadaka ba zakka ba.
Idan mutum ya zama mai gida, zai fitar da ita ga kansa, da wanda yake ciyar da su, kamar mata da xa, ko da qarami ne, da uwa da bawa da mai hidima. Hadisin “Ka fara da wanda kake xaukar nauyinsa”. Yana qarfafa haka. Kuma Annabi (ﷺ) ya ce, “Ku ba da (zakkar fid da kai) a madadin kowane xa da bawa, daga waxanda kuke ciyarwa”.
Shi kuwa jinjirin da ba a haifa ba kafin Idin zakkar Fid-da-kai, a madadinsa ba ta wajaba a kan mahaifinsa ba, amma babu laifi idan ya fitar da ita, kuma zai sami ladan nafila.
Amma gwargwadon abin da za a fitar sa’i ne na alkama, ko sha’ir ko zabibi, ko wanin haka daga mafi rinjayen abincin mutanen garin. Sa’i kuwa a ma’aunanmu na zamani yana daidai da kilogram (2.176). An rawaito daga Ibn Umar cewa, Annabi (ﷺ) ya wajabta sadaqar Fid-da-kai a sa’in na alkama.
Haqiqa malaman fiqihu na Hanafiyya sun halarta fitar da qimarta daga kuxi, ko kadarori, domin manufa dai ita ce, toshe buqatar mabuqata a ranar Idi, wannan kuwa yakan samu ta hanyar ba da kuxi, kamar yadda yakan samu da ragowar jinsunan da suka zo a cikin hadisin. Sai dai jamhurun malaman fikihu sun tafi a kana rashin halarcin fitar da qima a cikin zakkar fid da kai, domin hadisai sun bayyana wasu jinsin na musamman daga alkama da sha’ir da zabibib.
Ibnu Taimiyya ya ce, “Amma fitar da kuxi domin buqata da maslaha da aadalci, babu laifi a yin hakan”.
Ana rabata ga talakawa da misikinai a ranar Idi, domin shigar da farin ciki a garesu da samar musu da abin da suke buqata.
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah, kuma kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah. Kuma babu sakamakon ta’addanci sai a kan bisa azzalumai. Allah ya yi tsira a bisa mafi darajar manzanni, Annabinmu Muhamamdu da alayensa da sahabbansa ya yi tsira.
Bayah haka: Ya ku bayin Allah! Haqiqa Allah ya shar’antawa musulmi idi guda biyu masu albarka, kowane daga cikinsu yana zuwa ne bayan wata idaba mai girma, kuma bayan aiwatar da wani rukuni daga rukunnan addnin musulunci. kuma akwai wadatuwa a cikin waxannan idodi guda biyu ga musulmai da alheri da albarkatu da amfani mai yawa. Kuma sun zama a madadin iduka na jahilyya.
An karvo daga Anas ya ce, “Manzon Allah (ﷺ) ya zo Madina ya iske suna da kwanaki biyu da suke wasanni a cikinsu, sai ya ce, “Waxanne kwanaki ne waxannan?” suka ce. “Mun kasance muna wasa a cikinsu a jahiliyya” sai ya ce, “Haqiqa Allah ya musanya muku da mafi alheri daga gare su: idin qaramar Sallah, da idin Babbar Sallah” Abu Dawud da Nasa’i ne suka rawaito shi.
Domin kowace al’umma tana da iduka da suka qunshi ma’anonin wannan addinin, da manufofinsa, da burace-buracen mabiyansa da kuma irin ibadojinsa.
Allah Ta’ala ya ce,
( لِكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنَا مَنْسَكًا هُمْ نَاسِكُوهُ ) [الحج: 67]
(Kowace al’umma mun sanya mata idin da suke yi).
Ibn Abbas (R.A) ya fassara ma’anar (mansak): da idi. Ibn Jarir ne ya rawaito.
Al’ummomin da suke da addinin da aka saukar Allah ya sanya musu kwanakin idi don samun lada. Waxanda kuma ba su da wani saukakken addini Allah ya qaddar musu riqar wasu kwanaki a matsayin kwanakin idi, don su qara tsunduma cikin vata.
Idi a shari’ar Annabi su ne idin layya, da idin qaramar sallah, da idin juma’a. Savanin haka kuwa to bukukuwa ne na jahiliyya, da suke qara wa mutum nisanta daga Allah. Kamar dai bikin ranar haihuwa.
Ya ku bayin Allah: Idi ya qunshi wasu ma’anoni na musulunci manya-manya, da amfani mai yawa. Idi ya qunshi aqidar Musulunci tsarkakakkiyya tataciyya, wadda take ita ce mafi girman ni’ima da Allah ya yi wa xan Adam. Haka kuwa na tabbatar ta hanyar girmama Allah da kabbar gare shi, da kuma yabo da kirari a gare shi. Tare da shaidawa cewa, shi ne Ubangijin gaskiya wanda Musulmi yake neman kusanci zuwa gare shi, ta hanyar roqo da fata, da neman taimako da dukkan nau’o’in ibada, ba tare da tara bautarsa da wani abu ba, kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:
( وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا 18 ) [الجن: 18]
(Kuma masallatai na Allah ne, don haka kada ku kira wani tare da Allah).
Shaidawa da gaskiya cewa Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Mazonsa ne, ta hanyar bin umarninsa, da barin haninsa, da gaskanta labarinsa, da bautawa Allah da abin da ya shar;anta. Idi ya qunshi bayanin shari’ar musulunci, ta hanyar bayyana alamomi na idi, da gabatar da sallarsa, da bayyana hukunce-hukuncen musulunci a huxubarsa.
Idi ya qunshi tsarkake xabi’u, da kyautata halaye, ta hanyar kwaxaitarwa a kan haquri da juriya, da sa da zumunci a cikin wannan ranar, da afuwa, da tsarkake zukata daga qullata da hassada da gaba. Domin Idi yini ne na farin ciki da ‘yan’uwantaka ta Musulunci.
Idi ya qunshi alaqa ta ‘yan uwantaka tsakanin Musulmi, da tallafawa ta zamantakewa ta hanyar ba da zakkar Fid-da-kai kafin sallah, saboda faxinsa: “Ku wadatar da su ga barin yawon ruqo a wannan yini”. Yana nufin faqirai. Daru Quxni ne ya rawaito shi daga Ibn Umar.
Idi ya qunshi sauqin musulunci da rangwamensa, domin a wannan ranar Allah ya wajabta aje azumi, ya halarta daxaxan abubuwa, kamar yadda yake gabanin azumi wajen halatta su. Sai dai musulunci ya qulla wannan da babban tushe, wato imani da miqa wuya ga Ubangijin talilkai, ya buxe farin cikin idi da murnarsa ta hanyar buxe shi da salla raka’a biyu da Allah Ta’ala. Don kada musulmi ya shantake wajen holewa ya manta da Ubangijinsa, wanda ya raine shi da ni’imomisa, ya ije masa bala’i, Allah Ta’ala ya ce;
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا لَا تُحَرِّمُوا طَيِّبَاتِ مَا أَحَلَّ اللَّهُ لَكُمْ وَلَا تَعْتَدُوا إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ87 وَكُلُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللَّهُ حَلَالًا طَيِّبًا وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي أَنْتُمْ بِهِ مُؤْمِنُونَ 88 ) [المائدة:87 - 88]
(Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku haramta daxaxan abubuwa da Allah ya halatta muku, kuma kada ku wuce iyaka, haqiqa Allah ba ya son masu wuce iyaka. Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halak mai daxi, kuma ku ji tsoron Allah wanda kuka yi imani da shi).
Ya ku bayin Allah, akwai hukunce-hukunce a waxannan kwanaki, daga cikin su akwai cewa, Allah ya shar’anta mana kabarbari bayan kammala azumin watan ramadan, sai ya ce,
( وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ 185 ) [البقرة: 185]
(Kuma domin ku cika adadi, kuma ku girmama Allah saboda shiriyar ku da ya yi, ko kwa godewa Allah).
Annabi (ﷺ) ya yi umarni da sallar Idi ga maza da mata har da kullallun mata waxanda ba al’adarsu ba ce su fita, da masu haila, domin su halarci addu’ar alheri, da addu’ar musulmi, su qauracewa wajan Sallah, kada su zauna cikin filin idin, domin filin idi masallaci ne, yana da duk hukunce-hukuncen masallaci.
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Ummu Axiyya (R.A) ta ce, “Manzon Allah (ﷺ) ya umarce mu da fitar da masu haila da kullallun mata, su masu haila su nisanci salla.- wani lafazin-: Su nisanci wajen Sallah, su halarci alheri da addu’ar musulmi, sai na ce, “Ya Ma’aikin Allah idan xayarmu ba ta da riga” sai ya ce, “’'Yar uwarta ta tufatar da ita da rigarta.”
Ku fito ya ku Musulmi zuwa sallar Idi, mazanku da matanku, yara da manya, don bauta ga Allah, da aiwatar da umarnin Manzon Allah, da neman alheri, da addu’ar Musulmi. Da yawa alheri da kyaututtuka kan sauka a filin idi daga Ubangiji mai girma, addu’o’i tsarkaka da ake karvar su suna gudana a wannan guri. Mazaje su fita suna masu tsabta, suna masu sanya turare, suna masu sanya mafi kyawun tufafinsu. Sai dai bai halatta su sa alharini ba, da kowane abu na zinare, domin su haramun ne ga maza. Mata su fita cikin kamun kai, ba tare da sun sa turare ko bayyana ado ba.
Sunna ce mutum ya ci dabino kafin ya fita sallar idi, ya ci wuturi, uku ko biyar ko sama da haka in ya so, ya dai tsaya a kan mara. Anas xan Malik (R.A) ya ce, “Annabi (ﷺ) ya kasance ba ya fita da safe ranar idi har sai ya ci dabinai, kuma yana cin su mara”
Haqiqa Allah mabuwayi mai xaukaka ya ce,
( لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآَخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا 21 ) [الأحزاب: 21]
(Haqiqa kuna da abin koyi kyakkyawa cikin lamarin Manzon Allah, ga wanda ya ke qaunar rahamar Allah da ladan ranar lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa).
Ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah - ku sadar da zumunci, domin ma’abata ‘yan uwantakar jini, sashinsu shi ne mafi cancanta da sashi. Ku sadar da zamuncinsu, ko da sun yanke muku naku zumuncin. Allah ya dauwamar muku da albarkatunsa, ya yalawata muku arzikinku, ya albarkaci rayuwarku.
Ina neman tsari da Allah daga shaixani abin la’anta:
( إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ وَالْإِحْسَانِ وَإِيتَاءِ ذِي الْقُرْبَى وَيَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ وَالْبَغْيِ يَعِظُكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ 90 ) [النحل: 90]
(Haqiqa Allah yana umarni da adalci da kyautatawa, da ba wa makusanta, kuma yana hani a kan alfasha da mummunan aiki, da zalunci. Yana yi muku wa’azi, tsammaninku za ku wa’azantu).