islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Amfanin Tsoron Allah A Rayuwar Musulmi


14962
Surantawa
Tsoron Allah (taqawa) shine wasiyyan da Allah yayi wa mutanen farko da na qarshe, kuma shine kiran annabawa, kuma tutar masoya Allah. Taqawa itace bawa ya sanya shinge tsakaninsa da abinda yake tsoro , don haka mai taqawa shine wanda ya sanya shinge da kariya da ayyuka na gargari tsakaninsa da azabar Allah, sai ka ganshi yana nesa da haramtattun alamura, sannan yana gaugawa wajen aikata ayyukan alheri; don haka sai yayi rayuwa amintatta gangariya a nan duniya, a can lahira kuma ya samu matsayi madaukaki .

Manufofin huxubar

Amfanin tsoron Allah da muhimmancinsa.

Haqiqanin ma’anar tsoron Allah.

Xaukakar masu tsoron Allah da abin da Allah ya yi musu tanadi.

Siffofin masu tsoron Allah.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka, ina yi muku wasiyya da ni kaina, a kan jin tsoron Allah. Domin tsoron Allah shi ne matattarar dukkanin alkhairi bakixaya. Babu wani alkhairi na kusa, ko na nesa, face tsoron Allah yana zaburarwa a kansa. Haka nan, babu wani sharri na kusa ko na nesa, a fili ko a voye, face tsoron Allah yana ba da katanga don kariya daga gare shi.

Kuma haqiqa tsoron Allah shi ne abu na farko da Allah ya yi wa mutanen farko da na qarshe wasiyya da shi. Allah Yana cewa:

( وَلَقَدْ وَصَّيْنَا الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ وَإِيَّاكُمْ أَنِ اتَّقُوا اللَّهَ ) [النساء: 131]

(Haqiqa Mun yi wasici ga waxanda a ka ba wa littafi a gabaninku da kuma ku, a kan ku ji tsoron Allah).

Taqawa dai, ita ce da’awar dukkanin annabawa da kuma salihan bayi. Ko wane Annabi yakan cewa, mutanensa :

( أَلَا تَتَّقُونَ ) [الشعراء: 106].

(Yanzu ba kwa ji tsoron Allah ba).

Kuma Waliyyan Allah su ne waxanda suka yi imani, kuma suka kasance masu tsoron Allah.

Asalin ma’anar kalmar taqawa, shi ne mutum ya sanya kariya da shamaki tsakaninsa da duk abin da yake tsoron sharrinsa. Allah Shi ne mafi cancantar a ji tsoronsa, tare da girmamawa.

Imam Ali (R.A), yana bayin ma’anar Tsoron Allah da cewa, (shi ne ka ji tsoron Mai girma (Allah), kuma ka yi aiki da Alqur’ani, kuma ka wadatu da kaxan, kuma ka yi tanadin ranar lahira».

Ya ku bayin Allah! Ya kamata mu san siffofin masu tsoron Allah, domin mu yi qoqari mu yi koyi da su. Kaxan daga cikin siffofin, sun haxar da:

Imani da abin da gaibi, da tsayar da sallah, da ciyarwa domin Allah, yarda da abin da Allah ya saukar, da sakankancewa da ranar lahira. Allah Yana cewa:

( ذَلِكَ الْكِتَابُ لَا رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِلْمُتَّقِينَ 2 الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنْفِقُونَ 3 وَالَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ وَبِالْآَخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ 4 أُولَئِكَ عَلَى هُدًى مِنْ رَبِّهِمْ وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ 5 ) [البقرة:2 - 5]

(Wannan Alqur’ani babu kokwanto a cikinsa, shiriya ne ga masu tsoron Allah. Waxanda suke imani da abin da ya voyu, kuma suke tsaida sallah, kuma suke ciyarwa daga abin da Allah ya azurta su da. Waxanda suke imani da abin da muka saukar maka, da abin da muka saukar gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira. To waxannan suna bisa shiriya daga Ubangijinsu, kuma waxannan su ne masu samun babban rabo).

Daga cikin siffarsu, akwai cika alqawari, da kuma haquri a kan abin da ya same su na bala’i a rayuwa. Allah Ta’ala yana cewa:

( لَيْسَ الْبِرَّ أَنْ تُوَلُّوا وُجُوهَكُمْ قِبَلَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَلَكِنَّ الْبِرَّ مَنْ آَمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآَخِرِ وَالْمَلَائِكَةِ وَالْكِتَابِ وَالنَّبِيِّينَ وَآَتَى الْمَالَ عَلَى حُبِّهِ ذَوِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ وَالسَّائِلِينَ وَفِي الرِّقَابِ وَأَقَامَ الصَّلَاةَ وَآَتَى الزَّكَاةَ وَالْمُوفُونَ بِعَهْدِهِمْ إِذَا عَاهَدُوا وَالصَّابِرِينَ فِي الْبَأْسَاءِ وَالضَّرَّاءِ وَحِينَ الْبَأْسِ أُولَئِكَ الَّذِينَ صَدَقُوا وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ 177 ) [البقرة: 177].

“Albirru shi ne wanda ya yi imani da Allah, da ranar lahira, da mala’iku, da littattafai da annabawa, kuma ya ba da dukiya ga makusanta, da marayu, da talakawa, da matafiyi, da masu roqo, da wajen fansar bayi. Kuma ya tsayar da sallah ya ba da zakka. Da masu cika alkawari idan su xauka, kuma da masu haquri lokacin yunwa da cuta da lokacin yaqi. Waxannan su ne waxanda suka yi gaskiya, kuma su ne masu tsoron Allah).

Yana daga siffarsu, yawaita istigfari game da zunubansu. Allah yana cewa:

( وَسَارِعُوا إِلَى مَغْفِرَةٍ مِنْ رَبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ133الَّذِينَ يُنْفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِين134وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ ذَكَرُوا اللَّهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ وَمَنْ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ وَلَمْ يُصِرُّوا عَلَى مَا فَعَلُوا وَهُمْ يَعْلَمُونَ 135 ) [آل عمران: 135]

)Kuma ku yi gaggawa zuwa neman gafara daga Ubangijinku, da wata aljannah wacce faxinta kamar faxin sama da qasa ne, an tande ta ga masu tsoron Allah. Waxanda suke ciyarwa a lokacin da daxi da lokacin wahala, kuma masu haxiye fushi, kuma masu afuwa ga mutane. Kuma Allah yana son masu kyautatawa. Su ne waxanda idan suka aikata wata alfahasha, ko suka zalinci kawunansu sai su ambaci Allah, kuma su nemi gafarar zubbansu, kuma wanene yake gafarta zunubi ba Allah ba. Ba sa doge wa a kan abin da suka aikata na laifi alhalin suna sane).

Tsoron Allah yana cikie da alfano ga bawa duniya da lahira. Kaxan daga cikin alfanonsa:

- Ubangiji zai sanya bawa mai tsoron Allah abin da zai banbance tsakanin qarya da gaskiya, Allah yana cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا إِنْ تَتَّقُوا اللَّهَ يَجْعَلْ لَكُمْ فُرْقَانًا وَيُكَفِّرْ عَنْكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ 29 ) [الأنفال: 29]

(Ya ku waxanda suka yi imani, in kun ji tsoron Allah, to zai sanya muku mafita ya kankare muku laifukanku, ya gafarta muku. Kuma lalle Allah ma’abocin falala ne mai girma).

- Yana da cikin alafanon tsoron Allah: Allah yana karvar aikin mai taqawa ne, kamar yadda ya ce,

( إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللَّهُ مِنَ الْمُتَّقِينَ ) [المائدة: 27]

(Kaxai Allah Yana karva ne daga masu jin tsoronsa).

- Daga cikin alfanon akwai samon karramawa ta Allah ta’ala, Allah yana cewa,

(Haqiqa mafi girman daraja da matsayi a cikinku shi ne mafi tsoron Allah daga cikinku).

- Yana daga cikin amafanin tsoron Allah, Ubangiji zai ba wa mai shi kaso biyu na rahamarsa, kuma ya sanya masa haske da zai riqa tafiya a cikinsa, kuma ya gafarta masa zunubbansa, kamar yadda Allah ya ce,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَآَمِنُوا بِرَسُولِهِ يُؤْتِكُمْ كِفْلَيْنِ مِنْ رَحْمَتِهِ وَيَجْعَلْ لَكُمْ نُورًا تَمْشُونَ بِهِ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ 28 ) [الحديد: 28]

(Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku yi imani da manzansa, zai ba ku kaso biyu daga cikin rahamarsa, ya sanya muku haske a cikin rayuwarku, ya gafarta muku, haqiqa Allah mai yawan gafara ne mai jinqai).

- Yana daga cikin amfanin taqawa ga bawa, shi ne za ta zama dalilin kuvutarsa yayin da bayi za su qetare wuta, Allah yana cewa,

( وَإِنْ مِنْكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا كَانَ عَلَى رَبِّكَ حَتْمًا مَقْضِيًّا 71 ثُمَّ نُنَجِّي الَّذِينَ اتَّقَوْا وَنَذَرُ الظَّالِمِينَ فِيهَا جِثِيًّا 72 ) [مريم: 72].

“Babu wani daga cikinku, face sai ya shige ta kanta. Wannan wani abu ne na dole da Ubangijinka ya hukunta shi. Sannan sai mu tseratar da masu tsoron Allah, kuma mu bar azzalimai a gurfane a cikinta”

Sannan Allah ya sake faxa:

( وَيُنَجِّي اللَّهُ الَّذِينَ اتَّقَوْا بِمَفَازَتِهِمْ لَا يَمَسُّهُمُ السُّوءُ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ 61 ) [الزمر: 61]

(Kuma Allah zai tseratar da waxanda suka ji tsoron Allah ta hanyar ba su babban rabonsu, babu wani mummunan abu da zai same su, kuma ba za su yi baqin ciki ba).

- Kuma yana daga cikin amfanin tsoron Allah, Ubangiji zai gadar musu da gidan Aljanna ranar qiyama, Allah ya ce,

( تِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي نُورِثُ مِنْ عِبَادِنَا مَنْ كَانَ تَقِيًّا 63 ) [مريم: 63]

(Wannan ita ce Aljannar da za mu gadawa wanda yake mai tsoron Allah daga bayinmu).

Daga cikin irin wannan amfanin, Allah yana tare da masu tsoron Allah da goyon bayansu, da ba su nasara, Allah yana cewa,

( إِنَّ اللَّهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَوْا وَالَّذِينَ هُمْ مُحْسِنُونَ 128 ) [النحل: 128]

(Allah yana tare da masu jin tsoronsa, kuma mau kyautatawa a cikin ayyukansu).

- Hakanan Allah yana buxewa masu tsoron Allah albarkatunsa daga sama da qasa, kamar yadda ya ce,

( وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى آَمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَرَكَاتٍ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ) [الأعراف: 96]

(Da a ce ma’abota alqaryu za su yi imani, da mun buxe musu taskokin albarkatunmu daga sama da qasa.”

- Sannan Allah yana sanya wa mai tsoron Allah mafita daga duk wani qunci da damuwa, kamar yadda ya ce,

( وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مَخْرَجًا 2 ) [الطلاق: 2].

(Duk wani wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa mafita).

Ya ku bayin Allah, ku yi guziri da tsoron Allah da ku rabauta a rayuwarku ta duniya da lahira, domin tsoron Allah shi ne mafi alfanon abin da bawa ya yi guziri da shi. Allah yana cewa,

( وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوَى وَاتَّقُونِ يَا أُولِي الْأَلْبَابِ 197 ) [البقرة: 197]

(Ku yi guzuri, haqiqa mafi amfanin guzuri shi ne tsoron Allah. Kuma ku ji tsorona yaku masu hankula).

Allah Ya qara da cewa:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَلْتَنْظُرْ نَفْسٌ مَا قَدَّمَتْ لِغَدٍ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ 18 وَلَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ نَسُوا اللَّهَ فَأَنْسَاهُمْ أَنْفُسَهُمْ أُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ 19 ) [الحشر: 19]

.

(Ya ku waxanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah, kuma kowace rai ta yi duba ga abin da ta gabatar domin gobe (Qiyama). Ku ji tsoron Allah, haqiqa Allah Masani ne game da duk abin da kuke aikatawa. Kada ku zama kamar waxanda suka manta da Allah, sai ya mantar da su kawunansu. Waxannan su ne fasiqai).

Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alqur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah ya tabbata ga Annabin rahama, Muhammadu bn Abdullahi da alayensa da sahabbansa, da waxanda suka bi tafarkinsa har zuwa qiyama.

Bayan haka,

Ku sani – Allah ya muku rahama – Wanda Allah ya azurta ta shi da taqawa, har ta mamye zuciyarsa, to babu shakka ya xanxani ni’ima ta sa’adar duniya kafin ta lahira. Kuma ya kasance mafi karamci a gurin Allah. An karvo daga Abu Hurairata, ya ce, na ce, Ya ma’aikin Allah(ﷺ), wanene ya fi karamci cikin mutane? Sai ya ce, "Wanda ya fi su tsoron Allah". Sai suka ce, Ba a kan haka muke maka tambaya ba. Sai ya ce, "Annabin Allah Yusuf, xan Annabin Allah, xan badaxayin Allah". Sai suka ce, Ba a kan haka muke maka tambaya ba. Sai ya ce, "Kuna tambaya ta ne game da labawan asali, to masu kirkinsu a jahiliyya, su ne masu kirkinsu a musulunci idan sun yi ilimi".

Ya bayin Allah! Ku sani tsoron Allah yana hana hannu tava riqe haram, yana hana qafa ta tafi gurin abin da zai fusata Allah. Yana hana harshe faxar duk wata magana da Allah zai yiwa mutum hisabi a kansa. Yana hana ido kallon haram. Tsoron Allah yana sanya mutum ya riqa tafiya a gwadaben rayuwa yana mai taka-tsantsan cikin duk abin da zai yi ko ya bari. Sayyidina Umar Alfaruq yana cewa Ubayyi bn Ka'ab: Menene taqawa? Sai ya ce, "Shin ka tava bin hanya mai qaya? Sai Umar ya ce, "Na'am". Sai Ubayyu ya ce, "To ya riqa yi?" Sai ya ce, "Na yi dage na kula? Sai Ubayyu ya ce, "To wannan shi ne tsoron Allah, ya dage, ya kuma yi taka-tsantsan kada ya jawo kansa hushin Allah ta'ala".

Tsoron Allah shi ne zai sanya mutane a kan tafarkin gaskiya koda yaushe, Allah Ta'ala yana cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا إِنْ تَتَّقُوا اللَّهَ يَجْعَلْ لَكُمْ فُرْقَانًا وَيُكَفِّرْ عَنْكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ 29 ) [الأنفال: 29]

(Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka ji tsoron Allah, zai sanya muku mafita, kuma ya kankare muku laifuffukanku, kuma ya gafarta muku. Allah ma’abocin falala ne mai girma).

Babu abin da yake riqe tsoron Allah, ya kafe shika-shikansa a zuciyar muminin sai yawan ambaton Allah a kowane lokaci, a kowane hali. Idan mumini ya gafala daga ambaton Allah wanda shi ne yake shayar da jijiyoyin taqawa to sai ta bushe, ganyayyakinta su zube, ta zama kamar bushasshen karmami rididdigagge, iskar waswasi tana sheqe shi, wadda shaixan ke tayar wa da xan-adam, hakanan zuciyarsa mai masa umarni da mummunan umarni. Don haka babu makawa a dawwama a kan zikirin Allah, da tasbihi tare da godiya ga Allah, don mutum ya samu ya murqushe waxannan abokan gabar tasa guda biyu (Shexan da son zuciya).

Muslim ya ruwaito hadisi daga Sauban, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin babu sujjada xaya da za ka yi don Allah, face Allah ya xaukaka darajarka da ita, ya kuma share maka laifi da ita".

Allah yana cewa,

( لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآَخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا 21 ) [الأحزاب: 21]

(Haqiqa kuna da abin koyi mai kyau game da Manzon Allah, ga wanda yake fatan haxuwa da Allah, da kuma ranar lahira, kuma ya ambci Allah dayawa).

Mumini shi ne wanda yake yin koyi da Manzon Allah, domin shi ne yake kyakkyawan fatan haxuwa da Allah, sannan ya yi imani da sakamakon lahira. Wannan kuwa ba zai samu ba sai da yawan tuna Allah, yawan tuna Allah shi ne zai yiwa bawa jagora zuwa ga samun mafi xaukakar masauki a gurin Allah. Sannan shi ma zikirin ba zai zama ya samu ba sai da koyi da Manzon Allah. To wannan koyin idan mumini ya lazimce shi, to shi ne zai zama daga cikin masu tsoron Allah.

Muna roqon Allah Ta’ala ya sanya mu cikin masu tsoronsa. Muna roqonsa ya azurta mu da taqawarsa, kuma ya sanya mu cikin bayinsa masu tsoronsa, kuma ya saukar da mu a masaukansu wanda ya yi musu alkawari da faxarsa:

( إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَهَرٍ 54 فِي مَقْعَدِ صِدْقٍ عِنْدَ مَلِيكٍ مُقْتَدِرٍ 55 ) [القمر: 55]

(Lalle masu tsoron Allah suna cikin aljannatai da qoramu, cikin mazauni na gaskiya, a gurin sarki mai cikakken iko).