islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Kisfewar rana da wata


9235
Surantawa
lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah, waxanda suke nuni ga cikar qudurarsa, da cikar kamalarsa da hikimarsa da rahamarsa. Idan ka yi dubi girmansu, da tsarin tafiyarsu, za ka gane girman qudurar Allah. Kuma idan ka yi dubi maslaha da amfanin da ke cikin savawa a cikin tafiyarsu, za ka tarar cewa a cikin wannan akwai cikar kamala da rahamar Allah. Ku saurara! Yana daga cikin hikimar Allah a wajen tafiyarsu abin da yake faruwa na kusufi, wanda shi ne gushewar haskensu gaba xaya, ko wani sashensa. Lallai hakan yana faruwa ne da umarnin Ubangiji. Allah yana tsoratar da bayinsa da shi, domin su tuba zuwa gare shi su nemi gafararsa, su bauta masa, su girmama shi.

Manufofin huxubar

Wa’azantuwa da ayoyin Allah da halitta a sararin samaniya.

Tunani a kan halittar sama da qasa yana tunatarwa xan-adam cewa, ajalinsa ya kusa.

Izinar da take cikin kusufin rana da wata, da abin ya wajaba yayin da ya faru.

Kira zuwa ga gaggauta tuba da aiki na qwarai.

Jan-kunne a kan aikata wasu laifuffuka.

Sanin lokacin kusufi ba ya ciki sanin ilimin gaibi.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ku ji tsoron Allah ya ku musulmai haqiqanin jin tsoron Allah maxaukakin sarki, ku yi tunani akan abubuwan da ya halitta a cikin sammai da qassai, lallai a cikin wannan akwai aya ga masu hankali. Ku yi tunani a waxannan samman qarfafa da Allah Ya xaukaka da qarfinsa, kuma Ya riqe su da qudurarsa, da rahamarsa ta yadda ba za su faxo kan bayi ba. Ku yi tunani a kan yadda Allah ya gina su ba tare da wata varaka ko tsaga ba, da kuma yadda Ya qawaita sama da fitilu, waxanda suka mamayeta da kyawu da haske. Kuma ya halicci rana mai haske wata mai haskawa. Sannan sai ku yi tunani, yaya waxannan abubuwa masu haskakawa da fitilu suke tafiya da izinin Allah, a kan falakinsu wanda Allah Ya xora su a kai tun lokacin da ya halicce su har zuwa lokacin da za a tarwatsa su, ba sa qarawa a kan tafiyarsu kuma ba sa ragewa, kuma ba sa tashi daga kan wurin kuma ba sa kaucewa. Tsarki ya tabbata ga wanda yake tafiyar da su da qudurarSa, ya tsururuci wannan tsarin nasu da hikimarsa, kuma shi ne Mai qarfi Mabuwayi.

Ya bayin Allah, lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah, waxanda suke nuni ga cikar qudurarsa, da cikar kamalarsa da hikimarsa da rahamarsa. Idan ka yi dubi girmansu, da tsarin tafiyarsu, za ka gane girman qudurar Allah. Kuma idan ka yi dubi maslaha da amfanin da ke cikin savawa a cikin tafiyarsu, za ka tarar cewa a cikin wannan akwai cikar kamala da rahamar Allah.

Ku saurara! Yana daga cikin hikimar Allah a wajen tafiyarsu abin da yake faruwa na kusufi, wanda shi ne gushewar haskensu gaba xaya, ko wani sashensa. Lallai hakan yana faruwa ne da umarnin Ubangiji. Allah yana tsoratar da bayinsa da shi, domin su tuba zuwa gare shi su nemi gafararsa, su bauta masa, su girmama shi.

Ya bayin Allah, lallai Allah Mai girma da xaukaka Yana nunawa bayinsa abin da zai tunatarsu a cikin sasannin samaniya, in har sun kasance masu yin imani ne. Allah yana cewa:

( سَنُرِيهِمْ آَيَاتِنَا فِي الْآَفَاقِ وَفِي أَنْفُسِهِمْ حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُ الْحَقُّ أَوَلَمْ يَكْفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ 53 ) [فصلت: 53]

(Za Mu nuna musu ayoyinmu a cikin sasannin sama da kuma a cikin kawunansu, har ya bayyana a gare su cewa lallai (Alqur’ani), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cewa lallai shi Halartacce ne a kan kowane abu?).

Sannan Allah ya same jan hankalinmu da mu duba ayoyinsa a cikin sammai da qassai, domin mu dinga tuna cewa duniya ta zo qarshe, don mu yi guzurin tafiyar da babu dawowa, mu daina nawa. Kuma dole ne mu san gajartar rayuwar duniya, duk kuwa da yadda ta yi tsawo. Da kuma kusantowar lahira, ta hanyar kusantower ajali. Kuma idan xan adam ya rasu to shi alqiyamarsa ta tsaya, domin a wannan lokaci ba wani aiki, kuma ba riskar wani abu, kawai hisabi ne a Barzahu sannan kuma da gidan lahira. Allah yana cewa:

( أَوَلَمْ يَنْظُرُوا فِي مَلَكُوتِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا خَلَقَ اللَّهُ مِنْ شَيْءٍ وَأَنْ عَسَى أَنْ يَكُونَ قَدِ اقْتَرَبَ أَجَلُهُمْ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ 185 ) [الأعراف: 185]

“Shin, ba su yi duba ba a cikin mulkin sammai da qasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kome, kuma akwai tsammani kasancewar ajalinsu, haqiqa ya kusanto? To da wane labari a bayansa suke yin imani”.

Sannan wanda ba ya wa’aztuwa da ayoyin da suke watse a cikin sararin samaniya, sai ya yi la’akari da faxin Allah:

(Wanda Allah ya vatar, to, babu mai shiryar da su, kuma yana qale su, a cikin vatansu suna ximuwa).

A wata faxar kuma Allah Ya ce:

( قُلِ انْظُرُوا مَاذَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا تُغْنِي الْآَيَاتُ وَالنُّذُرُ عَنْ قَوْمٍ لَا يُؤْمِنُونَ 101 ) [يونس: 101]

“Ka ce, “Ku dubi abin da yake cikin ammai da qasa Kuma ayayo da gargaxi ba su wadatar da mutanen da ba su yi imani ba).

Sannan Allah ya tsoratar da mutane mummunan kamunsa, a inda ake faxa maxaukakin sarki, bayan wannan ayar:

( فَهَلْ يَنْتَظِرُونَ إِلَّا مِثْلَ أَيَّامِ الَّذِينَ خَلَوْا مِنْ قَبْلِهِمْ قُلْ فَانْتَظِرُوا إِنِّي مَعَكُمْ مِنَ الْمُنْتَظِرِينَ 102 ثُمَّ نُنَجِّي رُسُلَنَا وَالَّذِينَ آَمَنُوا كَذَلِكَ حَقًّا عَلَيْنَا نُنْجِ الْمُؤْمِنِينَ 103 ) [يونس: 103]

“To, shin suna jiran wani abu face kamar misalin kwanukan waxanda suka shuxe daga gabaninsu? Ka ce, “Ku yi jira! Lallai ni tare da ku, ina daga masu jira. Sannan sai mu tseratar da manzanninmu da waxanda suka yi imani, kamar wannan ne tabbatacce ne a gare mu, kuvutar da masu imani).

Allah yana da hikimomi masu yawa dangane da halittar sammai da qasa, kamar yadda Yake cewa:

( حِكْمَةٌ بَالِغَةٌ فَمَا تُغْنِ النُّذُرُ 5 ) [القمر: 5]

(Hikima cikakkiya! Sai dai abubuwan gargaxi ba sa amfani.)

Sau nawa Allah Yana turo da gargaxi a harasan manzanni, kuma sau nawa Allah Yana turo da wani abin gargaxi a cikin sasannin duniya, sai dai kamar yadda maxaukakin sarki yake cewa: “Sai dai abubuwan gargaxi ba sa amfani”.

Ya inganta daga manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga ayoyin Allah ba sa yin kusufi don mutuwar wani ko don rayuwar wani, sai dai Allah yana tsoratar da bayinsa da su. Idan kun ga wani abu na daga haka, ku yi gaggawa zuwa ga zikirin Allah da kuma zuwa ga Sallah da addu’a da istigfari”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

To, shin mun yarda da tsoratarwar da Ubangijinmu yake yi mana, kuma mun tsorata xin, sannan muka kama hanyar komawa gare shi tun farkon dare. Ya tabbata daga manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Duk wanda ya ji tsoro zai kama hanya tun farkon dare, wanda kuma ya kama hanya tun farkon dare to zai isa masaukinsu. Ku saurara, lallai hajar Allah mai tsada ce, lalle hajar Allah ita ce aljanna”. Tirmizi ne ya ruwaito shi.

Yana daga cikin yarda da tsoratarwar Ubangijinmu a gare mu, shi ne mu ji tsoro mu yi aikin kirki, mu guji mummunan aiki. Mu yi istigfari mu tuba daga sauran zunubai. Haka kuma mu yi addu’a mu yi zikiri, kar mu yi xagawa da alfahari. Mu yi sadaka sosai kuma mu guji azabar Sa’ira. Har sai Allah ya tabbatar da mu da tabbataccen zance a duniya da lahira kamar yadda Maxaukakin sarki yake cewa:

Ma’an: (Allah yana tabbatar da waxanda suka yi imani da magana tabbatacciya a cikin rayuwar duniya, da kuma Lahira. Kuma Allah Yana vatar da azzalumai, kuma Allah Yana aikata abin da Yake so).

Abin nufi da faxarsa: “ a rayuwar duniya”, shi ne a cikin qabari a daidai lokacin da za a dawo da ran mamaci zuwa gangar jikinsa, a lokacin yana jin takun takalman waxanda suka kawo shi, a yayin da suka juya suna komawa. Sai wasu mala’iku guda biyu su zo masa, su daka mishi tsawa. Sai su tashe shi su zaunar da shi, sai su ce masa: “wanene Ubangijinka? Menene addininka? Wani wannan mutumin da aka aiko a cikinku? Mene ne iliminka? Shi dai mumini zai ce, “Ubangijina shi ne Allah. Addinina kuma shi ne musuluncil. Annabina shi ne Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Na karanta littafin Allah sai na yi imani da shi na kuma gaskata. Wannan ita ce qarshen fitinar da za a bijirowa mumini. A wannan shi ne ma’anar faxar Allah “Allah yana tabbatar da waxanda suka yi imani da magana tabbatacciya a cikin rayuwar duniya). Amma fajiri sai ya ce: Ha! Ha! Ban sani ba, na ji mutane suna cewa kaza. Sai a ce masa; “Ba ka sani ba. Ba ka karanta ba”. Abu Dawud ne ya ruwaito shi.

Don haka sai mu xauki wannan al’amari da matuqar mahimmanci. Kuma mu yi tanadin neman tsari daga azabar qabari, kamar yadda manzon Allah ya umarce mu, yayin da aka yi kusufi, inda yake cewa: “Ku nemi tsarin Allah daga azabar qabari”. Sannan ya koyar da mu neman tsari daga wannan azaba a qarshen kowace sallah, inda muke cewa: (Ya Allah ina neman tsarinka daga azabar qabari da azabar wuta da fitinar rayuwa da mutuwa da kuma sharrin fitinar Dujal mai shafaffiya albarka). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Yana daga cikin abubuwa masu halakarwa da manzon Allah ya tsawatar a kansu, a lokacin da aka yi kusufi, shi ne zina. Inda yake cewa: (Ya ku al’ummar Muhammad, ba wanda ya fi Allah kishin ya ga bawansa ya yi zinam ko baiwarsa ta yi zina. Ya al’ummar Muhammad, da kun san abin da na sani da kun yi dariya kaxan, da kuma kun yi kuka mai yawa.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Don haka sai mu gujewa zina da duk sabubbanta ya bayin Allah, kuma mu rufe dukkanin qofofinsa. Kuma mu sani ba wanda ya fi Allah kishi, don haka mu guji fushinsa, kuma mu guji duk wani abu da ke kusantarwa zuwa ga zina, domin mu yi aiki da faxar Allah inda yake cew: “Kada ku kusanci zina, lallai ta kasance alfasha ce, kuma hanyar ta ta yi muni”. Kuma daina zira ga abin Allah ya haramta, kamar yadda Ubangijinmu ya yi mana wannan tarbiyyar, a cikin faxinsa:

( قُلْ لِلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَلِكَ أَزْكَى لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ 30 وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ ) [النور: 30 - 31]

(Ka ce wa muminai maza su kame ganinsu, kuma su tsare farjinsu. Wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lallai ne Allah, Masani ne ga abin da suke sana’antawa. Kuma ka ce wa muminai mata, su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjinsu…).

Wanda bai wa’azntu da tsoratarwar Allah ba, yaushe ne kuma zai wa’aztu. Wanda zuciyarsa ta gafala yaushe zai faxaku ya dawo kan hanya. Shin mai muke jira ne, ko sai mutuwa ta zo mana ba shiri, kamar yadda Allah ya ce:

( حَتَّى إِذَا جَاءَ أَحَدَهُمُ الْمَوْتُ قَالَ رَبِّ ارْجِعُونِ 99 لَعَلِّي أَعْمَلُ صَالِحًا فِيمَا تَرَكْتُ كَلَّا إِنَّهَا كَلِمَةٌ هُوَ قَائِلُهَا وَمِنْ وَرَائِهِمْ بَرْزَخٌ إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ 100 ) [المؤمنون: 100]

(Har idan mutuwa ta je wa xayansu, sai ya ce, ‘Ya Ubangijina, ku mayar da ni (duniya). Tsammanina in aikta aiki na qwarai cikin abin da na bari. Kayya! Lallai ne ita kalma ce, shi ne mafaxinta, alhali kuwa a baya gare su akwai wani shamaki har ranar da za a tayar da su).

Hadisi ingantance ya zo daga Manozon Allah (ﷺ), a yayin da aka yi kusufi, ya ce: “Lallai haqiqa an yi min wahayi cewa, za a fitine ku a cikin qabari, kwatankwacin ko kuma kusa da fitinar Dujal. Abu Dawud ne ya ruwaito shi.

Muna neman tsarin Allah daga fitinar qabari, muna neman tsarin Allah daga fitinar rayuwa da ta mutuwa, muna neman tsarin Allah daga fitinar Dujal shafaffe. Ba wanda ya fi Allah tausayi, kuma Shi ne yake cewa:

( وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكُمْ لَئِنْ شَكَرْتُمْ لَأَزِيدَنَّكُمْ وَلَئِنْ كَفَرْتُمْ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٌ 7 ) [إبراهيم: 7]

(Idan kun gode zan qara muku, amma idan kun butulce, lallai haqiqa azabata mai tsanani ce).

Ba wanda ya fi Allah haquri, Shi ne yake cewa,

( وَمَنْ يَحْلِلْ عَلَيْهِ غَضَبِي فَقَدْ هَوَى 81 ) [طه: 81].

(Kuma wanda fushina ya sauka a kansa, to lallai ya halaka).

Duk wanda yake fito-na-fito da Allah ta hanyar sava masa to haqiqa ya tave. Allah yana cewa: “Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na qarshenku da mutanenku da aljanunku sun kasance da zuciyar mutumin da ya fi kowa tsoron Allah daga cikinku, wannan ba zai qari mulkina da komai ba. Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na qarshenku da mutanenku da aljanunku sun kasance da zuciyar mutumin da ya fi kowa fajirci daga cikinku, wannan ba zai ragi mulkina da komai ba. Ya ku bayina lallai ayyukanku ne nake lissafa muku, sannan nake qididdige muku su, sannan in cika muku su. Duk wanda ya sami alheri, sai ya godewa Allah, wanda kuma ya sami savanin haka, kar ya zargi kowa sai kansa. Muslim ne ya ruwaito shi, daga Abu Zarr, Allah Ya yarda da shi.

Allay ya amfanar da ni da ku da shiriyar littafinsa. Wannan shi ne abin da zan ce, ina neman gafarar Allah ga kaina da kuma ku, da dukkanin sauran musulmi daga kowane irin zunubi, ku nemi gafararsa, lallai shi mai gafara ne mai jinqai.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Manzon Allah (ﷺ). Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! A nan muna son mu faxakar da ku akan wasu abubuwa waxada dadama daga cikin mutane ba su sansu ba. Na farko: Bayar da labarin Kusufi kafin ya faru, ba wani abu ba ne daga ilimin gaibu, kawai dai yana daga cikin ilimi na yau da kullum, wanda xan adam zai iya sani. Shekhul Islam, Ibn Taimiyya Allah ya yi masa rahama, ya ce: “Al'adar Allah ta gudana akan cewa, Kusufin rana yana aukuwa ne a qarshen wata. Shi kuma kusufin wata yana faruwa a tsakiyar wata, wato cikin dararen sha uku ko sha huxu ko sha biyar. To shi wata ba ya Kusufi sai a waxanna darare. Sannan kuma har ila yau, watan yakan vuya ne a ranakun ashirin da tara da kuma talatin, to ita kuma rana ba ta yin nata Kusufin sai a waxannan kwanaki da wata yake vuya. Sannan da rana da wata, dukkansu suna da wasu kwanaki sanannu a bisa al’ada, wanda ya san su to zai san lokacin faruwar kusufin rana ko na wata.

Ibn Taimiyya ya qara da cewa: “Amma sanin wani abu game da al’adar kisfewar rana da wata, wannan wani abu ne da waxanda suke da ilimin tafiyar rana da wata suka sani. Ba ilimin gaibi ne ba, kawai kamar ilimi ne na sanin canjin yanayi". Ya qara da cewa: “Sai dai duk lokacin da masana lissafi maganarsu ta zo xaya akan sha'anin kusufin rana ko na wata, to yana da wuya su yi kuskure. Amma kuma duk da haka ba a gina wani abu na shari'a akan maganarsu, domin ita dai sallar Kusufi, ba za a yi ta ba, har sai mun gani da idanuwanmu". Ya ci gaba da cewa: “Idan mutum ya yi shiri domin ganin wannan lokaci, wato abin masana suka ba da labarinsa, to yin haka ya dace domin yana da cikikin gaggawa ne zuwa ga biyayya ga Ubangiji Maxaukakin Sarki, tare da yi Masa bauta.”

Abu na biyu: Lallai rana ta tava kisfewa a zamanin Manzon Allah (ﷺ), sai ya fito a firgice, har yana jan gwadonsa a qasa, har sai da ya iso masallaci, sannan aka jama'a domin sallah. Nan da nan sai mutane suka taru. Sai Manzon Allah ya yi sallah raka’a biyu. A kowace raka’a akwai ruku’u biyu da sujjada biyu. Sai ya yi kabbara ya karanta Fatiha da wata sura mai tsawo, kamar Suratul Baqara. Har sai da sahabbansa suka dinga faxuwa saboda tsawon tsayuwar. Sannan ya yi ruku’u, ya tsawaita ruku’un, sannan ya ce: Sami’al Lahu Liman Hamidahu, Rabbana walakal Hamd. Sannan ya qara karanta Fatiha da wata sura mai tsawo, ba ta farko ba, sannan ya qara yin wani ruku’u mai tsawo ba na farko ba. Sannan ya ce: Sami’al Lahu Liman Hamidahu, Rabbana walakal Hamdu. Sannan ya tsawaita tsayuwar, sannan ya yi sujjada. Daga nan bayan ya xago daga sujjada sai ya tsawaita zama a tsakanin sujjada, sannan ya yi sujjada ya tsawaita ta. Daga nan sai ya tashi zuwa raka’a ta biyu. Sai ya tsawaita tsayuwar, amma ba ta kai tsayuwar da ya yi a raka’ar farko ba. Sannan ya yi ruku’u ya tsawaita ruku’un, amma bai kai tsawon ruku’un da ya yi a raka’ar farko ba. Sannan ya ce: Sami’al Lahu Liman Hamidahu, Rabbana walakal Hamdu. Sannan ya qara karatu ya tsawaita karatun, amma bai kai na farko ba. Sannan ya yi ruku’u, ruku’u na biyu, ya tsawaita shi, kuma shi ma bai kai na farkon ba. sannan ya yi sujjada guda biyu, sai ya yi sallama. A lokacin har rana ta bayyana. Kuma an ji shi a cikin sujjadarsa (ﷺ), yana cewa: “Ya Ubangiji ba ka yi mini akawarin ba za ka musu azaba ba alhalin ni ina cikinsu? Kuma ba ka yi mini alkwarin ba za ka yi musu azaba ba matuqar dai suna yin istigfari?

Daga nan sai ya yi wa mutane huxuba, ya yi musu cikakken wa'azi. Ya yabi Allah, da abubuwan da suka kamace Shi, Maxaukakin Sarki, sannan ya ce: “Lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu, daga ayoyin Allah ba sa kisfewa domin mutuwar wani ko don rayuwarsa. Idan kun ga haka, ku yi gaggawa zuwa ga sallah, ku yi gaggawa zuwa masallaci, ku yi gaggawa zuwa zikirin Allah da roqonsa da neman gafararsa”. A wata ruwayar “Ku yi addu’a, ku yi sadaka, ku yi Sallah”. Sannan ya ce: “Ya al’ummar Muhammdu, babu wani wanda ya fi Allah kishi, daga bawanSa ya yi zina, ko baiwarSa ta yi zina. Ya al’ummar Muhammadu, wallahi da kun san abin da na sani da kun yi dariya kaxan, kuma da kun yi kuka da yawa. Ya ce: Ba wani abu da aka yi muku alqawarisa, face sai na gan shi a cikin sallata wannan. Kuma an yi min wahayi, cewa lallai za a fitine ku a cikin qaburburanku, kusa ko kwatankwacin fitina Dujal". Sannan ya umarce su da su nemi tsari daga azabar qabari, sannan ya ce: “Lallai an zo da wuta, sashenta yana makar sashe, wannan shi ne lokacin da kuka gan ni na ja da baya, tsoron kada wani abu ya same ni daga hucinta. Har sai da na ga Amr xan Luhaiy a cikinta, yana jan 'yan hanjinsa a cikin wuta. Sannan na ga matan nan da ta xaure mage, ita ba ta ba ta abinci ba kuma ba ta qale ta ta fita ta nemi abincinta da kanta ba, har sai da yunwa ta kashe ta". Sannan ya ce: "Sai aka zo da aljannah, shi ne a lokacin da kuka gan ni na xan yi gaba, har na tsaya a wannan gurin da na tsaye. Kuma na miqa hannuna, ina qoqarin in tsiko kayan marmarinta domin ku gani da idanuwanku. Sai kuma na ga kada in yi hakan".

Ya al'ummar Annabi Muhammad! Ku sani fa kusufin rana ko wata wani baban al'amari ne mai ban tsoro. Baban dalili kuwa iri yadda Manzo (ﷺ) ya firgita ya yi gaggawa zuwa ga sallah yayin da rana ta yi kusufi. Sannan da irin waccan gamsasshiyar huxuba da ya yi. Don haka wajibi mu riqa tsorata duk sa'adda muka ga kusufi na rana ko wata, sannan mu yi gaggawar yin sallah da addu'a a masallatanmu, mu nemi gafarar Allah. Kuma mu yi ta yin sadaka. Kuma Annabi (ﷺ) ya yi umarni da 'yanta baiwa ko bawa lokacin da kusufi ya faru. Domin wanda duk ya 'yanta wani shi ma za a 'yanta shi daga shiga wuta. Don haka waxannan abubuwa su ne suke taimakawa wajen yaye bala'in da yake tattare da kusufin rana ko wata.

Ya ku musulmi ku sani duk sa'adda aka samu kusufi to ana yin gaggawar fara sallah, a kowane lokaci hakan ta faru, ba a la'akari da cewa ko wannan lokacin yana daga cikin lokuta da aka hana yin sallah a cikinsu. Domin wannan salla ce ta roqon Allah ya yaye wani bala'ai da ya sauka. Don haka za a iya yinta bayan la'asar, da bayan asuba, da lokacin hodowar rana.

Kuma ku sani ana son a sunna a yi wannan sallar cikin jam'i a masallatai. Kamar yadda Manzon Allah (ﷺ) ya yi. Kuma mata da maza suka halarci wannan sallah tare da shi. Amma koda mutun shi kaxai ya yi ta yi.

Allah Ta'ala yana cewa:

( وَمِنْ آَيَاتِهِ اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ لَا تَسْجُدُوا لِلشَّمْسِ وَلَا لِلْقَمَرِ وَاسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَهُنَّ إِنْ كُنْتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ 37 ) [فصلت: 37]

(Yana daga cikin ayoyinsa, dare da yini, da rana da wata. Ka da ku yi sujjada ga rana ko wata. Ku yi sujjada ga Allah wanda shi ne ya halicce su, idan har kun kasance shi kaxai kuke bautawa).