islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Munana zato


8785
Surantawa
Musulunci ya himmantu da karfafa damkon soyayya tsakanin musulmai, da karfafa igiyar yan-uwantaka tsakanin muminai, don haka ne yayi kira zuwa ga duk abinda zai kara damkon wannan zumuntar, Kaman yada sallama, da musafaha yayin haduwa, da dai sauransu. Hakanan musulunci ya tsoratar game da duk abinda zai raunana wannan soyayya, kamar mummunan zato tsakanin musulmai, da gulma da annamimanci , da dai sauran su. Lallai mummunan zato wata babbar hanya ce ta yada gaba da kiyayya tsakanin musulmai, da yanke alaqoqi, da wargaza iyalai, da bata yan-uwantakar musulunci.

Manufofin huxubar

Magance wannan mummunar xabi’a

Koyar da mutane samun nutsuwa a zuciya

Qarfafa ‘yan uwantaka tsakanin musulmi

Huxuba Ta Farko

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka;

Ya ku musulmi! Haqqin da yake kanmu shi ne samar da alaqarmu ta zama mai qarfi tabbatacciya kamar ginin bulo-da-bulo, mu fuskanci mutane da farar aniya, mu fuskance su da so da qauna, da sakakkiyar fuska, kuma mu kyautata zato a wajen mu’amalar mu da juna. Mu cire duk wani zargi wajen kallon ayyukan mutane da maganganunsu. Sau tari za ka ga wasu idan wani ya samu wata ni'ima ko wani cigaba na rayuwa sai su shi ga cikin baqin ciki da vacin rai, da samun qunci da rashin walwala da kiximewa saboda wannan ci gaba da ya samu a raywarsa. Dayawa za ka ji idan musulmi sun zauna a majalisa babu abin da suke cewa sai dai.. Ko wani kaza yake nufi da abin nan da yayi, ko ya aikata. Babu abin da suke yi sai munana zato ga ‘yan uwansu, wanda baya haifar da komai sai kawo gaba da qyashi da kawo tarwatsewar haxin kan jama’a, da raba ‘yan uwantaka, da raba zumunci, da kawo shakku a xaixaikun al’umma.

Dayawa mun gani ko muna jin mutane suna faxin irin sakamakon munanan zato da mutane suke yiwa juna. Idan kuma mummunan zato ya mamaye zuciya to babu abin da zai haifar sai saurin tuhamar juna, da kuma bin diddigin asiran mutane da zubar musu da mutunci, da binciken makusanci, har ka ji mai munana zato ga al’umma yana cewa “Zan yi qoqarin gano haqiqanin abin da ake ciki” wajen bincikensa, sai kuma ya ci zarafin xan uwansa, ko ya aibata shi, aqarshe sai ka ga ya yi laifi kashi-kashi. Lallai munana zato a tsakanin mutane yana kawo lalata alaqa da gaba da kuma son zuciya da ruxani, wannan kuma shi ya ke rusa soyayya a tsakanin mu, da kuma qeqashewar zukata, da rashin amincewa juna. Sai su fara gaba da juyawa juna baya da yanke zumunta. Al’amarin da zai magance mana wannan shi ne faxin Allah ta’al:

( وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَا تَنَازَعُوا فَتَفْشَلُوا وَتَذْهَبَ رِيحُكُمْ وَاصْبِرُوا إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ 46 ) [الأنفال: 46]

Ma’ana: (Kuyiwa Allah xa’a da manzonsa kuma kada ku yi savani a tsakanin ku, sai kuraraba kuma kwarjininku ya tafi, kuyi haquri, lallai Allah yana tare da masu haquri).

Al’umma sun kasance masu tarbiyya irinta musulunci, da kuma kyakkyawar zuciya, da ‘yan uwantaka, da tausayi, kuma alaqarmu takasance kamar ginin bulo da bulo.

Ya ku bayin Allah! Ku sani munana zato baya kawo alkhairi, sai dai ya zama ya kawo sharri da gaba da yanke zumunta, da tarwatsa dangi da vata ‘yan uwantaka ta musulunci. Kaxan ne daga cikin masu munana zato ba sa aikin savo. A lahira kuma za su yi nadama. Allah ya tsare mu. Allah (S.W.T) yana cewa:

( وَقَالُوا مَا لَنَا لَا نَرَى رِجَالًا كُنَّا نَعُدُّهُمْ مِنَ الْأَشْرَارِ 62 أَتَّخَذْنَاهُمْ سِخْرِيًّا أَمْ زَاغَتْ عَنْهُمُ الْأَبْصَارُ 63 ) [ص:62 - 63]

(Kuma suka ce, ‘me ya same mu, ba muganin waxansu mazaje mun kasance muna qidaya su daga ashararai? Shin mun riqe su abin izgili ne. ko idanunmu sun karkafta daga gare su ne?).

Masu tafsiri dadama sun fassara «Ashararai» a wannan ayar da cewa ana nufin su ne raunanan musulmi, waxanda ake masu izgili a nan duniya, ake tsammanin Allah ba zai tava musu rahma ba a lahira..

Kuma waxanda mujrimai suka kasance suna yi musu isgilanci a nan duniya, suma za su rama a gobe alqiyama kamar yadda Allah (S.W.T) ya ce:

( إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُوا مِنَ الَّذِينَ آَمَنُوا يَضْحَكُونَ 29 وَإِذَا مَرُّوا بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ 30 وَإِذَا انْقَلَبُوا إِلَى أَهْلِهِمُ انْقَلَبُوا فَكِهِينَ 31 وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَؤُلَاءِ لَضَالُّونَ 32 وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ 33 فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آَمَنُوا مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ 34 ) [المطففين: 29 - 34]

(Lalle ne waxanda suka kafirta sun kasance (a duniya) suna yiwa waxanda suka yi imani dariya. Kuma idan sun shuxe su, sai su dinga yin zunxe. Kuma idan suka juya zuwa ga iyalansu, sai su tafi suna kakaci. Kuma idan sun gansu sai su ce “lalle waxannan vatattune”. Alhali kuwa ba a aike su ba domin su zama masu tsaro akansu. To yaufa (a lahira) waxanda suka yi imani, suke yiwa kafirai dariya).

Hakanan Allah ta’ala yana cewa:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ) [الحجرات: 12]

Ma’ana: (Yaku waxanda suka yi imani, ku guji yawancin zato, domin wani vangare na zato zunubi ne).

Waxannan ayoyi suna nuni akan kiyaye mutunci musulmi matuqar kiyayewa, da rashin munana masa zato, idan kuma an ga wani yanayi to sai ayi masa nasiha.

Wannan kira ne ga muminai da su kiyaye kawunansu daga munana zato ga kowa, da samun haxin kai a tsakaninsu da rashin bibiyar asiran juna, kamar yadda ya zo a cikin littafin (Musannaf) na Abdurrazaq daga Abu Huraira yace daga Annabi (ﷺ) ya ce, “Ku guji zato, domin zato, shi ne mafi qaryar zance, kada ku riqa satar maganganun juna, kada ku riqa leqan asirin juna, kuma kada ku riqa yiwa juna hassada, kada ku yi gaba da juna, kada ku juya baya atsakaninku, ku zama bayin Allah ‘yan uwan juna.

Ya bayin Allah,

Wasu malamai sun ce. munana zato ga mutumin da halayensa na kirki suka bayyana da nagartarsa ta amanarsa, to haramun ne. Amma mutumin da halayensa marasa kyau, suka fito fili, ya kuma kasance mai bayyanar da varna to babu laifi idan an munana masa zato.

An karvo daga Sa’id xan Musayyib, yace “wani xan'uwana daga cikin sahabban Manzon Allah (S.W.A.) ya rubuto mini cewa, "Kasance mai kallon xan'uwan da kyawawan zato, har sai munanan halayensa sun bayyana gare ka. Duk kamlar da ta fito daga bakin xan uwanka, to kada ka yi mata mummunar fassara matuqar kana iya ba ta kyakkyawar fassara".

Don haka, wannan qa'ida ce mai mahimmanci, musamman wajen mu'amalantar manyan mutane masu daraja cikin al'umma. Amma duk da haka sai ka ga wasu ba su fahimci hakan ba. Sai ka ga sun yanke wa mutum hukunci ba tare sun yi la'akari da niyyarsa ba. Mutum kuwa zai iya mummunar magana ba tare da ya yi nufi ba, illa iyaka zamiyar harshe ya samu, Kamar yadda Ibn Qayyim yake cewa, “Kalma xaya mutane biyu suna iya amfani da ita, xaya yana nufin mummunar ma’ana, xaya kuma baya nufin haka, saboda lura da halayensa, da abin da yake kira zuwa gare shi yake karewa. Don hakane ba’a kafirta mutumin da yayi kuskure ba saboda tsabar farin ciki ya ce, “Allah kai ne bawana, ni kuma Ubangijinka” kalmace ta kafirci idan muka kalleta da wannan ma’ana, amma shi da ya faxeta, ba haka yake nufi ba ya faxeta ne bisa kuskure saboda tsananin farin ciki.

Sheikhul Islam Ibn Taimiyya yake cewa lokacin da yake kallon maganar waxanda suka sava masa, sai yace “Wannan magana dunqulalliya, mai son gaskiya yana iya ba ta ma’ana mai kyau. Marar gaskiya kuma zai shigar abubuwa diyawa a qarqashinta".

Wannan shi ne tsarin da malamai magabata na qwarai suka rayu akansa. saboda kasancewarsu masu tsarkakkiyar zuciya, da kaucewa son zuciya da yiwa al’umma nasiha, sukan kalli maganganun mutane ta fuska mai kyau.

Yaku bayin Allah, yana daga cikin munana zato, fassara maganganun wasu da aikinsu da mummunar fassara, da tuhuma ba tare da bincike ba, ko nema musu mafita, da qoqarin yin mummunar fassara ga kowace magana ko aiki wanda yake xaukar fuska biyu, fuskar alkhairi da fuskar sharri. Don me mutane suke yin hukunci akan abin da yake cikin zukata, bayan kuma sanin abin da zuciya ta voye da hisabinta haqqine na Allah (S.W.T) wanda shi ne masanin abin da yake voye da bayyane. Amma shi xan Adam ba shi da haqqin shiga cikin abin da yake voye, sai dai abinda yake bayyane. wannan shi ne abinda magabata na qwarai suka kasance akansa, waxanda zukatansu suke cike da ilimi na musulunci tatacce.

Abdurrazzaq ya ruwaito hadisi a cikin littafinsa Al-Musannaf daga Abdullah xan Utbah xan Abdullah xan Mas’ud ya ce: Na ji Umar xan Khaxxab (R.A) ya ce “Mutane ana gane kurakuransu a zamanin Manzon Allah (ﷺ) ta hanyar wahayi. Amma yanzu wahayi ya daina sauka, don haka mu yanzu muna gane kurakuranku ne da abin da ya bayyana na ayyukanku. Duk wanda ya bayyana mana alherinsa, sai mu zauna da shi lafiya, kuma mu kusanto shi, babu ruwan mu da abin da yake na zuciyarsa, Allah shi ne zai yi masa hukunci akan abin da ya voye a zuciyarsa. Wanda kuma ya bayyanar mana da sharrinsa, to ba zamu amince masa ba, kuma ba zamu gaskata shi ba, koda ya ce, shi da zuciya xaya yake zaune da mu".

Ya zama wajibi akan kowa ne musulmi ya binciki kansa game da kowace kalma da zai furta,ko wani hukunci da zai yanke, ya riqa tuna faxin Allah ta’ala,

( وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا 36 ) [الإسراء: 36]

“Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi. Lalle ne ji da gani da zuciya, dukkan waxannan, abin da ake tambayar mutum ne akansu) (Suratul Isra’i 35).

Abin da kuke ji shi ne abin da zan faxa muku. Ina kuma neman gafarar Allah gare ni da kuma sauran musulmi daga kowane zunubi, ku nemi gafarar Ubangiji, domin shi mai gafara ne, mai rahama.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu wanda fushin Allah yake sauka akansa sai azzalumai, tsira da aminci su tabbata ga shugaban manzanni, Annabin mu Muhammad kuma masoyinmu, da kuma iyalansa da sahabbansa da kuma waxanda suka bi tafarkinsu har zuwa ranar sakamako.

Ya ku bayin Allah! Mummuna zato yana da wasu dalilai da suke haddasa shi. Babban abin da yake haddasa xabi’a ta mummunan zato shi ne tarbiyyar da mutum ya samu daga gida ko ya abokai. Domin duk sanda mutum ya biye wa son zuciyarsa, sai ka ga ya faxa cikin xabi’ar munana zato. Idan mutum yana son abu sai ya makance ya kurumce. Hakanan idan ya so wani, sai ka ga ya rufe idonsa ba ya ganin kuskurensa ko da kuwa yana da kuskuren. Idan kuma ba ya son mutum, to ba zai tava ga farinsa ba. Ko da yaushe zai riqa bin diddingasa ne don ya samo kurakuransa.

Waxansu mutane kuwa suna ruxawa da cewa a kodayaushe su ne mutanen kirki, sauran mutane kuma akan kuskure suke, yana mai tsarkake kansa, yana raina wasu. Sai wannan ya gadar masa da mummunan zato. Lallai mummunan zato tsakanin musulmi abu ne wanda ya yaxu a wannan zamani. Aka wayi gari ‘yan uwantaka da take tsakanin al’umma tayi rauni, Wannan kuwa zai jawo musu rauni wajen fuskantar qalu-bale na cikin gida da waje.

Yaku bayin Allah! Lalle an cuci mutane dadama ta hanyar munana musu zato da tuhumarsu akan abin da ba ji ba ba su gani ba. Hakanan an qauracewa wasu mutanen kiriki dadama a sanadiyyar wannan mummunar ta’ada. Allah (S.W.T) ya ce:

( وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُبِينًا 58 ) [الأحزاب: 58]

(Lalle waxanda suke cutar da muminai maza da mata, ba tare da abin da suka aikata ba, haqiqa sun xaukarwa kansu wani mummunan qage da laifi mabayyani).

Idan muka gamsu da cewa mummunan zato abu ne mai halakarwa, to tilas ne mu tashi domin magance wannan matsalar saobda kada varna ta yaxu ta game ko-ina-da-ina.

Daga cikin hanyoyin magance wannan matsala, akwai kyautata zato ga mutane, da nisantar munana zato, da qoqarin zurfafa tunani mai tsawo kafin ka yanke hukunci ko tuhuma. A koda yaushe kuskure wajen kyautata zato ga mutane, ya fi alheri sama da kuskure wajen munana zato ga mutane. Umar bn Qhaxxab yake cewa “Kada ka yi wani zato daga duk wata kalma da fito daga xan uwanka mumini sai na alheri, matuqar hakan mai yi wu wa ne”.

Daga cikin hanyoyin magance mummunan zato, akwai bawa mutane uzuri, da rashin bibiyar asiransu, da kallon zamiyarsu. da qoqarin siffantowa da kyawawan xabi’u na musulunci wajen hukunci ga mutane, da kuma amfani da abin da yake a bayyane da barin abinda yake a voye ga Allah (S.W.T) masanin abin da yake a bayyane da voye.

Yaku bayin Allah kuji tsoron Allah ku fahimci faxin Allah ta’ala:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَبْ بَعْضُكُمْ بَعْضًا أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَنْ يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَحِيمٌ 12 ) [الحجرات: 12]

(Ya ku waxanda suka yi imani ku guji yawayawancin zato, lalle wani zaton laifi ne. Kuma kada ku yi leqen asiri. Kuma kada sashenku yayi gibar sashe, shin xayanku na son yaci naman xan uwansa yana matacce, to kunqi hakan. Kuma ku bi Allah da taqawa, lalle Allah mai karvar tuba ne mai jin qai).