islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Kafafen yada labarai da tasirinsu a cikin rayuwar mutane


7876
Surantawa
Kafafen yada labarai da nauoinsu daban-daban suna da matukar tasiri wajen tsara tinanin yara masu tasowa da iyalai da aluma gaba dayanta. Hakuwa na faruwa ne saboda abinda suke yadawa mai cike da hanyoyin tasiri da daukan hankali sosai, don haka ya zama wajibi a ribace su ribatar da ta dace, da rikarsu a matsayin wani minbari yada daawa, da yada dabiu ingantattu na musulunci

Manufofin huxubar

Jan hankalin mutane zuwa ga mahimmanci kafafen yaxa labarai.

Haxa kafafen yaxa labarai da yi wa addinin musulunci hidima.

Qarfafa wa wajen kyawawan halayen cikin aikin yaxa labarai.

Fito da matsalolin da kafafen yaxa labarai na musulunci suke fuskanta don neman mafita.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Ya ku ‘yan uwana musulmi a yau zamu tattauna ne akan wani abu mai girma, mai girma saboda girman amfaninsa idan an yi amfani da shi wajen aikin alheri, mai girma saboda girman haxarinsa idan an yi amfani da shi a wajen sharri da varna. Abu ne da yake da iko mai qarfi a cikin rayuwar mutane, har ma babu wanda zai iya fita ko gujewa ikonsa da tasirinsa. Wannan abu ba komai ba ne face kafafen yaxa labarai.

Haqiqa kafafen yaxa labarai irinsu Jaridu da Mujallu kafafe ne masu matuqar tasiri a cikin al’umma, wajen yaxa aqida da xabi’u, idan an ribace su wajen alheri da fahimtar da mutane addini, da abin da zai amfane su a duniyarsu, haqiqa sun zama kafofi mafi girma da amfani, idan kuwa aka yi amfani da su wajen kishiyar haka to sun zama mafi cutarwar kafofi.

Kafar yaxa labarai a wannan zamani wata tasha ce mai mahimmanci, tana da tasiri mai qarfi wajen sharri ko alheri a cikin sha'anin mutane, don haka wajibi ne a yi qoqari a ribaci waxannan kafafe waxanda ake sauraro ko ake kallo ko ake karantawa wajen kiran mutane zuwa ga addinin Allah, da yaxa kyawawan halaye, da yaqar munanan xabi’u.

Saboda haka ina faxakar da masu hali kan dole ne samar da irin waxannan kafafe, waxanda suke magana da yarenmu (hausa), ta yadda zai zama babban aikinsu shi ne yaxa musulunci da Sunnah a cikin al’umma, abin da muke gani na cutuwa da varna da sharri da rushe addini daga wasu kafafen yaxa labarai marasa manufa ya ishe mu.

Yaku al’ummar musulmi : Wajibi ne a kan waxanda suke kula da waxannan kafafen yaxa labarai su ji tsoron Allah, su sani cewa dukkanmu masu kiwo ne, kuma dukkanmu za a tambaye mu akan abin aka bamu kiwo, don haka kada a kuskura a gabatarwa da al’umma sai abin da yake kira ne zuwa ga alheri, da kafa kyawawan xabi'u na musulunci, a siffofi nagari, hakanan wajibi ne a kansu su tsamo al’umma daga dukkan wani abin da zai ruxa mata tunani, ya vata masa aqida, ya gurvata mata halaye, da ayyukansu na yau da kullum.

Yaku ‘yan jarida, aikin jarida matsayin numfashi ne ga al’umma, madubi ne ga mutane, don haka ku kiyaye amanar kalma da harafi, da gaskiyar zance, ku sani cewa da imani da tsoron Allah da kyakkyawar manufa kafafen yaxa labaran musulmi suka fita daban da na arna da kafirai. Ku nisanci qarya da jirkita zance, ku kirdadi gaskiya, ku guji yaxa jita – jita, kada ku faxi duk abin kuka ji ko kuka gani, ya tabbata Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Mutum ya isa maqaryaci ya faxi duk abin da ya ji”. Don haka Kada ku bada labari sai wanda ya tabbata, kada ku yaxa komai sai idan a cikin yaxa shi akwai gyaruwar al'umma a ciki, da yawa daga cikin ‘yan jaridar suna yaxa labaran da baya halatta a yaxa su a cikin mutane, saboda yaxa su yaxa alfasha ne da mummunan abu cikin muminai, Allah Maxaukakin Sarki kuwa ya hana haka, don haka ku ji tsoron Allah a cikin ayyukanku.

Yaku ‘Yan uwana yan jarida : Abin da ya wajaba ku mayar da hankalinku a kai shi ne yaxa aqida ingantacciya, wadda babu shirka da varna a cikinta, saboda Manzon Allah (S.A.W) lokacin ya aiki Mu’azu xan Jabal zuwa Yemen abin da ya yi masa wasiyya da shi kenan da farko, ya ce masa ya kira mutane zuwa ga shaida wa babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawan Allah ne Manzonsa, idan sun amsa masa, sai ya koya musu cewa Allah ya wajabta musu salloli biyar cikin dare da yini… to hakanan ya wajaba akan ‘yan jarida su aikata.

Hakanan wajibi ne akan ‘yan jarida su kira mutane zuwa ga kyawawan halaye da xabi’u, Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Kaxai an aiko ni don in cika kyawawan halaye”.

Hakanan wajibi ne akan kafar yaxa labarai ta zama mai gaskiya da adalci cikin duk abin da zata faxa, domin gaskiya da adalci ana son su a cikin dukkan komai. Hakanan kada kafar yaxa labarai ta nutse cikin yaxa varna da munanan abubuwa cikin al'umma, kuma wajibi ne kafofin yaxa labarai su lura da ladubban tattaunawa, da shiryar da mutane da hikima da kyakkyawan wa'azi. Allah Maxaukakin sarki ya ce, :

(مَا يَلْفِظُ مِنْ قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ18 ) [ق: ١٨].

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa : “Babu wani lafazi da zai faxa face a wurinsa akwai Raqibu da Atidu”.

Allah ya yi mana albarka cikin abin da muka ji, ya amfane mu da abin da yake cikin Alqur’ni da Hadisai. Haqiqa Allah mai iko ne a kan dukkan komai

Godiya ta tabbata ga Allah Maxaukakin Sarki, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xaya, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka :

Yaku bayin Allah, : Muna fama da matsaloli da yawa a cikin kafafen yaxa labaranmu, kuma wajibi ne mu canza su, don kafafen yaxa labarai su taka rawar da ta dace.

Daga cikin irin waxannan matsaloli akwai q arancin samun masu kishin addinin musulunci a fagen yaxa labarai, da yawa daga cikin masu aiki a kafafen yaxa labarai su kan manta da saqon addininsu na musulunci yayin da suke gabatar da aikinsu, kurum abin da ya dame su shi ne me zasu samu na abin duniya daga wannan aiki, don haka zaka ga irin waxannan suna yaxa abin da yake munana wa ne ga addininsu da aqidarsu da al’ummarsu.

Hakanan yana cikin matsalolin da muke fama da su qarancin masu bada gudummawar quxi ga wasu daga cikin kafafen yaxa labarai masu kyakkyawar manufa, don haka sai ka ji irin waxannan kafafe suna fama da rashin kuxi, abin da yake kaiwa da rushewarsu wani lokaci.

Kamar yadda yana cikin abin da yake damun da yawa daga cikin masu yaxa labarai a yau shi ne jahilci da son zuciya, sai ka samu mutum jahili a addini, yana gabatar da wani shirin addini, wanda alal – haqiqa varnar da zai yi ta fi gyaran da zai kawo yawa, don haka wajibi ne akan ‘yan jarida su san waye zai gabatar da kowane shiri, shirin na addini ne ko ba na addini ba. Ya zama ya san abin da zai gabatar, saboda Allah yana cewa :

(وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا36) [الإسراء: 36]

Ma’ana : “Kada ka shiga abin da baka da ilimi a kansa, haqiqa ji da gani da zuciya dukkan waxannan ababen tambaya ne a kansu”. (Isra’i : 36)

Yana cikin abin da ya wajaba a kan ‘yan jarida su lura da shi, waxannan wasannin kwaikwayon, da ake yaxa wa, da yawa da cikinsu suna xauke da guba da cutar wa mai yawa ga al’umma, musamman ma yara da mata, don haka wajibi ne kafin a yaxa wasa a tabbatar da meye manufarsa, me zai biyo bayan yaxa shi.

Daga cikin munanan abubuwan da waxannan wasannin kwaikwayon suka qunsa akwai cire kunya daga zukatan yara, duk da cewa Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Kunya alheri ce gaba xayanta” a wata riwayar “Kunya ba ta kawo komai sai alheri” Bukhari ne ya rawaito.

Daga cikin abin da waxannan wasanni suka qunsa: cakuxuwar maza da mata, da rungume – rungume, da sumba a fili, ba tare da tsoron Allah ba, wanda hakan ya kan sanya yara su xauka cewa irin waxannan al’amura babu laifi a aikata su, sai suma su riqa yi, su tashi a kai.

Daga cikin abubuwar da suke haifarwa : akwai yaxa ayyuka da maganganun alfasha a cikin al’umma, saboda haka ya zama wajibi a kan ‘yan jarida su san abin da za su riqa yaxawa mutane.

Yaku masu sauraro : Muna cikin wani zamani da varna ta yi yawa, don haka ‘yan jarida ku ji tsoron Allah, ku taimaka wajen gyara al’umma daidai gwargwadon ikonku.

Bayin Allah : Wajibi ne akan hukuma da samar da kafafen yaxa labarai masu nagarta, masu tsarki, waxanda za su tsaya wajen yaxa wannan addini ingantacce ga al’umma. Wajibin shugaba ne ya koya wa mutane addininsu, ya tsaftace su daidai iyawarsa, kamar yadda yake wajibi a kan hukuma da tsarkake kafafen yaxa labaranta, ta gyara su, da shiryar da su zuwa ga abin da yake gyaruwar al’umma ne da qasa gaba xaya.

Hakanan wajibi ne a kan xaixaikun mutane su samar da kafafen yaxa labarai masu kyakkyawar manufa, waxanda za su kare mummunan farmakin da ake wa musulunci da musulmi, domin muna sane da cewa a cikin dokokin qasa akwai damar da samar da kafafen yaxa labarai, don haka yana kan mawadata su aikata wannan, wataqila hakan ya zama wani tanadi garesu ranar alqiyama.

Haka ma wajibi ne a kan mutane su yi inkarin duk wani mummunan aiki ko varna da take fitowa daga kafafen yaxa labarai, ta hanya mai kyau da shari’a ta yarda da ita, ko dai da hannu, ko da baki, ko kuma da zuciya, kamar yadda ya zo a hadisin Annabi (S.A.W).

Yaku ‘yan jarida ku ji tsoron Allah, ku sani cewa za a tambayeku a wata rana, gaban masanin gaibu, ranar da babu wani wanda zai voye wa Allah, ranar da ake fayyace sirri, ku yaxa alheri a cikin mutane, a ko yaushe ku riqa tuna duk wanda ya yi nuni ga aikin alheri to kamar ya aikata ne.

Hakanan yaku mutane ku amfanu da kafafen yaxa labarai a cikin abin da bai savawa shari’a ba, ku tuna ba duk abin da aka faxa ko ake yaxa wa ba ne gaskiya, kuma ingantance, wanda Allah yake so, don haka kada ku xauki duk abin kuka ji, kowa ana xaukar maganarsa ana bari, sai Annabi (S.A.W). Ku sani Allah yana cewa :

(وَقُلِ اعْمَلُوا فَسَيَرَى اللَّهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ105) [التوبة: ١٠٥]

Ma’ana : “Ka ce (musu) Ku yi aiki da sannu Allah da Manzonsa da Muminai za su ga aikinku). (Attauba : 105).