islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Wasu Daga Cikin Ayoyin Halittun Allah


14937
Surantawa
Lallai tunani da izina game da ayoyin Allah a wannan duniya yana gadarwa dan adam imani da qudurar Allah da kadaituwarsa a duniyar nan. Kuma haqiqa Allah madaukakin sarki ya kwadaitar da mu game da hakan a littafinsa, don haka ya umarce mu da duba zuwa ga halittun sammai da qassai da duwatsu da sauran ayoyinsa, domin bayi su san cewa fa lallai wannan duniya tana da mahalicci me sarrafa ta, wanda shi kadai ya cancanci kadaitawa da ibada.

Manufofin huxubar

Tunatar da mutane wasu daga cikin ayoyin halittun Allah.

Bayanin girman Allah Ta’ala, kuma da cewa shi ne wanda ya cancanci bauta shi kaxai.

Kiran Mutane da su godewa Allah ta’ala da ya hore musu waxannan manya-manyan halittu.

Kiran mutane a kan su yi amfani da waxannan halittu wajen bautawa Allah

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ‘yan uwa! Lallai cikin halittun Allah baki xaya, akwai aya da take tabbatar da cewa, Allah shi kaxai ne, kuma shi ya cancanta a bautawa shi kaxai. Allah yana cewa,

( أَوَلَمْ يَنْظُرُوا فِي مَلَكُوتِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا خَلَقَ اللَّهُ مِنْ شَيْءٍ وَأَنْ عَسَى أَنْ يَكُونَ قَدِ اقْتَرَبَ أَجَلُهُمْ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ 185 ) [الأعراف: 185]

(Shin ba su yi duba ba cikin masarautar sama da qasa, da ma duk wani abin da Allah ya halitta. Kuma tabbas ajalinsu ya qarato. To da wane zance ne bayansa suke bayar da gaskiya?) .

Kuma Allah ya ce,

أَفَلَمْ يَنْظُرُوا إِلَى السَّمَاءِ فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَاهَا وَزَيَّنَّاهَا وَمَا لَهَا مِنْ فُرُوجٍ6وَالْأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنْبَتْنَا فِيهَا مِنْ كُلِّ زَوْجٍ بَهِيجٍ 7 تَبْصِرَةً وَذِكْرَى لِكُلِّ عَبْدٍ مُنِيبٍ 8 ) [ق: 6 -8]

(Shin ba su yi duba ba zuwa sama da take kansu, yaya muka gina ta, kuma muka qawata ta, babu wata varaka, ko kecewa tare da ita. Qasa kuma muka miqar da ita, kuma muka jefa duwatsu a cikinta, muka tsirar daga kowane irin nau’in kayan marmari mai qayatarwa. Faxakarwa ce da tunatarwa ga duk wani bawa mai komawa ga Allah).

Kuma Allah ya ce,

( أَفَلَا يَنْظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ 17 وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ 18 وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ 19 وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ 20 ) [الغاشية:17 - 20]

(Shin ba sa yin nazari kan raquma, yaya aka halicce su? Haka nan sama, yaya aka xaga ta? Haka nan qasa, yaya aka shimfixa ta?).

Lallai yana daga cikin ayoyin Allah, halittar sama da qasa. Duk wanda ya yi nazari kan halittar sama, da kyawunta da xaukakarta, da qarfinta, zai gane ikon Allah da cancantarsa da a bauta masa shi kaxai. Halitta da take nuna iyawa da qwarewa; halitta da babu makusa a tare da ita. Allah yana cewa,

( فَارْجِعِ الْبَصَرَ هَلْ تَرَى مِنْ فُطُورٍ 3 ثُمَّ ارْجِعِ الْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنْقَلِبْ إِلَيْكَ الْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ حَسِيرٌ 4 ) [الملك: 3 - 4]

(Ka mayar da gani zuwa sama. Shin ka ga wata kecewa tare da ita? Sannan ka sake mayar da gani karo na biyu, ganinka zai dawo gare ka, yana tavavve, alhali ya gaji).

Haka idan mutum ya yi nazari kan halittar qasa, yadda Allah ya shimfixa ta, kuma ya keta hanyoyi a cikinta, ya kuma kafa duwatsu a kanta, ya kuma albarkace ta da abubuwa irin daban-daban na buqatun halitta, kuma ya hore ta ga xan Adam yana kai-kawo a kanta daga nan zuwa can ba tare da tangarxa ba. Kuma a cikinta xan Adam yake samun abincinsa, da abin sha. Duk wannan yana nuna ikon Allah da cancantarsa a bauta masa shi kaxai. Allah yana cewa,

( وَفِي الْأَرْضِ آَيَاتٌ لِلْمُوقِنِينَ 20 ) [الذاريات: 20]

)A cikin qasa akwai ayoyi daban-daban ga masu sakankancewa da samuwar Allah).

Hakanan yana daga cikin ayoyinsa, abin da ya watsa a sama da qasa na halittu iri daban-daban: Sama akwai mala’iku, wanda ba mai iya qididdige su, sai Allah. Allah yana cewa,

( وَمَا يَعْلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ ) [المدثر: 31]

(Babu wanda ya san yawan rundunar Ubangijinka, sai shi).

A qasa kuwa, akwai halittu dangi daban-daban, sun sava da juna ta fuskar halittarsu. Daga cikinsu akwai waxanda suke masu amfani ga xan Adam, wanda ta hanyarsu yake qara sanin cikar ni’imar Allah a kan bayi. Daga cikinsu akwai masu cutarwa ga xan Adam, wanda ta hanyarsa xan Adam yake qara gane matsayinsa da kuma rauninsa a gaban sauran halittun Allah. Kuma dukkaninsu suna tsarkake Allah, tare da gode masa, kamar yadda ya ce,

( تُسَبِّحُ لَهُ السَّمَوَاتُ السَّبْعُ وَالْأَرْضُ وَمَنْ فِيهِنَّ وَإِنْ مِنْ شَيْءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَكِنْ لَا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ إِنَّهُ كَانَ حَلِيمًا غَفُورًا 44 ) [الإسراء: 44]

(Sama guda bakwai, da qasa, da abin da yake cikinsu, suna tsarkake Ubangiji. Kai babu wani abu, face sai yana tsarkake shi. Lallai shi ya kasance mai haquri ne, mai gafara).

Kuma duk wannan halittu, Allah yake arzuta su shi kaxai. Kamar yadda Allah ya ce,

( وَمَا مِنْ دَابَّةٍ فِي الْأَرْضِ إِلَّا عَلَى اللَّهِ رِزْقُهَا ) [هود: 6].

(Babu wata dabba da take rarrafawa a qasa, face Allah ne yake arzuta ta).

Yana daga cikin ayoyinsa, dare da rana. Allah ya sanya dare, don nutsuwa ga bayi: Su kwanta a cikinsa, su yi barci, su sami hutu. Ya kuma sanya rana, gudanar da harkokin rayuwa, da neman arziki. Kamar yadda Allah ya ce,

( قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ جَعَلَ اللَّهُ عَلَيْكُمُ اللَّيْلَ سَرْمَدًا إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَنْ إِلَهٌ غَيْرُ اللَّهِ يَأْتِيكُمْ بِضِيَاءٍ أَفَلَا تَسْمَعُونَ 71 قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ جَعَلَ اللَّهُ عَلَيْكُمُ النَّهَارَ سَرْمَدًا إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَنْ إِلَهٌ غَيْرُ اللَّهِ يَأْتِيكُمْ بِلَيْلٍ تَسْكُنُونَ فِيهِ أَفَلَا تُبْصِرُونَ 72 ) [القصص: 71 - 72]

(Ka ce, “Ku ba ni labari, idan Allah ya sanya dare dindindin, har zuwa ranar tashin qiyama, wane Ubangiji ne ba Allah ba, zai zo muku da haske. Ba kwa jin abin da ake gaya muku?” Ka ce, “Ku ba ni labari, idan Allah ya sanya rana dindindin, har zuwa ranar tashin qiyama, wane Ubangiji ne ba Allah ba, zai zo muku da dare, wanda za ku nutsu a cikinsa? Ba kwa ganin abin da ake gaya muku?).

Ya ku ‘yan uwa! Lallai wannan sararin duniya gabaxayansa, da abin da yake cikinsa, halitta ce ta Ubangiji, ba wanda ya halicce ta, sai shi, kamar yadda Allah ya ce,

( أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ 35 أَمْ خَلَقُوا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بَل لَا يُوقِنُونَ 36 ) [الطور:35 - 36]

)Shin an halicce su ne daga babu, ko kuma su suka yi halitta? Ko kuma sun halicci sama da qasa ne? Bari dai, ba sa sakankancewa ne).

Duniya ba ta halicci kanta ba, kuma ba zai yiwu a ce haka kawai ta samu ba, ba tare da wani abu ya halicce ta ba. Wanda ya halicce ta, shi ne Allah, kuma shi yake tsaye da lamarinta, babu wanda ya halicce ta, sai shi, ba kuma wani Ubangiji, sai shi. Albarkacin Allah sun ya waita, shi ne wanda ya fi kowa iya qaddarawa».

Da fatan Allah ya albarkace ni da ku bakixaya da abin da muka ji na ayoyin qur’ani mai hikima, da wa’azi mai amfani. Lalle shi Allah mai ji ne mai gani.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayye halitta, kuma fiyayyen annabawa, Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsa har zuwa ranar qiyama.

Bayan haka, ya ku ‘yan uwa! Ya zama wajibi mu gode wa Allah, bisa waxannan halittu da ya yi, kuma ya hore su gare mu. Allah ya da sanar da mu abin da ba mu sani ba, ya koya mana abin da zai inganta addininmu da rayuwarmu. Yana daga cikin abin da Allah ya sanar da mu, mafarar halittar wannan duniyar, abin da ba za a iya sanin sa ba, sai ta hanyar Manzanni. Duk wani wanda zai yi magana kan yadda aka halicci sama da qasa, to dole ne mu gwada maganarsa da abin da Manzanni suka zo da shi. Idan sun yi daidai, sai mu karva, idan kuwa suka sava wa juna, to ba za a karvi maganarsa ba.

Hakanan yana daga cikin abin da Allah ya sanar da mu, ya halicci sama da qasa, da abin da yake tsakaninsu: Ya halicci sama a cikin kwana biyu, ya kuma kafa duwatsu a kanta, ya tanadar da albarkatu, wanda bayi za su amfana da su, cikin wasu kwanaki biyu daban. Idan aka haxa wannan, kwana huxu kenan. Sannan ya nufi sama, alhali tana hayaqi, sai ya daidaita ta, ta zama sama, sammai bakwai, cikin kwanaki biyu, ya yi wahayi cikin kowace sama, da abin da ya kevance ta. Gabaxaya kwana shida kenan, da Allah ya halicci sama da qasa a cikinsu, kuma ya ajiye abubuwa da xan Adam yake buqata a cikinsu: Ya samar da ruwa, ya samar da abinci iri daban-daban, waxanda za su tabbatar da xorewar xan Adam a doron qasa, kuma ya kimsa wa xan Adam yadda zai yi hulxa da danginsa, da ma sauran halittun Allah. Duk Allah ya yi wannan, ba don komai ba, sai don a bauta masa shi kaxai, kamar yadda Allah yake cewa,

( وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ 56 ) [الذاريات: 56]

(Ban halicci aljanu da xan Adam ba, sai don su bauta mini).

Don haka, ya zama tilas a kan kowane mutum, ya bauta wa Allah shi kaxai, kamar yadda Allah ya yi umarni, don godiya ga Allah, bisa waxannan manya-manyan baiwaiwaki da Allah ya yi mana. Kamar yadda Allah ya ce,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُلُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ وَاشْكُرُوا لِلَّهِ إِنْ كُنْتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ 172 ) [البقرة: 172]

(Ya ku waxanda suka yi imani! Ku ci daga abubuwa masu tsarki, da muka arzuta ku da su, kuma ku gode wa Allah, idan kun kasance shi kaxai kuke bautawa).

Kuma Allah yana cewa,

( فَابْتَغُوا عِنْدَ اللَّهِ الرِّزْقَ وَاعْبُدُوهُ وَاشْكُرُوا لَهُ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ 17 ) [العنكبوت: 17]

(Ku nemi arziki a wajen Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa. Zuwa gare shi ne za ku koma).

Ya Ubangiji! Muna gode maka a kan waxannan kyaututtuka masu girma, kuma muna gode maka a kan aiko mana Manzanni da ka yi. Godiya ta tabbata ga Allah, wanda ya shiryar da mu ga wannan addini, ba mu zamo masu shiriya ba, ba don Allah ya shiryar da mu ba.