islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Kwadaitarwa Wajen Neman Halal Da Nisantar Haram


10573
Surantawa
Haqiqa Allah Madaukakin Sarki ya halatta mana dadadan abubuwa, ya haramta mana munanan abubuwa, masu cutar da jikinmu da hankulanmu, babu ko shakka halal shi ne abin da ya zama mai dadi a karan – kansa, kuma babu cutarwa a cikinsa, sannan aka same shi ta hanyar da shariaa ta yarda da ita. Haramun kuwa shi ne abin da yake mai cutarwa a karan – kansa, wanda Allah da Manzonsa suka haramta shi, ko kuma aka same shi ta hanyar da sharia ta haramta.
p>Manufofin huxubar

Kira zuwa ga neman halal.

Kwaxaitarwa akan gudun duniya da nisantar haramun.

Bayanin falalar neman halal da bala’in da yake cikin neman haramun.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Yaku ‘yan uwana musulmi : Waye a cikinmu ba ya son rayuwa mai daxi duniya da lahira? Wane ne a cikinmu ba ya son ya zama lami – lafiya a cikin gidansa! Yana da abin da zai ci? Waye a cikinmu yake son ya zama nauyi akan wani!?. To ku taho – Yaku bayin Allah – zuwa abin a zai sa mu samu waxancan abubuwan, ku taho zuwa ga wani abu mai girma, wanda yake a cikinsa gyaruwar duniya da lahira take, wanna abu kuwa shi ne neman halal da nisantar haramun.

Haqiqa Allah Maxaukakin Sarki ya halatta mana daxaxan abubuwa, ya haramta mana munanan abubuwa, masu cutar da jikinmu da hankulanmu, babu ko shakka halal shi ne abin da ya zama mai daxi a karan – kansa, kuma babu cutarwa a cikinsa, sannan aka same shi ta hanyar da shari’a ta yarda da ita. Haramun kuwa shi ne abin da yake mai cutarwa a karan – kansa, wanda Allah da Manzonsa suka haramta shi, ko kuma aka same shi ta hanyar da shari’a ta haramta.

Bayin Allah, Neman abinci wani abu ne da Allah ya halicci halitta da shi, don haka ya sanya mana rana ta zama lokacin neman abincin, ya sanya mana dare ya zama lokacin hutu gare mu, ya umarce mu da fita da tafiya a bayan qasa don neman abinci da cin abin da ya sanya a bayanta na arziqi.

Manzon Allah (ﷺ) ya nuna falalar neman halal inda yake cewa : “Babu wani abin da mutum zai ci da yafi alheri fiye da abin da ya samu ta hanyar aiki da hannunsa. Annabin Allah Dawud ya kasance yana ci daga abin ya yi da hannunsa” Bukhari ne ya rawaito.

Don haka wadatuwa ga barin mutane da hanyar neman halal abu ne mai girma, xaukaka ce babba, Sayyidina Umar xan Khaxxab (R.A) yana cewa : “Babu wani wuri da nake so mutuwa ta same ni a wajen fiye da wajen da nake saye da sayarwa, don in ciyar da iyalaina”.

A cikin neman halal akwai kare mutunci, da samun dukiya, da samun xaukakar da Allah ya yi wa xan Adam. An karvo daga Abdullahi xan Amru – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Abubuwa huxu idan kana da su, to kada ka damu da duk abin da ka rasa a duniya, (su ne) Kiyaye amana, gaskiyar zance, kyakkyawan hali, da kamewa a wajen abinci”. Imamu Ahmad ne ya rawaito da sanadi kyakkyawa.

Ya ‘yan uwana ku sani cewa neman halal wajibi ne, dole ne, domin babu wani wanda qafarsa zata gushe ranar alqiyama face sai an tambaye shi a ina ya samu dukiyarsa kuma a ina ya kashe ta, don haka wajibi ne akan dukkan musulmi da musulma su kirdadi halal da aiki mai kyau, don su ci halal su ciyar da halal.

Ku yi duba – ya 'yan uwa ga sayyidina Abubakar – Allah ya yarda da shi – yaronsa ya kawo masa wani abinci ya ci, sai yaron ya ce, “Ko kasan a inda na sami wannan abincin?” sai ya ce, “a ina ka same shi” sai yaron ya ce, “Ai na yi wa wani mutum ne bokanci a lokacin jahiliyya, kuma ban iya bokancin ma ba, kurum dai na yaudare shi ne, don haka sai na gamu da shi sai ya bani ladan aikina, to wannan shi ne abin da ka ci!” nan da nan sai Abubukar ya shigar da xan ‘yatsan shi cikin bakinsa ya yi amai abin da yake cikinsa”. Bukhari ne ya rawaito.

A wata riwaya cewa ya yi : “Da wannan abun ba zai fita ba sai tare da raina, da na fitar da ran, Allah ina neman uzuri a kan abin da tumbi da jijiyoyi suka xauka ya rage bai fito ba”.

Hakanan Sayyidina Umar wata rana ya sha wani nono wanda ya qayatar da shi, sai ya cewa wanda ya kawo masa nonon, “a ina ka same shi?” sai ya ce, “Ai na wuce ni da wajen dabbobin sadaka, sai na tatsi nonon dabbobin”, nan da nan sai Umar ya shigar da hannusa cikin bakinsa ya amayar da shi.

Waxannan su ne bayin Allah nagari waxanda suke fitar haramun daga cikinsu, haramun xin da ya shiga bada saninsu ba, wanda da sun barshi babu komai a kansu, amma duk da haka suka amayar da shi, to me waxanda suke cika cikinsu da haramun a yau zasu ce!. Inna lillahi Wa inna Ilaihi Raji’un.

Yaku masu sauraro : Haqiqa neman haramun yana haifar da munanan abubuwa a cikin al’umma, daga ciki abin da yake haifarwa : akwai yaxuwar cututtuka, xebe albarka, saukar musiba da bala’i iri iri, karayar arziki, zalunci, gaba, da zaman banza. Kaicon waxanda suke cin haramun, suke renon ‘ya ‘yansu da iyalansu da haramun, haqiqa irin waxannan mutane kamar masu shan ruwan kogi ne, suna qara sha suna qara jin ishirwa, ba sa wadatuwa da abu mai yawa, kaxan kuma ba ya isarsu, suna bin karkatattun hanyoyin tara arziqi, cin riba, caca, qwace, sata, tauye ma’auni, voye aibin kayan sayarwa, sihiri, bokanci, cin dukiyar marayu da gajiyayyu, rantse – rantsen qarya, wasa da hauka, makirci, hanyoyi dai daban – daban karkatattu, sun zama irin mutanen nan da manzon Allah ya yi ishara da zuwansu inda yake cewa : “Zamani zai zo, mutum ya zama ba ya damuwa ta ina kuxi ya zo masa, ta halal ne ko haram” Bukhari da Nasa’i suka rawaito.

‘Yan uwana ma’aikata, ‘yan kasuwa, masu sana’a, dillalai da ‘yan kwangila dukkan musulmi da musulma, ku sani wajibi ne a kanku ku nemi halal, ku nisanci haramun, ku kiyaye haqqoqin mutane, ku cika alqawarin dake tsakaninku da Ubangijinku da wanda yake tsakaninku da mutane, ku nisanci qarya da algush, da cin dukiyar mutane da hanyar haramun, saboda cin halal ne jiki yake yin kyau, gavvai suke samun nishaxi, zuciya take gyaruwa, idan kuma an yi addu’a Allah ya amsa.

Yaku ‘yan uwana samari : Manzon Allah (ﷺ) ya fifita kowace sana’a akan zaman banza da roqon mutane, Yana cewa “Na rantse da wanda raina yake hannunsa, xayanku ya xauki igiyarsa, ya je ya yi itace, ya xauko a kan gadon bayansa, ya fi a kan ya je wajen wani mutum ya roqe shi, ya bashi ko ya hana shi” Bukhari ya rawaito.

Don haka ma Sayyidina Umar – Allah ya yarda da shi – yake cewa : “Babu wani wuri da nake so mutuwa ta same ni a wajen fiye da wajen nake saye da sayarwa don in ciyar da iyalaina”. Ya ci gaba da cewa : “Kada xayanku ya zauna ya qi neman arziqi, ya riqa cewa Allah ka azurta ni, alhali kun san sama ba ta yin ruwan zinari ko azurfa”.

An tambayi Imam Ahmad – Allah ya yi masa rahama – cewa : “Me zaka ce akan wanda ya zauna a gida ko masallaci ya ce, ba zan yi aiki ba, ina nan har arziqina ya zo ya sameni” sai Imam Ahmad ya ce, “wannan mutum ne jahili bai san ilimi ba, bai ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa ba : “Haqiqa Allah ya sanya min arziqina a qarqashin takobina ba”.

An karvo daga Hassan ya ce, “Abubuwa biyu masu daxi ne : abin da mutum ya samu ta hanyar dakon da ya yi a bayansa, da abin da ya samu da hannunsa”.

Abu Wa’il – Allah ya yi masa rahama – shi kuma cewa yake : “Dirhamin da na samu ta hanyar kasuwanci ya fi guda goman da na samu ta hanyar kyauta”.

Sa’id xan Musayyib – Allah ya yi masa rahama – yana cewa : “Babu alheri a tare da wanda ba ya neman dukiya, wadda zai biya bashi da ita, ya kare mutuncinsa, ya sauqe nauyinsa, in kuma ya mutu ya bar wa magada abin gado”.

Wannan fa kaxan kenan daga cikin irin yadda musulunci yake kwaxaitar da mabiyansa wajen neman halal da nisantar roqo da bara da qasqanci da cin haramun. Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “Duk wanda ya yi roqo (bara) alhali yana da abin da ya ishe shi, to ranar alqiyama zai zo da fuskarsa a kerkece kamar an yagushe ta. Sai aka ce, meye abin da zai ishe xin? Sai ya ce, “Dirhami hamsin, ko abin da ya yi daidai da shi na zinari”. Abu Dawud da Nasa’i da Ibnu Majah suka rawaito shi.

Da wannan ne zamu gane qasqancin waxanda ba sa neman na kansu sai dai bara da roqon mutane, irin waxannan mutane ba su san cewa neman halal yana da wani daxi da garxi na musamman ba?, ya aka yi suka yarda suka zama kamar karnuka, suna bin duk abin da aka jefa musu cikin qasqanci da wulaqanci, ba sa tafiya face hancinsu yana qasa yana shinshine – shinshine. Allah Maxaukakin Sarki ya kare mu, ya yi mana gamo – da – katar. (Ameen).

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (ﷺ) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

‘Yan uwana masu sauraro : Yana daga cikin abin da zai taimakemu wajen cin halal da barin haramun nisantar duniya, da rashin sa ta a zuciya, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, “Wanda duniya ta zama ita ce himmarsa, Allah zai rarrraba masa al’amarinsa, ya sanya masa talauci a gaban idonsa, ba kuma abin da zai samu na duniya sai abin da aka rubuta masa. Wanda kuwa lahira ce niyyarsa, Allah zai tattara masa al’amarinsa, ya sanya wadatarsa a cikin zuciyarsa, kuma duniya ta zo masa akan dole”. Ibnu Majah ne ya rawaito shi.

Hakanan an rawaito daga Abu Huraira (R.A), Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Bawan dinari ya tave, bawan dirhami ya tave, bawan riga ya tave, in ya samu ya yarda, in kuma bai samu ba ya yi fushi, (To irin wannan mutum) idan qaya ta soke shi kada (Allah) ya cire masa. Madallah da bawan da yake riqe da ragamar dokinsa saboda Allah, kansa ya yi qura da gizo, idan yana gadi to zai tsaya wurin gadinsa, idan aka ajiye shi a bayan runduna, to zai tsaya a bayan, idan ya nemi izini ba a yi masa izinin ba (saboda an raina shi) idan ya nemi alfarma ba a yi masa. (To madallah da wannan bawa a kan wancan bawan duniyar). Bukhari ne ya rawaito.

Ku sani – Yaku bayin Allah – cin haramun da tara haramun yana jawo fushin Allah Maxaukakin Sarki a kan bawa, saboda Allah mai tsarki ne, ba ya karvar aiki kuwa sai mai tsarki, don haka duk wanda ya tara haramun, ya zama shi ne cin sa da shan sa, to ya sani babu shi ba Allah, ya yi nisa da Allah Maxaukakin Sarki.

Ibnu Qayyim – Allah ya yi masa rahama – ya ce, “Ba abin da yake sa bawa ya yi abin da Allah ya haramta masa sai abubuwa guda biyu : Abu na farko, munana zato ga Allah, da tunanin cewa idan ya bi Allah, ba zai bashi wani abin alheri ba. Abu na biyu : ya kasance ya san cewa duk wanda ya bar wani abin da Allah ba ya so don Allah, Allah zai canza masa wanda ya fi alheri, amma sai kawai sha’awarsa ta rinjayi haqurinsa (ya kasa haquri), son zuciyarsa ya rinjayi hankalinsa, (sai kawai ya afkawa haramun xin). Na farko raunin ilimi ne ya kawo shi, abu na biyu kuwa raunin hankali da basira”. (Al – Fawa’id shafi na 48).

Yaku musulmi : Yana daga cikin albarkar halal idan mutum ya yi sadaka da shi, Allah yana karvar wannan sadakar ya reneta, kamar yadda xayanku yake renon xan goxiyarsa. An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wanda ya yi sadaka da wani abu kwatankwacin dabino na halal – Allah ba ya karvar wani sai mai tsarki – to Allah zai karvi wannan sadakar da hannunsa na dama, ya reneta kamar yadda xayanku yake renon xan goxiyarsa, har ta zama kamar dutse”.Bukhari da Tirmizi da Ibnu Majah.

Ya ‘yan uwa : yana cikin mafi girman abin da yake sa a buxe qofofin rahama da arziqi ga mutane tsoron Allah Maxaukakin Sarki, Allah yana cewa :

(وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى آَمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَرَكَاتٍ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ96) [الأعراف: ٩٦]

Ma’ana : (Da mutanen alqarya sun yi imani sun ji tsoron Allah da mun buxe musu abarkatu daga sama da qasa) (Al – A’araf : 96).

Don haka dukkan alheri yana cikin tsoron Allah, duk wanda ya ji tsoron Allah, Allah ya isar masa, kuma zai sanya masa mafita daga dukkan wani qunci da yake ciki, ya azurta shi da inda baya zato, babu yadda za a yi rayuwa ta yi qunci ga wanda ya ji tsoron Allah ya kiyaye dokokinsa.

Yana daga cikin mafi girman gudun duniya barin haramun, babu gudun duniya da tsoron Allah ga wanda yake cin haramun, ko yake mu’amala da haramun, ko yake zaluntar mutane, saboda haka wajibi ne a kanka ya kai – bawan Allah – ka kuvuta daga zalunci tun gabanin ka biya a ranar da babu dirmahi ko dinari, in kana da aiki na qwarai a xiba a ba wanda ka zalunta, in baka da shi a xebo munanan ayyukan wanda ka zalunta a xora maka. Allah ya tseratar damu daga wuta.

Ya ku bayin Allah : Babu wata rai da zata mutu face sai ta cika arziqinta, don haka ku ji tsoron Allah ku kyautata hanyar neman abincinku, An karvo daga Jabir – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Kada ku ga jinkirin arziqi, babu wani bawa da zai mutu, har sai ya cika qarshen arziqinsa, don haka ku kyautata neman halal, ku bar haramun" Ibnu Hibban ne ya rawaito.

Allah ka wadatamu da halal xin ka daga barin haramun xin ka, ka wadatamu da xa'arka mu bar savonka, ka wadata mu da falalarka, mu bar wanda ba kai ba. Ya Allah kada ka sa duniya ta zama ita ce babbar burinmu, ko ta zama ita ce qarshen iliminka, ko wuta ta zama makomarmu, muna roqonka cin moriyar duk wani aikin alheri, da kuvuta daga zunubi. (Ameen).