islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


bikin (idin) babbar salla


6659
Surantawa
Haqiqa idin babbar sallah idi ne na layya, kuma idi ne na karamci da tausayawa ga mabukata, wani irin idi ne wanda miliyoyin musulmi suke haduwa domin aiwatar da mafi girman shaira (alama cikin alamomin addini) wato hajji. Haka nan a idin layya ne karamcin masu karamci ke bayyana wajen layya da yanka, domin neman kusanci zuwa ga Allah, da kuma rabawa matalauta da mabukata.

Manufofin huxubar

Bayanin yin layya.

Bayanin sharaxan layya da ladubbanta

Umarni da kaxaita Allah da tsoratarwa game da wasu savon Allah na fili.

Wasiyyoyi ga xaukakin vangarorin al’umma

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ya ku ‘yan’uwa a musulunci! Ina yi wa kai na da ku wasiyya da jin tsoron Allah maxaukakin sarki, domin wannan ita ce wasiyyarsa ga bayinsa na farko da na qarshe. Allah maxaukakin sarki yana cewa:

( وَلَقَدْ وَصَّيْنَا الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ وَإِيَّاكُمْ أَنِ اتَّقُوا اللَّهَ ) [النساء: 131] .

(Haqiqa mun yi wasicci ga waxanda muka baiwa littafi gabaninku da ku kanku, da ku ji tsoron Allah).

Ya ku bayin Allah, shin kun san kowace rana ce wannan? Ita ce ranar idin babbar sallah mai girma wanda Allah ya xaukaka ta kuma ya girmama matsayinta, kuma ya ambace ta da sunan Ranar Babban Hajji. Domin alhazai suna aiwatar da mafi girman ayyukan hajjinsu a cikinsa. Sukan yi jifan shexan, su yanka abin yankansu, su aske kawunansu, su yi xawafi ga xakin Allah, sannan su yi sa’ayi tsakanin Safa da Marwa. A wannan rana ne, alhazai suke babban shirin dunfarar filin Mina, bayan sun tsaya a waje mai girma, wajen tsayuwar Arfa. Sun xaga hannayensu cikin qanqan da kai zuwa ga Allah. Sun zubar da hawaye na tsoron Allah domin neman tuba da komawa ga Allah. Sannan sun nemi taimako a gurin wanda duk wani taimako da datarwa ke hannunsa. Sannan sun hari Muzdalifa, sun kwana a nan, duk domin biyayya ga sunnar Mustafa (ﷺ), wanda yake cewa: “Ku koyi ayyukan hajjinku daga gurina”

Ya ku bayin Allah. Allah ya sanya wannan rana, ranar biki da farin ciki, wanda albarkasa da falalarsa da alherinsa yake komawa ga musulmi gabaxaya. A wannan rana musulmai sukan qara kusantar Ubangijinsu ta hanyar yanka hadayarsu, domin biyayya ga sunnar Manzon Allah (ﷺ). Domin Manzon Allah (ﷺ), ya yi yanka hadayarsa da kansa, da hannunsa mai albarka. Ya soke raquma sittin da uku a hajjinsa ta bankwana. Bukhari da Muslim sun rawaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya yi layya da raguna guda biyu qosassu, masu qaho. Ya yanka su da hannunsa, ya ambaci sunan Allah sannan ya yi kabbara.

Allahu Akbar! Allahu Akbar!! La’ilaha illal lah, Allahu Akbar, Allahu Akbar walil lahil hamd.

Ya ku musulmai, haqiqa akwai falala mai girma da lada gwaggwava ga wanda ya raya sunnar yin layya. An samo hadisi daga manzon Allah ya ce: “ Babu wani aiki da da xan’adam zai yi a ranar babbar sallah, wanda Allah ya fi so, sama da zubar da jini (yanka abin yanka), kuma ita (abin yankan) za ta zo ranar alqiyama da kofatunta da qahonninta da gashinta. Kuma jinin da aka zubar yana da wata daraja a wurin Allah tun kafin ya zuba a qasa. Kuma wanda ya yi layya ana ba shi lada a kowane gashin na jikin dabbar, da ko wane sufi nata. Don haka, ku jiyar da kanku daxi da ita). Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito.

Yana daga cikin abin da ya kamata a sani, Allah ya tsare ku, shi ne akwai sharuxxa guda uku game da abin layya.

Na farkon su shi ne: Cikar shekarun da aka ambata a shar’ance. Wanda shi ne shekara biyar ga raqumi, da kuma shekara biyu ga shanu, da shekara xaya ga tumaki da kuma rabin shekara ga awaki.

Sharaxi na biyu: Ya kasance abin da za a yanka xin lafiyye ne marar illa, wanda zai ta hana a yi layyar da shi. Kuma manzon Allah ya bayyana hakan, idan ya bayyana cewa, (Nau’in dabbobi guda huxu ba sa wadatarwa a layya. Daga ciki akwai gurguwa da gurguntakar ta bayyana sosai, sai kuma mai makantar da makantar ta bayyana, da kuma dabba mara lafiya, wadda rashin lafiyar ta bayyana, da ramamma marar kitse). Imam Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi da Nisa'i suka ruwaito shi daga Bara’u xan Azib, Allah ya yarda da shi.

Sharxi na Uku: A yanka abin layyar a cikin lokacin da shari’a ta qayyade. Lokacin shi ne, daga fitowar rana a ranar idi, zuwa faxuwar rana, a rana ta uku. Amma abin da ya fi falala shi ne a ranar farko. Kuma babu laifi a yanka da daddare. Kuma akuya guda xaya za ta ishi mutum xaya da iyalan gidansa, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Ayyub, Allah ya yarda da shi.

Allah Akbar! Allah Akbar!! Allah Akbar!!! La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamdu.

Ya ku ‘yan’uwa masu yin layya, ya kamata a gare ku kyautata a wurin yankanku, ta hanyar wasa wuqa, domin hutar da abin da za a yanka, da kuma tausaya masa. Sannan kuma akan kwantar da shi ne daga vangaren hagunsa. Kuma abin da ya inganta a sunna game da naman da aka yanka shi ne, mutum ya ci wani abu daga ciki, sannan ya yi sadaka da wani kaso, sannan kuma ya kyauta da wani. Kuma sannan an fi so mutum ya yanka da kansa, ko kuma ya kasance yana wurin a lokacin da za a yi yankan. Kuma ba a ba wa mahauci ladan aikinsa daga cikin naman da aka yanka. Ubangiji maxaukaki sarki yana cewa,

( فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ 2 ) [الكوثر: 2]

(Ka yi sallah domin Ubangijinka, kuma ka yi yanka)

Allah Akbar Allah Akbar Allah Akbar, La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamdu.

Ya ‘yan’uwa a Musulunci, ana lissafa wannan taron, ta vangaren ginuwarsa da albarkarsa da hikimar yinsa, a matsayin wani abu da yake bayyana haxin kan musulunci. Allah yana cewa:

( إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ ) [الحجرات: 10]

(Lallai muminai ‘yan’uwa ne).

Allah ya qara da cewa:

( إِنَّ هَذِهِ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً ) [الأنبياء: 92] .

(Wannan al’umma taku alumma ce guda xaya)

Allah yana cewa:

( وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآَخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ 85 ) [آل عمران: 85]

(Kuma wanda ya nemi wini addini ba musulunci, to, ba za a karva daga gare shi ba. Kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara).

Sannan Allah yana cewa:

( وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اُعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ 36 ) [النحل: 36].

(Haqiqa mun aika wa kowace al’umma da manzo da cewa, ku bautawa Allah ku qauracewa duk wani xagutu).

To waye wanda ya halicci bayi, ya azurta su, kuma ya samar musu da ji da gani da hankali da tunani, ba Allah shi kaxai ba? Kuma ba wani abu kwatankwacinsa, daga cikin mala’iku ko annabawa ko mutane da duwatsu ko waliyyai wanda za a iya daidaita shi da Allah ko wane ne. Ba wanda yake iya samarwa da kansa wani abin amfani, ko abin cutarwa, kuma ba su da ta cewa game da mutuwa ko rayuwa ko tashi a ranar qarshe. Yana daga abin mamaki ka ga wasu suna neman kusanci ga wani abin halitta mai rauni, kuma faqiri, sannan su manta da wanda ya yi halitta mai qarfi kuma wanda yake mawadaci.

( آَللَّهُ خَيْرٌ أَمَّا يُشْرِكُونَ 59 ) [النمل: 59] .

(Shin Allah shi ne mafi alheri ko kuma abin da suka shirka da shi).

( أَأَرْبَابٌ مُتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ 39 ) [يوسف: 39]

(Wasu iyayengiji mabanbanta su ne suka fi alheri, ko kuwa Allah kaxaitacce mai qarfi).

Tsarki ya tabbata a gare shi kuma ya xaukaka daga abin da suke haxa shi da shi.

Ya bayin Allah, ya zama wajibi ga bayi su kaxaita Ubangijinsu a cikin duk abubuwan da suke yi da kuma a duk halin da suke ciki. Ba a yin sallah sai don Allah, ba a yin addu’a sai don shi, ba a yanka, ba a bakance, ba a neman kusanci, sai da Allah, ba a rantsuwa ba a neman taimako sa ga Allah.

( قُلْ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ 162 لَا شَرِيكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ 163 ) [الأنعام: 162 - 163]

.

(Ka ce sallata da yankana da rayuwata da mutuwata duk na Allah ne Ubangijin talikai. Ba shi da abokin tarayya, da wannan aka umarce ni, kuma ni ne farkon masu miqa wuya).

Ya bayin Allah ku ji tsoron zuwa wajen masu sihiri da masu duba da bokaye, da masu da’awar sanin gaibu:

( قُلْ أَفَرَأَيْتُمْ مَا تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ إِنْ أَرَادَنِيَ اللَّهُ بِضُرٍّ هَلْ هُنَّ كَاشِفَاتُ ضُرِّهِ أَوْ أَرَادَنِي بِرَحْمَةٍ هَلْ هُنَّ مُمْسِكَاتُ رَحْمَتِهِ قُلْ حَسْبِيَ اللَّهُ عَلَيْهِ يَتَوَكَّلُ الْمُتَوَكِّلُونَ 38 ) [الزمر: 38].

“Ka ce, “Ashe to kun gani abin da kuke kira, waxanda suke wanin Allah ne, idan Allah ya nufe ni da wata cuta, shin, su abubuwan nan masu yaye min cutarsa ne? Ko kuma ya nufe ni da wata rahama, shin, su abubuwan nan masu hana ni rahamarsa ne?” Ka ce, “Mai isata Allah ne, gare Shi masu tawakkali ke dogara).

Ya ku shugabannin musulmai, ya ku masu riqe da madafun iko, lallai abin da ke wuyanku a gaban Allah abu ne mai girma. Domin lallai Allah yakan kawar da wani abu ta hanyar shugaba ba tare da ya kawar da shi ta hanyar Alqur’ani ba. Ku yi jagorancin mutanenku da littafin Allah, ku yi hukunci da sunnar manzon Allah, ku tsayar da addini. Ku riqe Allah yana cewa:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآَخِرِ ذَلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا 59 ) [النساء: 59]

(Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi xa’a ga Allah kuma ku yi xa’a ga Manzonsa, da shugabanni daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa, idan kun kasance kun yi imani da Allah da ranar lahira, wannan shi ne mafi alheri gare ku, kuma shi ne mafi kyan makoma).

Malaman musulunci, matsayinku a wannan addini mai girma ne. Ku ne magada annabaw,a kuma halifofin manzanni, masu bijiro da gyara, kuma amintattu game da isar da kiran Allah da bayani. Ku tashi ku yi tsayuwar daka wajen isar da abin da ya wajaba a kanku. Ku guji karkatar da ilimi don xan wani abin qashin miya. Ku zama ababan koyi na gari ga jama’a.

Allah yana cewa,

( وَلْتَكُنْ مِنْكُمْ أُمَّةٌ يَدْعُونَ إِلَى الْخَيْرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ 104 ) [آل عمران: 104]

(Lalle a samu wata al’umma daga cikinku da za su riqa kira zuwa ga alheri, kuma suna umarni da kyakkyawan abu, kuma suna hana mummuna. Waxannan su ne masu cin babban nasara).

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa tsarkakakkiya mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu yake so, kuma ya yarda. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya, yana da sunaye mafiya kyau, da sifofi maxaukaka. Kuma ina shaidawa cewa Annabinmu Muhammad bawan Allah ne kuma manzonsa ne, masoyinsa ne kuma badaxayinsa ne, kuma shi ne amintaccensa a kan wahayinsa, kuma shi ne zavavve a cikin halittunsa kuma maxaukaki, daga manzanninsa, Allah ya turo shi mai shiryarwa, mai bushara mai gargaxi, kuma mai kira zuwa ga Allah da izininsa kuma fitila ce mai haskakawa. Ubangiji ya qara daxin tsira a gare shi, da iyalansa da sahabbansa da matansa da ‘yan’uwansa da mabiyansa, da daxin tsira da aminci mai yawa.

Allah Akbar Allah Akbar Allah Akbar, La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamdu.

Ya ku musulmai, ku tuna haxuwarku irin wannan, ranar da Allah zai haxa na farko da na qarshe, domin rarrabe hukunci a tsakaninsu. A cikinsu akwai wanda zai karvi littafinsa da hannun dama, akwai kuma wanda zai karvi littafinsa da hannun hagu. Ku tuna, ya ku bayin Allah, ranar da za a tashe ku zuwa ga Ubangijinku zai tashe ku a cikin tsaraici ba takalma, kuna masu lova, kamar yadda iyayenku suka haife ku, idanuwa sun yi muku zuru-zuru. Ku tuna ya ku bayin Allah, ku tuna mutuwa da magaginta, da qabari da duhunsa da tashi a ranar lahira da ximautarsa. Don haka ku yi shiri don tunkarar wannan ta hanyar tuba na gaskiya da ayyukan kirki waxanda za su kusantar da ku zuwa ga Allah. Sayyidina Abubakar Allah ya yarda da shi yana cewa: “Kowane mutum mai wayar gari ne a cikin iyalansa, amma kuma mutuwa ta fi kusa da shi sama da hancin takalminsa.

Ya ‘yan’uwa na aqida, gida na musulunci wani tubali ne na ginin al’ummar musulma a addinin musulunci. Ta hanyar gyaruwar zamantakewar iyali ne al’umma duka take gyaruwa, idan kuma suka vaci, komai na al’umma yakan vaci, kuma rukunan al’ummar sukan sakwarkwace. Saboda haka ya zama wajibi a kan miji da mata da ‘ya’ya su tabbatar da gyaruwa gidansu. Kuma su samar da tarbiyya mai kyau. Kuma su toshe duk wata hanya da kan iya kawo varaka. Kuma ya zama tilas a kan mata da miji, kowannensu ya sauke haqqin xan uwansa da yake kansa. Duk wata matsala ta zamantakewar iyali, da yawan sake-saken aure a cikin al’umma, da sauran abubuwan da suke tarwatsa gidaje, sai kawai don qin aiwatar da abin da ya dace daga vangaren mata da miji. Kowannensu ya qi yin abin da ya kamata ya yi. Sau nawa irin wannan ya zama sababin lalacewar ‘ya’ya, har ma suka zama abin farautar mutanen banza. Saboda haka ya zama dole a kanmu mu haxa kai gaba xaya don ganin mun samar da mafita ga wannan matsaloli a cikin al’umma. Kuma waxanda suke malamai da shugabanni da marubuta, ya kamata su ba wa wannan matsala haqqin da ya kamata. Ya bayin Allah, al’amarin aure, da tsadar sadaki, da lalacewar ‘yan mata, da nuna alfahari, da xorawa kai abin da bai kamata ba, da varnatar da dukiya da almubazzaranci, duk abubuwa ne da ya kamata a lura da su.

Ya ku matasa, duk burin wanna al’umma yana kanku, ku ne manyan gobe. Ya kamata ku tashi wajen ganin kun sauke nauyin da yake kanku. Ku ne jikiokin jaruman farko na wannan al’umma waxanda suka jagoranci buxe garuruwa da musulunci. Don haka ku tashi tsaye ku yi abin da ya kamata ku yi. Ku san matsayinku, ku yi riqo da addininku. Kuma ku nemi haxin kai da malamanku, kuma ku riqi hanyar da take ita ce madaidaiciya, tsakatsakiya ba tare da shisshigi ko kasawa ba. Haka kuma banda zaqewa, kuma ban da lalaci. Ku guji aukawa cikin gafala da sha’awar zuciya, da kuma kutsawa cikin shubuhohi.

Ya ‘yan matan musulmai, ku ji tsoron Allah, ku kiyaye kanku ta hanyar kamewa, da kunya da hijabi. Ku kasance mata musulmai, muminai, masu tawali’u. Ku a musulunci wani abu ne mai karamci kuma mai tsada. Don haka ku masu ilimi game abin da maqiya musulunci suke qullawa, waxanda suke son cutar da ku ta hanyar yaxa tsaraici da cakuxuwar maza da mata, da halatta abubuwan da Allah ya haramta. Ku tashi tsaye wajen aikinku na tarbiyya ga ‘yan baya masu tasowa.

Ya ‘yan’uwa musulunci, ku kula da sallah domin ita ce tushen addininku. Ba wani rabo a cikin addinin musulunci ga wanda ya bar sallah. Ku xabi’antu da xabi’un musulunci masu kyau. Kuma ku guji furta abubuwa ba tare da xabbaqa su ba. Domin shi addinin musulunci ba kawai a faxa da baki ba ne, abu ne da ya shiga zuciya, kuma ayyuka sukan gaskata shi. Ku godewa Allah maxaukakin sarki a bisa dukkanin ni’imominsa da falalolinsa, domin addininku na musulunci yana tabbatar da nutsuwa, yana kuma kore kokwanto da kwan-gaba-kwan-baya, da rashin tabbas. Allah ya yi gaskiya da yake cewa:

( وَمَنْ يَعْشُ عَنْ ذِكْرِ الرَّحْمَنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌ 36 وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ مُهْتَدُونَ 37 ) [الزخرف:36 - 37]

(Kuma wanda ya bijirewa ambaton Allah Mai rahama, to, za mu haxa shi da shaixan shi ne abokinsa. Kuma lallai su, haqiqa suna kange su daga hanya, kuma suna zaton cewa su shiryayyu ne).

Allah Akbar! Allah Akbar!! Allah Akbar!! La’ilaha illallah, wallahu akbar Allah Akbar, walillahil hamd.