islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Rayuwa bayan mutuwa


14849
Surantawa
Da yawa daga cikin mutane suna zaton idan sun mutu aka binne su shi ke nan rayuwa ta qare daga nan. Wannan fahimta an gina ta a kan kuskure babba kuma mummuna. Mutum bayan ya mutu ...

Manufofin huxubar

Abin da zai kasance bayan mutuwa na al’amuran ranar alqiyama.

Zaburarwa a kan kyawawan ayyuka da tsoratarwa ga barin munanan ayyuka.

Kira i zuwa gaggauta tuba kafin lokaci ya qurewa xan adam.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka: Ya ku bayin Allah!

Da yawa daga cikin mutane suna zaton idan sun mutu aka binne su shi ke nan rayuwa ta qare daga nan. Wannan fahimta an gina ta a kan kuskure babba kuma mummuna. Mutum bayan ya mutu yana shiga wata sabuwar rayuwa. Akwai rayuwa ta zaman qabari, da rayuwa ta bayan hisabi. Za mu xan yi tsokaci a cikin littafin Allah da Hadisai ingantattu a kan wannan al’amari. Tare da fito da al’amarin a fili na abin da zai kasance bayan mutuwa.

Idan mutum ya mutu, an binne shi, farkon rayuwar da zai fara fuskanta shi ne fitinar qabari.

Hadisi ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim daga Anas xan Malik, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan baya ya mutu an sa shi a cikin qabarinsa yana jin motsin takalman waxanda suka kawo shi. Sai mala’iku biyu su zo masa. Sai su zaunar da shi, su ce masa, "Me za ka ce dangane da wannan mutum? To mumini sai ya ce, "Na shaida haqiqa shi bawan Allah ne, kuma manzonsa ne". Sai a ce da shi kalli mazauninka na wuta, amma yanzu Allah ya sauya maka shi da gida a aljanna". Sannan duk zai gansu a lokaci xaya.

Qatada ya ce, Manzon Allah ya ce: "Za a buxe masa qabarinsa tsawon zira’i saba’in za a ce da kafiri, ko munafiqi, "Me za ka ce dangane da wannan mutum?" Sai ya ce, "Kawai ni ma ina faxar abin da na ji mutane suna faxa". Za a ce masa, "Ba ka sani ba, kuma ba ka karanta ba. Sai a doke shi da wata guduma ta qarfe, zai yi wata qara mai qarfi duk wanda yake wajen zai ji ta, in ban da mutum da aljan".

An karvo daga Abu Ayyub ya ce, "Wata rana manzon Allah ya fito bayan rana ta faxi, sai ya ji wata murya, sai ya ce: "Yahudawa ne ake gana musu azaba a qabari". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Shi ya sa a kowanne lokaci Manzon Allah (ﷺ) ya yi salla sai ya nemi tsari daga azabar qabari. Kuma ya umarci al'ummarsa da yin hakan.

Sannan bayan haka, sai a shiga yiwa kafiri da munafiki azaba. Shi kuma mumini a sa shi cikin ni'ima. Don haka bawa wace irin amsa ka tanadarwa wannan rana. Domin kuma rana ce da babu makawa sai ta zo.

Bayan haka kuma sai Allah ya tayar da duk waxanda suka mutu daga qaburburansu. Shi ya sa Allah Yake cewa:

أَوَلَمْ يَرَ الْإِنْسَانُ أَنَّا خَلَقْنَاهُ مِنْ نُطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُبِين77وَضَرَبَ لَنَا مَثَلًا وَنَسِيَ خَلْقَهُ قَالَ مَنْ يُحْيِي الْعِظَامَ وَهِيَ رَمِيمٌ78قُلْ يُحْيِيهَا الَّذِي أَنْشَأَهَا أَوَّلَ مَرَّةٍ وَهُوَ بِكُلِّ خَلْقٍ علىِ79) [يس: ٧٧ – ٧٩].

)Shin mutum baya gani ne mun halicce shi daga xugon miniyyi amma sai ga shi ya zama mai bayyana husuma. Mutum ya buga mana misali ya manta halittarsa, ya ce, «Wane ne zai raya qasusuwa alhalin sun ritittike?». Ka ce, «Wanda ya qagi halittarsu a farko shi ne zai raya su. Kuma shi masani ne ga dukkan halitta).

Sannan daga nan sai Allah ya tara halittu duka don yin hisaba, kamar yadda ya ce:

(وَلَقَدْ جِئْتُمُونَا فُرَادَى كَمَا خَلَقْنَاكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَتَرَكْتُمْ مَا خَوَّلْنَاكُمْ وَرَاءَ ظُهُورِكُمْ وَمَا نَرَى مَعَكُمْ شُفَعَاءَكُمُ الَّذِينَ زَعَمْتُمْ أَنَّهُمْ فِيكُمْ شُرَكَاءُ لَقَدْ تَقَطَّعَ بَيْنَكُمْ وَضَلَّ عَنْكُمْ مَا كُنْتُمْ تَزْعُمُونَ94) [الأنعام: 94]

Haqiqa kun dawo mana kuna xaixaikunku, kamar yadda muka halicce ku a farko karo. Kuma kun bar duk abin da muka hore muku a can bayanku Kuma duk waxanda kuke riyawa cewa za su cece ku ba mu gan su ba tare da ku. Babu wata alaqa da ta rage a tsakaninku. Abin da kuke riyawa shi ne mai cetonku ya vace muku ba kwa ganinsa).

Sannan Allah zai ta shi kafirai akan fuskokinsu. Duk sun makance, su zama kurame kuma bebaye. Allah ya ce:

(وَنَحْشُرُهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَى وُجُوهِهِمْ عُمْيًا وَبُكْمًا وَصُمًّا مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ كُلَّمَا خَبَتْ زِدْنَاهُمْ سَعِيرًا97) [الإسراء: 97]

Ma’ana: (Za mu tattara su a ranar qiyama a kan fuskokinsu suna makafi, kuma bebaye, kuma kurame. Makomarsu jahannama ce, duk sa’adda ta mutu sai mu qara rura musu ita).

A wannan lokaci ne mai cike da ban tsoro za ka ga kafirai da munafukai suna masu qanqan da kai, idanuwansu sun zazzaro, babu wani mai magana sai fa wanda Allah ya ba shi dama. Zukatansu sun zama fanko. Allah yana cewa:

(وَلَا تَحْسَبَنَّ اللَّهَ غَافِلًا عَمَّا يَعْمَلُ الظَّالِمُونَ إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمْ لِيَوْمٍ تَشْخَصُ فِيهِ الْأَبْصَارُ42 مُهْطِعِينَ مُقْنِعِي رُءُوسِهِمْ لَا يَرْتَدُّ إِلَيْهِمْ طَرْفُهُمْ وَأَفْئِدَتُهُمْ هَوَاءٌ43) [إبراهيم: ٤٢ – ٤٣].

(Kada ka yi tammanin cewa, Allah ya gafala da abin da azzalumai suke aikatawa. Kawai yana musu jinkiri ne domin wata rana da idanuwa za su zazzaro. Suna masu gaggawa, suna xaga kawunansu. Idanuwansu ba sa qiftawa. Kuma zukatansu duk sun zama iska).

Hakanan yana cewa:

(يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا لَا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَنُ وَقَالَ صَوَابًا38) [النبأ: 38]

(Ranar da Mala’ika Jibrila zai tsaya, tare da mala’iku sahu-sahu. Ba sa iya magana sai wanda Allah Mai rahama ya yi masa izini, kuma ya faxi maganar da take daidai).

Zukata a rannan za su zo maqoshi, suna cike da tashin hankali. Azzalumai a wannan rana ba su da wani mai cetonsu, ko wani abokin arzuki da za a saurare shi. Tsawon wannan rana ya kai tsawon shekara hamsin na lissafin duniya.

An karvo daga Abi Hurairata ya ce, manzon Allah ya ce: “Mutane za su yi gumi ranar alqiyama wasu har yakan kai tsawon zira’i saba’in a qasa, wasu kuma gumin ya yi mus linzami har zuwa kunnuwansu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Yaku bayin Allah!

Daga wannan lokaci kuma sai a taho da ba yi zuwa ga Allah, babu wani abu da zai xoye wa masa. Allah yana cewa:

يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ6) [الزلزلة: 6]) (A wannan yini ne mutane za su fito daban-daban, don a nuna musu ayyukansu).

Sai kuma a fara hisabi, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: "Za a zo da kafiri ranar qiyama a ce masa inda kana da kwatankwacin duniyar nan na zinari za ka iya ba da shi ka fanshi kawunanka? Sai ya ce, "Na’am". Sai Allah ya ce, "An tambaye ka abin da bai kai haka ba ba ka bayar ba".

A wata riwayar: "Na neme ka da abin da ya fi wannan sauqi a lokacin da kake cikin tsatson Adam, cewa, kada ka haxa komai da ni, amma ka qi sai da ka yi shirka". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Ya zo a hadisi cewa: "Babu wani daga cikinku face Allah ya yi masa magana shi da shi, ba tare da tafinta ba. Mutum zai kalli damansa ba abin da zai gani sai abin da ya aikta. Haka zai sake kallon hagunsa ba zai ga komai ba sai abin da ya aikata. Sannan ya kalli gabansa ba abin da zai gani sai wuta tana ci. Don haka ku ji tsoron shiga wuta ko da da tsagin dabino ne, ko kuma da kyakkyawar kalma". Bukhari da Ibn Majah ne suka rawaito.

Sanan daga nan ne sai a ba za takardun ayyuka, Allah yana cewa:

(وَوُضِعَ الْكِتَابُ فَتَرَى الْمُجْرِمِينَ مُشْفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَا وَيْلَتَنَا مَالِ هَذَا الْكِتَابِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةً وَلَا كَبِيرَةً إِلَّا أَحْصَاهَا وَوَجَدُوا مَا عَمِلُوا حَاضِرًا وَلَا يَظْلِمُ رَبُّكَ أَحَدًا49) [الكهف: 49]

.

Ma’ana: (Kuma za a aje littafi, a wannan lokaci za ka ga masu laifi a tsorace saboda halin da suke ciki. Kuma suna cewa, “Ya kaiconmu, wanene irin littafi ne wannan? Ba ya barin qaramin laifi da babba sai ya lissafa su. Kuma suka samu abin da suka aikata a halarce. Kuma Ubangijin ba zai zalunci wani ba).

To fa a nan ne mutane za su kasu kashi biyu, wasu za su karvi littafinsu da dama, wasu za su karva da hagu.

(فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ فَيَقُولُ هَاؤُمُ اقْرَءُوا كِتَابِيَه21إِنِّي ظَنَنْتُ أَنِّي مُلَاقٍ حِسَابِيَهْ 20فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَاضِيَةٍ 21فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ22قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ23 كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الْأَيَّامِ الْخَالِيَةِ24وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِشِمَالِهِ فَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُوتَ كِتَابِيَهْ25 وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيَهْ26يَا ýلَيْتَهَا كَانَتِ الْقَاضِيَةَ27مَا أَغْنَى عَنِّي مَالِيَهْ28 هَلَكَ عَنِّي سُلْطَانِيَهْ29) [الحاقة: ١٩ - ٢٩].

(Duk wanda aka ba shi littafinsa da hannun damarsa zai ce, ku karvi littafina ku karanta. Ni da na tabbatar da cewa, zan gamu da hisabina. To shi yana cikin rayuwa yardadda. Yana cikin aljannah maxaukakiya. ‘ya’yan itatuwanta dab-da-dab suke. Ku ci ku sha kuna masu jin daxi saboda abin da kuka aikata a kwanakinku da suka shuxe. Amma kuma wanda aka ba shi littafinsa a hannunsa na hagu, sai ya ce, ya kaico na ina ma ba a ba ni littafi na ba. Kuma ban san menene hisabi na ba. Ina ma mutuwa ta gama da ni. Dukiyata ba ta wadatar da ni komai ba. Ikona ya vace mini).

Sannan Allah Zai yi umarni a sanya mizani domin auna ayyukan bayi.

Allah yana cewa:

(وَنَضَعُ الْمَوَازِينَ الْقِسْطَ لِيَوْمِ الْقِيَامَةِ فَلَا تُظْلَمُ نَفْسٌ47) [الأنبياء: ٤٧].

Ma’ana: (Kuma za mu san ya ma’aunai na adalci domin ranar qiyama, to ba za a zalucni wata rai wani abu ba).

Sannan bayan haka kowa zai zo ya wuce ta kan siraxi kamar yadda ya zo a hadisi, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Za a zo da wata gada a sanyata a kan doron jahannama. Sai muka ce, "Ya Manzon Allah Wacce iri gada kuma?' Sai ya ce: " Gada ce mai tsansti da zamiya. Da qugiyoyi akanta da qayar tsidahu masu faxi. Irin waxanda ake samunsu a Najdu. Larabawa suna ce musu: Sa'adan. Mumini zai wuce ta kan wannan siraxi kamar walqiya, wani kuma kamar iska, wani kuma kamar ingarman doki. Wani ya tsira ya kuvuta. Wani kuma ya kukkuje a wuta. Har na qarshesu ya zo ya wuce da jan ciki. Bukhari ne ya ruwaito. Abu Sa’id ya ce: “Wannan gadar ta fi gashi sirantaka, kuma ta fi takobi kaifi.

Bayan an gama bi ta kan siraxi, za a zo a yi qisasi da hisabi a tsakannin bayi. Farkon abin da Allah zai fara qasasi akansa shi ne jinannaki.

Allah zai keve muminai a kan wata gada tsakanin wuta da aljanna, sai Allah Ya yi qisasi a tsakaninsu, a bisa abin da suka zalunci kawunansu a gidan duniya. Idan Allah Ya tsarkakar da su, sannan sai a sa su a aljanna.

An karvo da ga Abu Sa'id Al-Khudri ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Muminai za su kuvuta daga shiga wuta. Sai a zo a dakatar da su a kan wata gada tsakanin aljannah da wuta. A yi musu qisasi; abin da sashinsu ya zalinci sashi da shi a duniya. Har sai an tace su, kuma a tsarkake su, sai a yi musu izinin shiga aljannah". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Yaku Musulmi!

Duk waxannan fa al’amura tabbatattu ne, kuma tabbas za su faru. Babu wani shakku. Ko tababa, a kan faruwarsu, babu abin da ya rage illa mu tashi mu farka daga wannan dogon baccin da muke ciki.

Ya zama dole a kan duk wanda Allah Ya ara masa wani vangare na mulkinsa da ya ji tsoron Allah kar ya yi zalunci. Kar ya kasance marar damuwa da halin da waxanda yake shuganci suke ciki. Suna kwana da yunwa, kai kuwa kana qoshi. Kar bar su suna zama abin farautar miyagun mutane. Ya za ka fuskanci wannan rana idan ka jewa Ubangiji da irin wannan hali? Ka tuna faxar Manzon Allah (ﷺ) da yake cewa:

"Babu wani mai kiwo da Allah zai ba shi kiwo ya je masa yana mai cin amana, face ya shiga wuta".

Ya ku waxanda Allah ya ba su shugabanci, gwamnoninku da ‘yan majalisinku da ciyamominku, ku ji tsoron Allah a kan amanar da Ya ba ku. Kowa ya duba ya ga me ya tanadar domin waccan rana. Ranar hisabi, ranar tonon asiri, ranar da-na-sani.

Haka kuma su waxanda ake shugabanta kowa ya daina varna da sakaci a wajen aiwatar da umarnin Allah, a dinga yin salla a kan lokaci. Ku daina qarya da sata da zamba da qeta da ha’inci. Kowa ya ribaci lokacinsa da quruciyarsa da lafiyarda domin Ubangiji yana nan a madakata.

Dukkan Yabo da kirari sun tabbata ga Allah Ubangijin Halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban manzanni, kuma fiyayyen haltta, annabin tsira, annabin rahma, Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa da duk waxanda suka bi tafarkin addininsu da koyarwarsa har zuwa ranar alqiyama. Bayan haka:

Yaku bayin Allah!

Allah Yana cewa:

(وَكَذَلِكَ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ قُرْآَنًا عَرَبِيًّا لِتُنْذِرَ أُمَّ الْقُرَى وَمَنْ حَوْلَهَا وَتُنْذِرَ يَوْمَ الْجَمْعِ لَا رَيْبَ فِيهِ فَرِيقٌ فِي الْجَنَّةِ وَفَرِيقٌ فِي السَّعِير7)ِ [الشورى: 7]

(Hakanan mun yi maka wahayin wannan Alqur’ani da harshen Larabci, domin ka gargaxi mutanen Makkah da kewayenta. Ka gargaxesu da ranar tattara halittu, babu kowanto game da wannan rana. Wasu za su kasance a aljannah, wasu kuma a cikin wutar Sa’ira).

Allah ya ce a cikin Suratul Hudu:

(إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآَيَةً لِمَنْ خَافَ عَذَابَ الْآَخِرَةِ ذَلِكَ يَوْمٌ مَجْمُوعٌ لَهُ النَّاسُ وَذَلِكَ يَوْمٌ مَشْهُودٌ 103 وَمَا نُؤَخِّرُهُ إِلَّا لِأَجَلٍ مَعْدُودٍ104 يَوْمَ يَأْتِ لَا تَكَلَّمُ نَفْسٌ إِلَّا بِإِذْنِهِ فَمِنْهُمْ شَقِيٌّ وَسَعِيدٌ105 فَأَمَّا الَّذِينَ شَقُوا فَفِي النَّارِ لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَشَهِيقٌ106 خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ السَّمَوَاتُ وَالْأَرْضُ إِلَّا مَا شَاءَ رَبُّكَ إِنَّ رَبَّكَ فَعَّالٌ لِمَا يُرِيدُ107) [هود: ١٠٣ - ١٠٧].

“Haqiqa a cikin wannan akwai aya ga duk wanda yake tsoron ranar lahira. Wannan yini ne da Allah yake tara mutane cikinsa Kuma yini ne da ake halartarsa. Ba ma jinkirta shi sai don wani ajali qididdigagge. Ranar da za ta zo, babu wata rai da za ta yi magana sai da izininsa. Daga cikinsu akwai xan wuta, akwai xan aljanna. Bayi na qwarai suna cikin aljanna suna masu dawwama a cikinta, dawwamar sama da qasa, wannan kyauta ce ba mai yankewa ba. Waxanda kuma suka yi aikin tsiya to suna cikin wuta masu dawwama ne a cikinta dauwamar sama da qasa. Lalle Ubangijinka mai aikata abin da ya ga dama ne).

Kuma Allah yana cewa:

(وَسِيقَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِلَى جَهَنَّمَ زُمَرًا حَتَّى إِذَا جَاءُوهَا فُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا أَلَمْ يَأْتِكُمْ رُسُلٌ مِنْكُمْ يَتْلُونَ عَلَيْكُمْ آَيَاتِ رَبِّكُمْ وَيُنْذِرُونَكُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَذَا قَالُوا بَلَى وَلَكِنْ حَقَّتْ كَلِمَةُ الْعَذَابِ عَلَى الْكَافِرِينَ71 قِيلَ ادْخُلُوا أَبْوَابَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا فَبِئْسَ مَثْوَى الْمُتَكَبِّرِينَ72 وَسِيقَ الَّذِينَ اتَّقَوْا رَبَّهُمْ إِلَى الْجَنَّةِ زُمَرًا حَتَّى إِذَا جَاءُوهَا وَفُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا سَلَامٌ عَلَيْكُمْ طِبْتُمْ فَادْخُلُوهَا خَالِدِينَ73) [الزمر: ٧١ – ٧٣].

Haka Allah zai kora ‘yan wuta zuwa jahannama jama’a-jama’a. Har sai zo mata sai a boxe qofofinta, kuma masu gadinta su ce musa: “Shin manzanni daga cikinku ba su zo muku suna karanta muku ayoyin Ubangijinku ba, kuma suna gargaxinku haxuwarku da wannan yinin ba?”Sai suka ce, E, sun zo. Sai dai kalmar azaba ta riga ta tabbata akan kafirai. Sai a ce musu ku shiga qofofin jahannama, kuna masu dauwama a cikinsu har abada. Tir da makomar masu girman kai. Kuma a ka ja waxanda suka ji tsoron Ubangijinsu jama’a-jama’a zuwa aljannah. Har sai idan sun zo mata alhalin an buxe qofofinta. Sai kuma masu gadinta su ce musu, “Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji daxi. Ku shiga aljannah kuna masu dauwama a cikinta har abada”).

Yaku bayin Allah!

Ku ji tsoron Allah. Ku sani mafi darajarmu a wajen Allah shi ne mafi tsoronsa. Duk wanda aikinsa ya daqilar da shi, to dangantakarsa ba za ta ciyar da shi gaba ba. Ku sani Allah yana lissafa muku ayyukanku da kuke yi, don haka duk wanda ya samu alheri to ya godewa Allah. Wanda kuma ya sami kishiyar wannan to kar ya zargi kowa sai kansa.