islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Kayan maye da tasirinsu wajen lalata samari


7695
Surantawa
Allah ya fifita xan adam da abubuwa masu yawa, wadda ya xara halittu dadama da su. Allah ya fifita shi da hankali, da fahimta da tunani. Hankali ne mafi girman niima da Allah ya yi wa xan-adam. Da hankali ne yake iya banbance tsakanin alheri da sharri, da abu mai cutarwa da mai amfanarwa. Da hanakali xan adam zai yi rayuwa mai kyau, ya iya tafiyar da alamuransa. Da shi ne yake shaqatawa ya more rayuwarsa. Da hankali ne duk alummomi kan ci gaba a rayuwa.

Manufofin huxubar

Sanin cewa, hankali ni’ima ce, wajibi ne a gode wa Allah a kanta.

Gargaxin samari da su guji shan kayan maye waxanda za su lalata musu rayuwarsu.

Yaqi da al’adar shan kayan maye tsakanin samari

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Lalle Allah ya fifita xan-adam a kan dadama daga halittarsa, kamar yadda yake cewa,

( وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِي آَدَمَ وَحَمَلْنَاهُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَرَزَقْنَاهُمْ مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَى كَثِيرٍ مِمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلًا 70 ) [الإسراء: 70]

(Haqiqa mun karrama xan-adam, kuma mun xauke shi a kan tudu da cikin teku, kuma mmu azirta shi da kayan daxi, kuma muka fifita shi a kan yawayawanci abin da muka halitta fifitawa ta sosai).

Allah ya fifita xan adam da abubuwa masu yawa, wadda ya xara halittu dadama da su. Allah ya fifita shi da hankali, da fahimta da tunani. Hankali ne mafi girman ni’ima da Allah ya yi wa xan-adam. Da hankali ne yake iya banbance tsakanin alheri da sharri, da abu mai cutarwa da mai amfanarwa. Da hanakali xan adam zai yi rayuwa mai kyau, ya iya tafiyar da al’amuransa. Da shi ne yake shaqatawa ya more rayuwarsa. Da hankali ne duk al’ummomi kan ci gaba a rayuwa.

Da zarar mutum ya rasa hankalinsa, to shi da dabbobi duk xaya babu bambanci. Ba ya da wani amfani, kuma ba zai amfana da komai ba. Zai ma zama kaya a kan danginsa da al’ummarsa.

To duk da tsadar da hankali yake da ita, za ka ga wani wanda shi bai damu da hankalinsa, ballanta ma ya yi qoqarin ganin ya ba shi wata kariya ta musamman.

Kai har ma za ka ga da wanda zai sa qafarsa ya take hankalinsa, ya kama bin son zuciyarsa, kuma basirarsa ta makance.

Da zarar mutum mai hankali ya kwankwaxi kofin giya, ko wani abu mai sa maye, ko ya shaqi wata tabar mai bugarwa, to fa nan take zai lalubi hankalinsa ya rasa. To shi ke nan daga sannan ya zama dabba sanye da mutane. Sai kuma ya shiga duniyar laifuffuka da alfasha. Rayuwa kuma ta sakwarkwace, ya manta da Ubangijinsa, ya zalinci kansa, ya keta rigar mutuncinsa da hannunsa. Da zarar hankali ya vace to ‘ya’yansa sun zama marayu, matarsa ta yi rashin miji. Da hake ne ya watsar da wani abu na lalurar rayuwa wanda duk wata sharvi’a da Allah ya saukar da ita ta zo da wajabcin kiyaye shi, wanda shi ne hankali. Wanda duk ya sha abin maye har ya rasa hankalinsa, wannan ya cuci kansa, ya kuma cuci al’ummarsa, ya jefa su, ya kuma jefa addininsa cikin wulaqanci. Zai kuma zama barazana ga zaman lafiyar al’umma.

Ya ku bayin Allah! Kayan maye sun gama rusa mutanen da suke da alaqa da su. Sun jefa su cikin kurkuku shekaru aru-aru, sakamakon abin da suka jawo kansu na laifuffuka. ‘yan’yansu da matansu suka zauna tamkar marayu. Ya lalata yarintasa da rayuwarsa ta hanyar amfani da makamin da maqiyansa suka ba shi. Har aka wayi gari gidajen yari sun cika maqil da irin waxannan asararru.

Ya ku bayin Allah! Wasu wawaye marasa hankali sun xauko abin da maqiya suka kawo musu, mavarnata suke dillancinsa. Wallahi musifa ce kawai ta faxa wa musulmi ba tare da sun ankara ba. Domin maqiya sun gane ta ina za su shiga musulmi su yi musu illa. Allah ya yi gaskiya da ya ce,

وَلَا يَزَالُونَ يُقَاتِلُونَكُمْ حَتَّى يَرُدُّوكُمْ عَنْ دِينِكُمْ إِنِ اسْتَطَاعُو) [البقرة: 217] ) (Ba za su gushe ba suna yaqar ku, har sai sun raba ku da addininku idan sun samu iko).

Babban abin mamaki shi ne, mutumin da zai sayi abin za raba shi da hankalinsa da kuxinsa. Me ya sa wanda zai sha giya, ba zai wa’azuntu da wani wanda ya sha ta ta rusa masa rayuwarsa ba? Me ya sa wanda yake shan abin maye, ya yarda ya fitar da kansa daga tawagar masu hankali zuwa qungiyar mahaukata?!

Hasanul Basari yana cewa, «Da a ce ana sayar da hankali, da mutane sun sayar da shi da tsada«.

Ayoyi da hadisai masu yawa sun zo don tabbatar da haramcin shan giya, kamar faxar Allah da yake cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالْأَنْصَابُ وَالْأَزْلَامُ رِجْسٌ مِنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 90 ) [المائدة: 90]

.

(Lalle kaxai giya da caca da gumaka, da kibau na rantsuwa, duk daga aiki ne na shexan, don haka ku nisance shi, lalle za ku rabauta).

Kai su sahabbai ma ba wai kawai haramcinta suka fahimta ba kaxai, a’a sun fahimci cewa an haxa ta da shirka, wadda ita ce zunubin da ya fi kowa ne zunubi da xan adam zai sava wa Allah da shi.

An karvo daga Ibn Abbas Allah ya yarda da shi, ya ce, «Yayin da haramcin giya ya sauko, sai sahabban Annabi (S.A.W.) suka tafi wajen junansu, suka ce, an haramta giya, kuma na sanya ta daidai da shirka). Xabrani ne ya ruwaito shi, da salsala ingantacciya.

Saboda Allah cewa ya yi, «qazanta ce daga aikin shaixan». Kuma dangane da shirka ya ce, «To ku nisanci qazanta ta gumaka».

Muslim ya ruwaito hadisi daga Abdurrahman bn Wa’ala ya ce, na tambayi Ibn Abbas game da sayar da giya? Sai ya ce, Manzon Allah (S.A.W.) ya kasance yana da wani aboki na qabilar Saqif, ko kuma Daus. Sai ya gamu da Annabi (S.A.W.) a ranar buxe Makka, yana xauko wata gora ta giya don bawa Annabi kyauta. Sai Manzon Allah (S.A.W.) ya ce, «Wane, ba ka san Allah ya haramta giya ba?» Sai mutumin nan ya cewa yaronsa: Tafi ka sayar da ita. Sai Manzon Allah (S.A.W.) ya ce, «Da me ka umarce shi?» Sai ya ce, Na umarce shi ne ya sayar da ita ne. sai Manzon Allah ya ce, «Wanda ya haramta shanta shi ne kuma ya haramta sayar da ita». Sai ya sa aka je aka zubar da ita a bayan gari.

Daga cikin hadisan da suka bayyana haramcin giya, akwai hadisin da Manzon Allah (S.A.W.) yake cewa, «Babuwani da zai sha giya, kuma a karvi sallarsa har tsawon kwana arba’in. Idan kuma ya mutu da ita a cikinsa, za a haramta masa Aljannah. Idan ya mutu a cikin kwana arba’in da shanta to ya mutu irin mutuwar jahiliyyah». Xabrani ne ya ruwaito shi da salsala mai kyau daga Abdullah bn Amr.

Wand duk ya sha giya a duniya, to Allah zai haramta ta masa shan ta lahira. Kamar yadda ya zo a hadisi na Abdullahi xan Umar, ya ce, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce, «Wanda ya sha giya a duniya to ba zai sha ta lahira ba». Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

An karvo daga Ibn Umar (R.A.) ya ce, Manzon Allah (S.A.W.) «Allah ya la’anci giya, da mai shanta, da shayar da ita, da mai sayar da ita, da mai sayanta, da mai tace ta, da wanda yake sa wa a tace masa, da mai dakonta, da wanda ake masa dakonta». Abu Dawud ne da Ibn Majah suka ruwaito shi.

A musulunci an harmata duk wani abu mai sanya maye, kaxan xinsa da mai yawa. Domin shan kaxan shi yake jawo shan mai yawan. Sannan shan abin maye ya zame masa jiki. An karvo daga Jabir, (R.A.) ya ce, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce, «Duk abin mai yawansa zai sa maye, to kaxan xinsa haramun ne». Abu Dawud ne da Nasa’i suka ruwaito shi.

Ya ku bayin Allah! Yana daga abin da ya kamata a ja kunne a kansa, tabar wiwi, da sauran abubuwan da suke raba mutum da hankalinsa, su raunana mutum su raunana masa duk wani kuzari. Shan irin waxannan qazantattun abubuwa suna makantar da gani, su tushe basira, kuma ana xaukar duk wani mai shansu mutumin da ba adali ba, wanda bai san yadda zai tafiyar da lamuransa ba. Yana dariya barkatai babu dalili. Yana kuka ba tare da wani dalili ba. Za ka ga idanunsa suna walqatawa kamar wanda ya ga mutuwa.

Kamar yadda maqiya musulunci suke kawo kayan maye kala-kala, suka mayar da tamkar qawar haxiya ta magani, alhalin suna xauke da sinadiri mai cutarwa kamar herawin. Duk wannan aiki ne na shaixan. Don haka ku nisance shi don ku samu rabauta.

Wannan shi ne abin da zan iya faxa. Ina neman gafarar Allah ga kaina da ku bakixaya. Ku nemi gafararsa. Lalle shi mai yawan gafara ne mai jin-qai.

Huxuba Ta Biyu

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafi xaukakar Annabawa, annabinmu Muhammad da iyalan gidansa, da sahabbansa, da tabi’ai, da duk wani wanda ya bi hanyarsa da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Ya bayin Allah! Lalle kayan maye sun cutarwa qwarai a addini, kamar yadda Allah yake cewa,

( إِنَّمَا يُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُوقِعَ بَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ فِي الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ وَيَصُدَّكُمْ عَنْ ذِكْرِ اللَّهِ وَعَنِ الصَّلَاةِ فَهَلْ أَنْتُمْ مُنْتَهُونَ 91 ) [المائدة: 91]

(Kaxai shexanne yake son ya jefa adawa da qiyayya tsakaninku ta hanyar giya da caca, kuma ya hana ku ambaton Allah. To ko za ku hanu).

Kayan maye suna hana sallah, ga shi kuwa ita ce ginshiqin addini, kuma suna hana ambaton Allah. Kuma mai shan su yana tare da shaixanu. Duk wani wanda ya saba shan giya sai ka gan shi ba ya iya ayyukan xa’a. Yana ganin wahalarsu a kansa. Zuciyarsa ba ta tare da alheri sam-sam. Sannan kuma ka same shi mai son aikata haramun ne, koda yaushe, domin zuciyarsa ta riga ta runu da waxannan kayan qazamtar. Don haka koda yaushe addinin a cikin raguwa yake, al’amarunsa qara tavarvarewa suke.

Ya ku bayin Allah! Yana daga cikin cututtukan kayan maye cewa, su suna dakusar da qwaqwalwa. Tana mayar da mutum su-su-su, kuma ya zamana ba ya zama ba ya gani sosai. Sannan ya riqa tangaxi idan yana tafiya. Zuciyarsa ta daina bugawa yadda ya kamata, sukan sa jijiyoyinsa su xaxxaure, yakan iya samun shanyewar wani vangaren jikinsa, jininsa ya daina gudana yadda ya kamata. Kamar yadda zai zama kullum cikin tsoro da damuwa. Duk sanda ya ji wani motsi sai ya firgita. Ta ko ina tsoro ne kewaye da shi, yana jin tsoran qarshen lamarinsa, da cututtukan da za su iya auka masa.

Babu ruwansa da duk wani halin qwarai. Yana aikata duk wani laifi. Sau nawa ne ake aukawa manya-manyan laifuffuka saboda kayen maye da aka sha. Sau tari an aukawa ayyukan alfasha da savon Allah saboda shan abin da ya bige hankali. A lokuta dadama an ketawa wasu rigar mutuncinsu, an sace dukiyoyin wasu, an samu miyagun haxurra a kan hanyoyi, duk saboda shaye-shayen kayen maye.

Ya ku bayin Allah!Maqiya Allah ba za su tava saurarawa wani mumini ba, za su yi ta yin fafutukar ganin sun rushe al’ummar muslmi, sun rushe halayyar samari. Don haka suka mai da qoqarinsu da himmarsu wajen su ga sun sauwaqe samun kayan maye, ta yadda yara ma za su iya samusu. Wannan ya taimaka wajen yaxuwarsu cikin samarin musulmi, har ta kai wasu an shigar da su asibitin mahaukata, wasu kuma an kai su gidajen yari.

Ya ku iyaye, akwai nauyi babba a kanku dangane da wannan lamari. Don haka ku sanya wa ‘ya’yanku idanu, ku riqa yi musu addua’a ta gari da ikhlasi da kykkyawar niyya, domin Allah ya tsare mu gabaxaya daga wannan gubar mai rushe rayuwa. Don haka, sai mun taimakawa juna domin yaqar wannan annoba.

Allah yana cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا قُوا أَنْفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَائِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَا يَعْصُونَ اللَّهَ مَا أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ 6 ) [التحريم: 6]

(Ya ku waxanda suka imani, ku tsare kawukanku da iyalanku daga wuta, mutane da duwatsu ne makamashinta. Masu gadinta mala’iku ne masu kausasan zukata, masu qarfi, ba sa savawa Allah abin da ya umarce su, suna aikata abin da aka umarce su da shi).