islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Tsarkin Mara Lafiya Da Sallarsa


11133
Surantawa
Sallah tana da shaani mai girma a zuciyar mumini, zaka ga yana kiyaye ta a duk lokutansa, kuma kowane yanayi yake. Duk da yake a wasu lokutan, wasu matsaloli zasu iya fadowa mutum kamar rashin lafiya, to a irn wannan yanayi ma, musulunci bai gafala ba wajen bayyana masa abinda ya wajaba kanshi a irin wannan yanayi, yayi masa bayanin yadda zaiyi tsarki, da yadda zaiyi sallah, da yada zaiyi azumi, tare da yimasa rangwame mai girma dake bayyana rahamar Allah wajen rangwame ga bayinsa.

Manufofin huxubar

Tunatarwa a kan muhimmancin kiyaye sallah

Bayanin sunnar jarraba, da roqon Allah lafiya

Gargaxi a kan xabi’ar sakacin marasa lafiya da sallah

Wayar dakan likitoci da masu kula da marasa lafiya

Huxuba Ta Farko

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhamamdu bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suk a yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancanci a ji tsoronsa kuma kada ku mutu face kuna musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kumamafi kyawun shiriya shiriyar Annabi (ﷺ), kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagagunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi’a ce, kuma duk wata bidi’a vata ce, kuma duk wani vata yana wuta.

Bayan haka:

Ya kai musulmi, ka yi sani - Allah ya datar da ni da kai zuwa dukkan alheri – cewa Allah mai buwaya da xaukaka, mai hikima ne cikin jarrabarsa ga bayinsa da abin da yake jarrabasu da shi. Shi yakan jarrabesu wani lokacin da abin farin ciki, wani lokacin kuwa da tsanani, duk wannan jarrabawar da gwadawar domin ya bayyana godiyar mai godiya da haqurin mai haquri. Allah mai girma da xaukaka yana cewa,

( وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّى نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنْكُمْ وَالصَّابِرِينَ وَنَبْلُوَ أَخْبَارَكُمْ 31 ) [محمد: 31]

(Kuma wallahi za mu jarrabe ku don mu san masu jihadi daga cikinku, da masu haquri, kuma don mu jarraba haqiqanin lamarinku).

Yana jarrabasu da farin ciki da tsanani. An karvo daga Suhaib Ar-Rumi (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, Mamakin lamarin mumini, shi lamarinsa dukkaninsa alheri ne, kuma babu mai wannan sai mumini, idan farin ciki ya same shi sai ya gode, sai ya zama alheri gare shi, idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haquri sai ya zama alheri gare shi. Muslim ne ya rawaito shi.

Kenan Mumini yayin bala’i yana haquri yana yarda yana qaunar abin da Allah yayi wa masu haquri alqawari da shi, Allah ya ce,

( إِنَّمَا يُوَفَّى الصَّابِرُونَ أَجْرَهُمْ بِغَيْرِ حِسَابٍ 10 ) [الزمر: 10]

(Kaxai ana cikawa masu haquri ladansu ba tare da lissafi ba).

Kuma ya ce,

( وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ 155 الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُمْ مُصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ156 أُولَئِكَ عَلَيْهِمْ صَلَوَاتٌ مِنْ رَبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُهْتَدُونَ 157 ) [البقرة: 157]

(Kuma ka yi wa masu haquri bushara. Waxanda idan masifa ta same su sai su ce,, mu ga Allah muke, kuma mu zuwa gare shi muke komawa. Waxannan suna da tsira daga Ubangijinsu da rahama, kuma waxannan su ne shiryaiya).

An karvo daga Abu Sa’id da Abu Hurairah (R.A) daga Annabi (ﷺ) ya ce, (Babu wani Abu da zai sami mumini na raxaxi, ko wahala, ko damuwa, ko vaqin ciki, ko cuta, har qaya da zai taka ta, face Allah ya kankare masa zunubinsa da ita). Bukhari ne ya rawaito shi. Ya kai musulmi, muslmi ba ya fatan bala’i, ba ya taro bala’i, domin shi bai sani ba zai iya haquri ko zai iya fushi, don haka ne yayin da Al’abbas baffan Annabi (ﷺ) ya yi tambaya cewa, wace addu’a zai yi, sai Annabi (ﷺ) ya ce, “Ya baffana, ka tambayi lafiya, sai ya maimaita masa tambyaar sau dayawa shi kuma yana ce masa, "Ya banfan Manzon Allah ka roqi Allah lafiya) Ahmad ne ya rawaito shi, da Bukhari cikin Al’adabul Mufrad, da Tirmizi kuma ya inganta shi.

Yakai Musulmi ka kusanci Allah a lokacin lafiyarka da qarfinka da abin da za ka iya na biyayya, domin idan ka aikata haka sannan ka gajiya, to Allah zai rubuta maka ladan abin da ka kasance kana aikata shi cikin halin lafiyarka. Kuma an karvo daga Abu Musa (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Idan bawa ya yi rahsin lafiya ko ya yi tafiya za a rubuta masa abin da ya kasance yana aikatawa yana halin zaman gida mai lafiya). Bukhari da Abu Dawud ne suka rawaito shi.

Ya ku bayin Allah, Allah mai girma da buwaya yana cewa,

( إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَوْقُوتًا 103 ) [النساء: 103]

(Lalle sallah ta kasance ga muminai abin wajabtawa ne bisa lokatai). Ma’ana, abar wajabtawa a lokatai kevantattu da Allah mai vuwaya da xaukaka ya vayyanasu, kuma Annabi (ﷺ) ya qara filla-filla da su. Sai Allah mai girma ya bayyana muhimmancin sallah da girman sha’aninta, kuma cewa ita an wajabtata a kan muminai bisa lokuta a lokuta na musamman.

Ya kai musulmi, haqiqa yana daga xabi’ar Musulmi kulawa da sallah da lura da ita, da dauwamar aikatar da ita da kiyayeta, ga shi Allah ta’ala yana cewa,

( الَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلَاتِهِمْ دَائِمُونَ 23 ) [المعارج: 23]

(Waxanda suke madauwama a kan sallarsu).

Kuma yake cewa,

( وَالَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ34 أُولَئِكَ فِي جَنَّاتٍ مُكْرَمُونَ35 ) [المعارج:34 - 35]

(Waxanda suke kiyaye sallarsu. Waxannan suna cikin aljannatai ababan girmamawa).

Kenan sallah sha’aninta a zuciyar mumini sha’ani ne mai girma, yana kiyaye ta, yana lazimtar ta, ba ya rabuwa da ita matuqar hankalinsa yana nan, matuqar yana ji, yana hankaltar abin da yake faxa, to lallai ana nemansa da ya yi sallah. Allah ta’ala ya ce game da Isah xan Maryama:

ýوَأَوْصَانِي بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ مَا دُمْتُ حَيًّا 31 ) [مريم: 31] ( (Kuma ya yi min wasiyya da sallah da zakka matuqar ina raye).

Ya kai Musulmi, lallai wasu daga cikin musulmi sukan yi sakaci cikin sallah, ba don kasala wajen yin ta ba, ba kuma don wulaqantata ba, sai dai wasu shubuhohi da kan bijiro musu, da suke sa su su jinkirta yin sallah a lokacinta, musamman wanda aka jarraba da wata cuta, wannan cutar kan iya sanya shi ya jinkirta sallah daga lokacinta, da jinkirta ta zuwa wani lokaci daban, har ya warke daga wananan cuta da ta same shi. Yana ganin cewa wannan cutar za ta hana shi yin wannan sallah, da cika sahradanta da wajibanta, sai ka gan shi yana sakaci da sallah saboda jahilci, ba wai kasala ba, ko wulaqanci da ita.

Ya kai musulmi! Abu ne sananne cewa tsarki daga najasa da kari, da najasar tufafi da ta jiki da bagiren da zai yi sallar, sharaxi ne na ingancin sallah; domin Allah ta’ala yana cewa:

وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ 4 ) [المدثر: 4] ( (Kuma ka tsarkake tufafinka). Kuma Annabi (ﷺ) yana cewa game da mutum bi yu da ake azabatar da su a cikin qaburburansu: "Shi dai xayansu ya kasance ba ya kaffa-kaffa da bawali) Bukhari ne yarawaito daga hadisin Jabir (R.A).

Kuma an karvo daga Ibn Abbas (R.A) ya c, "Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Mafi yawancin azabar qabari daga bawali ne, don haka ku tsarkaka daga bawali". Bazzar da Xabarani da Hakim da Daru quxuni ne suka ruwaito shi. Kuma Annabi (ﷺ) yana cewa, "Ba a karvar sallar xayanku idan ya yi kari har sai ya yi alwala". Muslim ne ya rawaito shi daga hadisin Abi Huraira (R.A). Sai ya nuna mana sharxanta tsarki ga jiki da tufafi da gurin da mutum ke sallah a kanta, wannan abu ne da ake nema a shari’ah.

Sai dai mara lafiya wani lokaci yakan iya gazawa game da waxannan abubuwa, ya iya kasancewa rashin lafiya ne ya hana shi yin tsarki da ruwa, ko ya hana shi wanke gavvan alwarsa da ruwa. Idan ya sami ikon yin haka ko aka sama masa wanda zai taimaka masa a kan alwala, to wannan ni’ima ce daga Allah. Sai dai idan haka ya yi masa wuya ya kasa yin alwala da ruwa, ko don rashinsa, ko kasa amfani shi, ko idan yin amfani da shi yakan qara masa rashin lafiya, ko ya jinkirta warkewa, domin Allah ta’ala ya sanya masa musayar haka, shi ne taimama, Allah ta’ala ya ce,

( فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ ) [النساء: 43]

(Idan ba ku sami ruwa ba, to ku yi taimama a qasa tsarkakkiya, ku shafi fuskokinku da hannayenku da su).

Idan kuma aka qaddara cewa, ba zai iya alwala da ruwa ba, kuma ba shi da abin da zai yi taimama da shi, kuma lamarin ya yi wahala, to zai yi sallah a halin da ya sami kansa. Allah yana cewa,

( وَمَا جَعَلَ عَلَيْكُمْ فِي الدِّينِ مِنْ حَرَج ) [الحج: 78].

(Allah bai sanya muku wahala a cikin addini ba).

Ya kai Musulm! Wani lokacin rashin lafiya ya iya samun musulmi a sashin gavvansa na alwala, ta yadda ba zai iya bi ta kansu da ruwa ba, wannan yana da hali biyu; ko dai wannan gavar ta zama a lulluve da abin rufewa wanda za a iya shafa akansa ta samansa, wannan za a yi shafa a kan abin da aka lulluve shi da shi na maxauri, sai ya yi shafa akansa yayin alawala, kuma shafar ta wadatar; domin wannan shafar tana daidai da wanki, ko kuma ya zama ba za a iya wanke wannan gavar da ruwa ba, kuma samun ruwa komai qanqantar sa zai yi tasiri bisa raunin, to a nan sai ya yi taimama. An karvo daga Abdullahi xan Abbas ya ce: rauni ya sami wani mutum a zamin Manzon Allah (ﷺ), sannan ya yi mafarki, sai aka umarce shi da yin wanka, kuma ya yi wankan ya mutu. Da labari ya zo ga Annabi (ﷺ) sai ya ce, "Sun kashe shi; Allah ya wadan su, ashe ba maganin rashin sani ita ce tambaya ba?" Abu Dawud, da ibn Khuzaimah, da Ibn Hibban ne suka ruwaito shi.

Idan duk haka ya faskara, to sai ya yi shafa a kan makarin da ruwa, in kuma hakan ma ya yi wuya, to sai ya yi taimama ga wannan gavar.

Ya ku bayin Allah!

kowane musulmi ana nemansa da ya yi sallolin farilla, matuqar hankalinsa na nan, matuqar yana ganewa yana fahimta, to a na nemansa da wannan sallar gwargwadon iyawarsa, kuma sallar farilla ba ta faxuwa daga gare shi matuqar yana fahimta; domin wannan farilla rukuni ne daga rukunan musulunci, kuma dalili ne na gaskiya bisa abin da ke cikin zuciya na musulunci da imani; tana nuni a bisa lazimtar musulunci da gaskiya, ita tana daga mafi girman farillan musulunci, kuma mafi darajarta bayan tauhidi domin musulmi ana nemansa da sallah a tafiyarsa da zaman gidansa, ana nemansa da ita a halin tsoronsa da kwanciyar hankalinsa, ana neman sa da ita a rashin lafiyarsa da cikin lafiyarsa, sallah ba ta tava saraya daga gare shi har abada, kuma halin magabatanmu na gari haka yake. Muhammadu shugaban na farko dana qarshe, jagoranmu Shugabanmu (ﷺ) ya kasance yana aiwatar da sallah a lokacin rashin lafiyarsa, ko da zaune yake, yana salla a zaune yayin da ya gajiya daga tsayuwa. An ba da labari cewa Anas (R.A) ya faxo daga kan doki sai ya daushe, sai ya kasance yana sallah a zaune. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Ya xan uwana, idan aka jarrabe ka da cuta, to ka sani cewa, salla dole ce, dole kuma a ba da ita a lokacinta, dole a kula da ita, kuma Ubangijin mu maigirma da xaukaka ba ya kallafawa bayi abin da ba za su iya ba, sai dai lamarin mai sauqi ne, Allah ta’ala yana faxa game da siffar Annabinsa (ﷺ),

وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَالْأَغْلَالَ الَّتِي كَانَتْ عَلَيْهِمْ) [الأعراف: 157] ) (Kuma yana sauke musu nauyinsu da takure-takuren da ke kansu).

Ka yi sallah a tsaye domin tsayuwa rukuni ne daga rukunan sallah, kuma ya wajba a bisa mara lafiya ya yi sallar farilla a tsaye, ko a sunkuye, ko a dogare a jikin garu, ko sanda da zai dogara akanta.

Idan ka gajiya game da tsayuwa, ko kana wahala, to ka yi sallah a zaun. Idan ka gaza zaman to, ka yi sallah a kan kwivinka. Idan ka kasa, to ka yi sallah a rigingine; Imaranu xan Husaini (R.A) ya ce, “Na kasance ina da Basur, sai na tambayi Manzon Allah (ﷺ)? Sai ya ce, "Ka yi sallah a tsaye. Idan ba za ka iya ba, to ka yi a zaune. Idan ba za ka iya ba, to a kan kwivinka). Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Manzon (ﷺ) ya ziyarci wani mara lafiya, sai ya ganshi yana sallah a kan wani matashi, sai ya karve shi, ya yi wurgi da shi. Sai ya sake xaukar wani itace zai yi sallah akansa; sai ya karve shi, ya yi jifa da shi, sannan ya ce, "Ka yi sallah a qasa in za ka iya, idan ba haka ba, ka yi nuni, ka sanya sujjadarka qasa-qasa daga ruku’inka). Baihaqi ne ya ruwaito shi daga Ibn Abbas, kuma Malam Albani ya ce hasan ne.

Wannan yana nufin dole a yi sallah a lokacin ta, ko da ka kasance a kwivinka ne, koda da nuni da kanka? Domin muhimmin lamari shi ne fahimtar zuciya da riskar abin da yake faxi.

Ya kai Musulmi, ka yi sallah a tsaye, in ka sami ikon ruku’u ka yi ruku’i a tsaye, idan ba za ka iya yin ruku'u a tsaye ba, ka yi nuni da ruku’i, sannan ka yi nuni da sujjada. Wato ka qudirianiyar cewa, kai yanzu kana yin ruku’i ne a haka, ko kana yin sujjada ne. Ka sanya kanka a cikin sujjada mafi qasa-qasa daga ruku’u, don ruku’u ya banbanta da sujjada.

Inko ba zaka iya nuni da kanka ba cikin ruku’i da sujjada, to sai ka yi amfani da idanuwanka, sai ka runtse kaxan wajen ruku’i, kuma ka runtse da sosai wajen sujjada.

Amma nuni da yatsa, kamar yadda wasu marasa lafiya suke aikatawa. Bai inganta ba, kuma ba shi da asali a Alqur’ani ko Sunnah, ko a cikin zantuttukan malamai.

Ya kai Musulmi ka sani cewa, Allah ya wajabta wa musulmi sallah yayin rincavewar yaqi da karafkiyar takubba. Ya wajbta musu sallah yayin da suke fuskantar abokin gabarsu, suna fito-na-fito da abokan gabarsu, to ina ga musulmin da ke cikin nutsuwarsa da kwanciyar hankali?

Allah ka ya fe mana ka karvi ibadunmu na qwarai ka sanar da mu addininmu, ka kuma karvi rayuwarmu muna musulmi. Ku ne mi gafar Ubangijinku shi mai gafara ne mai jin qai.

Huxuba Ta Biyu

Yabo ya tabbata ga Allah. Tsira da aminci su tabbata ga mafi xaukakar manzanni, Annabin mu Muhamamdu da alayensa da sahabbansa da wanda ya bi tafarkinsa har ya zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:

Ya ku musulmi, fuskantar Alqibla sharaxin ingancin sallah ne, wannan ba wani ruxani a cikinsa, sai dai idan mara lafiya ya kasa fuskantar alqibla ko a qaddara cewa gadon sa da shimfixarsa ba su kalli alqibla ba, kuma juya su ya faskara, to za ka yi sallah ne yadda ka samu halinka, wannan ba zai hana ka ba.

Ya kai musulmi, wasu marasa lafiyar sukan kasa yin alwala kuma sukan rasa waxanda za su taimaka su ga hakan, ko kuma tufafinsu da shimfixarsu su vaci da najasa, su kasa gusar da ita ko canjata, ko kuma wannan rahsin lafiyar ya zama shi ya janyo hakan. Sai lokutan sallah su wuce tufafinsa na cikin najasa, shimfixarsa na cikin najasa, gas hi ba zai iya tsarkake su ba, wannan zai yi sallah a halin da ya tsinci kansa a ciki, Allah kuma ya san halinsa da makomarsa.

Idan ciwo ko rauni yana fitar da ruwa ko mugunya, to sai ka yi sallar a haka. An karvo daga Miswar xan Makhramah, cewa shi ya shiga wajen Umar bn Khaxxab a daran da aka soke shi, sai ya tashi Umar domin sallar asubahi, sai Umar ya ce, “Na’am babu rabo cikin musulunci ga wanda ya bar sallah”. Sai ya yi sallah, alhalin mikinsa yana tsartar da jini). Imamu Maliku ne ya ruwaito shi.

Hakanan faxakkakun zukata suke, hakanan muminan zukata masu sakankancewa suke, wannan ciwon babba bai zama abu ne da zai hana su tuna sallah da kulawa da himmantuwa da ita ba.

Ya ku bayin Allah; ya wajaba ga musulmin da yake kula da mara lafiya a gidansa ko yake zaune da shi a asibiti ya tsoraci Allah, ya taimaki mara lafiyan wajen aiwatar da waxannan sallolin, ya tuna masa su idan lokutansu sun zo. Ya taimaka masa wajen yin su. Ya wajaba musulmi su taimaka wajan yin wannan farillar, musamman idan kana da iyaye biyu; uba da uwa, to ya wajaba ka ji tsoron Allah game da su, ka taimake su wajen yin wannan aiki na gari, da kiransu zuwa sallah, da sauqaqe wahalhalu gare su, da hidimta musu da abin da zai taimake su wajan ba da wannan farilla, domin Allah yana cewa,

( وَأْمُرْ أَهْلَكَ بِالصَّلَاةِ وَاصْطَبِرْ عَلَيْهَا ) [طه: 132]

(Kuma ka umarci iyalanka da sallah, kuma ka yi haquri a kanta).

Ya wajaba ga likitoci musulmi da waxanda ke lura da marasa lafiya a asibitoci su tsoraci Allah cikin lamarin marasa lafiya musulmi, su tuna musu lokacin sallah, su bayyana musu lokutanta, su himmatu da wannan lamari himmatu wa babba, su bayyana musu alamomin alqibla, su taimaka musu a bisa abin da zai sauqaqe musu lamarin sallarsu na alwala da taimama, domin wannan abu abin nema ne, kuma yana daga cikin taimakekeniya cikin biyayya da tsoron Allah. Allah kuwa yana cewa,

( وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ) [المائدة: 2]

(Kuma ku yi taimaki juna a kan biyayya da tsoron Allah, kuma kada ku yi ku taimaka wa juna a kan zunubi da ta’addanci).

Haqiqa likita ya kan iya damuwa da kula da lokacin shan magani, da wasu qaiyadaddun lokuta na safiya da yammaci, wannan abu ne mai kyau, sai dai kar mu yi sakaci da sallah, kada mumanta cewa ita tana daga mafi muhimmancin lamurra, mu kula da ita da sha’aninta, domin ita abincin ruhi ce, bai kamata a yi sakaci ko wasa da ita ba. Idan likita yana kulawa da lokacin shan magani, to ya wajaba a kula da mara lafiya game da waxannan salloli, mu tuna masa idan lokacinta ya yi, mu bayyana masa, mu taimaka masa, mu ba shi duk abin da zai taimaka masa yin wannan sallar, domin wannan lamari ne mai hummanci qwarai. Mara lafiya da ba zai iya alwala ba a kowane lokaci, ko yana samun wahala wajen saukowa don yin kowace sallah a lokacinta, to ya halatta ya haxa tsakanin Azahar da La’asar, da kuma tsakanin magariba da isha’i. Amma zai yi azahar raka’a huxune, la’asar ma huxu, magariba uku isha’i huxu. An halatta masa haxawa banda qasaru; domin a cikin wannan akwai tausasawa gare shi da sauqaqawa, idan cika tsarki da sauka don ba da kowace sallah ita kaxai ya yi masa wahala ya halatta ya haxa tsakaninsu saboda uzuri na shari’ah, Abin da dai ake buqata shi ne a kula da wannan farilla a himmatu da ita da tunata, da kiyaye ta, domin ita ce adireshin musulunci.

Ya kai musulmi, ka kula da wannan sallar, ka kiyaye ta, ka lazimceta, ka sani cewa babu rabuwa tsakaninka da ita har ka gamu da Allah kana mai kiyayeta, kana mai lazimtar ta, kana mai dauwamar aikata ta, domin ka zama daga masu gadan aljannar firdausi maxaukakiya. Allah yake cewa,

( وَالَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلَوَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ 9 أُولَئِكَ هُمُ الْوَارِثُونَ 10 الَّذِينَ يَرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ 11 ) [المؤمنون:9 - 11]

(Da kuma waxanda suke kiyaye sallar su, waxannan su ne masu gado. Waxanda suke gadon aljannar firdausi su masu dauwama ne a cikinta).

Kuma Allah maxaukaki yana cewa,

( فَإِنْ خِفْتُمْ فَرِجَالًا أَوْ رُكْبَانًا ) [البقرة: 239] .

(Idan kun ji tsoro, to (ku yi sallar) kuna tafe ko kuna haye).

Malamai suka ce, wannan dalili ne a kan cewa ga jiyawa game da rukunan sallah kan sarayar da su idan ya ji tsoron abokin gaba, ko yayi qoqarin riskar abokin gabar zai sallah ne a yanayin da yake ciki ko da da nunine, yana kallan alqibla ne ko baya kallonta. Ina roqon Allah ya sanyani ni da ku daga masu kiyayeta masu lura da ita, masu lazimtarta, lallai shi mai iko ne a bisa komai, Allah ya sanya ni da ku daga masu kiyayeta har ranar da zamu gamu da shi da falalarsa da karamcin sa.

Kuma ku sani – Allah ya jiqanku – cewa mafi kyawun zance shi ne littafin Allah,

kuma mafi alherin shiriya ita ce shiryar Muhammadu (ﷺ), kuma mafi sharrin lamurra fararrunsu kuma duk wata bidi’a vata ce. kuma ku lazimci jama’a domin hannun Allah na tare da jam’a. Ku yi salati – Allah ya jiqanku – a bisa Annabinku Muhammadu – don aiwatar da umarnin Ubangijinku wanda yake cewa,

( إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا 56 ) [الأحزاب: 56]

(Haqiqa Allah da mala’ikunsa suna salati ga Annabi ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati da taslimi a gare shi).

Allah ka yi salati da sallama da albarka a bisa shugaban na farko da na karshe Muhammadu xan Abdullahi, kuma ka yi yarda bisa halifofinsa shiryaiyu.